bayyinaat

Published time: 26 ,January ,2017      15:10:13
Mutum halitta ne mai bukatar rayuwa a al'umma da ta iyali, rayuwar iyali kuwa ita ce mafi karancin haduwar zaman tare amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wannan asasin an gina shi ne da namij da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da aiyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyaiya mai karfi da alaka tsakanin iyali.
Lambar Labari: 24
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki, tsira ya tabbata ga zababben halittar Allah annabi Muhammad da alayensa tsarkaka

"Su tufafi ne gare ku, kuma ku tufafi ne gare su". Bakara: 187. 

Aure samar da wata alaka ce mai karfi tsakanin namiji da mace da yakan halatta wa junansu duk wata alaka da ta kan iya kaiwa ga samar da zuri'a, da hawan wasu hakkoki kan junansu. Aure wata ni'ima ce da Allah ya sanya ga bayinsa da babu mai samu sai da ludufinsa (s.w.t). Babu wani mutum da zai yi aure da wata ko wata ta auri wani sai Allah ya rubuta musu hakan. Aure hanya ce da ake samar da muminan bayi, shari'a ta yi bayanin cewa babu wani mumini da za a samar ba ta hanyar aure ba, don haka tsarkin haihuwa ana samun ta ne ta hanyar aure kawai. Musulunci yana ganin halaccin aure kuma yana karfafawa kan hakan, kuma yana umarni da shi kuma yana murna da aure da wuri, wannan kuwa yayin da kowanne mace da namiji ya cika shekarun kamalarsa, ga mace da namiji, a lokacin ne yake karfafa yin aure domin kada alfasha ta wakana. 
Mutum halitta ne na al'umma da zaman cikin iyali wanda yake shi ne mafi karancin haduwar zaman tare, amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wanda wannan asasin an gina shi ne da namiji da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da aiyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyaiya mai karfi da alaka tsakanin iyali. Shin kuwa mutum ya san wajibi ne a kansa ya daukaka himmarsa zuwa ga Allah (s.w.t) domin ba a yi shi don ya damfaru da duniya ba, "Ina zaku ne" . Shin kuwa mutum ya san cewa yana da wani nauyi da ya hau kansa? "Ku kare kawukanku da iyalanku daga wuta, wacce gumagumanta su ne mutane da duwatsu" . 
Littafin "Rayuwar Ma’aurata”  ya kunshi bahasosida suka shafi "Mace a Al’adu da Musulunci” da yake kunshe da bayanai ne game da marhaloli da mace ta kasance a ciki daga zamanin da zuwa yau a takaice, don hadafin fahimtar ni’imar da Allah (s.w.t) ya yi mana a wannan Addini da ya aiko mafificin halitta Manzo Muhammadu (s.a.w) da shi, sa’anan kuma zai taimaka wajan sanin matakai da marhaloli na tarihi da mata suka wuce a sauran al’ummu da suka gabata. Sai bahasin "Auren Mace Fiye da Daya” don hadafin kariya ga hukuncin musulunci da manzon rahama (s.a.w) kan abin da ya shafi auran sama da mace daya da yawaitar matan Mafificin halitta. Sai kuma bahasi na uku "Rayuwar Ma'aurata”  wanda yake bayani da nuni kan namiji ko macen da za a zaba don zama tare. Tare da bayanin nauyin da ya hau kansu, da yadda ya kamata su rayu, da sauran bayanai da suka shafi rayuwar ma'aurata. 
Musulunci addini ne mai fadi da ya himmantu da warware duk matsalolin dan'adam, don haka ne ya kalli duk wani janibi na rayuwar mutane, saboda haka ne muka yi imani da cewa babu wani abu da musulunci bai yi magana a kansa ba. Sai dai an samu takaitawar musulmi wurin ba wa komai hakkinsa sai suka himmantu dawasu bangarori suka manta da wasu. Da zamu kalli fagen siyasa, zaman tare, tattalin arziki, tsaro, kotu, dauloli, da alakoki, rayuwar iyali, babu wasu bayanai masu yawa da zaa samu. 
Takaitawar yin bayaninsa ya sanya wasu al'ummu suna daukarsa a matsayin addini tauyaiye da ba shi da wani abin cewa a kowane fage sai na ibadoji da wasu mu'amaloli kamar aure, ciniki, haya, saki, rantsuwa, da makamancin hakan. Suna masu jahiltar iliminsa da hikimominsa masu kima da darajada zasu iya fitar da wannan duniyar daga kangin da take ciki, da bayar da warwara ga duk wani dan'adam a kowane fage. Rashin fadada magana kan hikimar da hukuncin addini yake kunshe da ita ya sanya hatta musulmi sun jahilci mafi yawan hikimomin hukuncin addini a kan kowane lamari. 
Littafin ya kalli al'adun mutanenmu na kasar Hausa da yadda suke rayuwa domin neman gyara cikin wannan al'ummar tamu da ilmantarwa ko tunatarwa game da wasu muhimman bayanai da ya kamata su mayar da hankali kansu game da gyara zaman tare domin samun al'umma ta gari. Sannan ya kunshi takaitaccen bayani ne game da yadda ya kamata gida ya kasance, da siffofin ma’aurata, da kuma yadda ya kamata su kalli rayuwa, da abin da ya shafi kula da hakkin juna kamar yadda musulunci ya gindaya ba tare da ketare iyaka ba. 
A musulunci an yi umarni da yin aure ba domin biyan bukatar duniya ko ta sha’awa ba kawai, akwai bukatar gina al’umma saliha da zata ci gaba da daukar nauyin isar da sakon Allah a duk fadin Duniya, wannan yana bukatar taimakekeniya tsakanin ma’aurata, sa’annan akwai samun nutsuwar ruhi da dan'adam yana bukatarsa wanda an sanya shi ne ya zamanto ta hanyar zamantakewa tsakanin miji da mata. Komai ilimin da mutum (namiji ko mace) suka samuko wata ni'ima ta duniya idan ba su samu mai debe musu kewa ta fuskacin zaman aurataiya ba to akwai wani gibi babba da ba su cike shi ba wanda ba ya samuwa sai ta hanyar aurataiya . Sai dai idan ba a samu dacewa da abokin zama nagari ba ta yadda aka mayar da kauna da so suka koma kiyaiya da gaba, to rayuwa takan gurbace ta koma gwara rashin abokin zama. 
Ana son yin aure da wuri ga wanda ya balaga matukar ya samu yalwa, domin a cikin rashin yin hakan akwai fitina a bayan kasa da fasadi mai girma kamar yadda ya zo a ruwaya . Mu sani akwai kamalar da ba ta samuwa sai ta hanyar aure, irin wadannan abubuwansun hada da: sanin ma’anar ciyarwa, yafewa, soyaiya, hakuri, juriya, daukar nauyin mutane, reno, tarbiiyar ‘ya’ya, fahimtar kimar iyaye, tunanin gida, da sauransu. 
 Ayatul-Lahi makarim shirazi yana cewa: Sau da yawa daga cikin abubuwa kamar ma’anar soyaiya, da kauna, da yafewa, da kyauta, da baiwa da tausayi, da fansar rai, ma’anarsu ba ta ganuwa da fahimtuwa sai da aure, wadanda ta hanyar zaman banza da matar haram ko zaman gwauranci da rashin aure ba za a iya fahimtar hakikaninsu ba, kuma riskarsu tana yiwuwa ta hanyar zamantakewar aure ne kawai . 
 Muna fatan littafin ya zama mai amfani ga rayuwar al’umma baki daya, ta yadda zai zama sanadi na gina al’umma saliha da ci gaban duniyar musulmi. Daga karshe ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga iyaye da duk bayin Allah salihai malamaina da duk wanda ya sanar da ni wani abu da amfaninsa ya shafi duniya da lahira. 

BANGARE NA FARKO
Wannan bangaren yana bayani ne kan mace da namiji da asalin halittarsu da yanayinta a badinin samuwarsu da zahirin kirar halittarsu ta jiki tare da kawo wasu daga cikin sirrin yin halittar su bisa nuni da kimar da halittar mutum take da ita maza da mata babu wani bambanci, kuma mata suna da wani matsayi da kima ta musamman mai sanya namiji ya tafi wurinsu don neman su da kama hannunsu. A nan ne zamu gane cewa shari'a tana kallon maza da mata da idanuwan mutuntakarsu ba da jinsinsu ba sai dai a wasu hukunce-hukunce da suka shafi halittar jikinsu. Amma al'ummu suna kallon mutum ne ta cikin jinsinsa a matakin farko don haka ne aka samu matsalar nan ta yin bambanci tsakanin wadannan jinsina guda biyu namiji da mace a al'ummu daban-daban, sai Allah ya aiko manzanninsa don su luras da mutum kan cewa mai daraja a wurinsa shi ne wanda ya fi tsoronsa ba tare da la'akari da jinsinsa ba. 

SIRRIN HALITTAR NAMIJI DA MACE
Mutum halitta ne mai bukatar rayuwa a al'umma da ta iyali, rayuwar iyali kuwa ita ce mafi karancin haduwar zaman tare amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wannan asasin an gina shi ne da namij da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da aiyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyaiya mai karfi da alaka tsakanin iyali. 
Mace taushi da kanshi ce kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi , kuma mata suna daga cikin abubuwa uku da aka sanya sonsu a zuciyar ma’aikin Allah (s.a.w) , don haka son mata ba aibi ba ne. Sai dai son da Manzon Allah (s.a.w) yake masu so ne na baiyanar adon Allah , ba na sha’awa ba. Don haka son mata ta hanyar kallon janibi daya na halittar jikinsu shi ne aibi domin wannan yana komawa zuwa ga bukatun jiki ne tsantsa da dulmuya cikin kogin sha’awar rai, amma son su don kasancewarsu halarar adon Allah  a wannan duniyar wani gani ne da yake komawa zuwa ga sanin mahalicci madaukaki. Imam Ali (a.s) yana cewa: Babu wani abu da zan gani sai na ga Allah kafinsa, da bayansa, da tare da shi . Ganin wasiiyin Manzon Allah (s.a.w) gani ne da ya hada da ganin zuci wanda ya kunshi so, kauna, sani, da tunani, bai takaita da gani na zahiri ba!. 
Yawan takura wa mata a duniya ya jawo bahasin ‘yancin mace, wannan kuwa wani abu ne da yake tun farkon tarihi aka samu danniya ga jinsin mace, har aka samu al’ummu da suke ganin mace wata halitta ce tsakanin mutum da dabba, sai dai an samu wasu suna ganin shin da gaske ne namiji ya fi mace ko kuwa? Kuma shin mace ta fi namiji ko kuwa? sai dai duka bangaren biyu suna kan kuskure ne, domin musulunci yana kallon kowane mutum namiji da mace a matsayin mutum ba ta jinsinsa ba. Wannan ne muke cewa: "Kallon mutuntaka ga jinsi, ba kallon jinsintaka ga mutum ba”. 
Wannan nazari na musulunci shi ne kawai mafita, don haka yabo da suka da ake samu daga bangarori biyu duka kuskure ne, domin asalin wannan tattaunawar ta samo asali daga batun cewa akwai bambanci tsakanin mace da namiji. Kamar dai yadda wasu suke rikici kan "Jari Hujja” ne daidai ko "Gurguzu” a tsarin siyasa ko tattalin arziki alhalin duk biyu suna nuni zuwa ga kallon mutum ta fuskacin tattalin arziki, ba kamar yadda musulunci yake ganin sa ta fuskacin dan'adamtaka ba. 
Musulunci yana kallon mace a matsayin mutum ne, kamar yadda yake kallon namiji a matsayin mutum, bai ce mace daban namiji daban ba a matsayin halittu biyu; ya zo ne da hukunce-hukunce gare su iri daya, sai dai ya bambanta su a hukunce-hukunce a wurin da suka saba, domin kowannensu ya kasance ya samu nasa hakkin daidai yadda ya dace da rauninsa ko karfinsa. Sai mace ta zama sarauniya mai aiki da halitta da dabi’un halaiyar zuciyarta domin gyara al’umma, sai namiji ya zama bawa amma shugaba domin jagoran mutane shi ne hadiminsu kamar yadda ya zo a hadisi, don haka sai ya sanya ci gaban gida da al’umma da hankalinsa, kamar yadda mace zata sanya ci gaban gida da al’umma da dabi’un halaiyarta. 
Akwai hadisai da yawa masu tawili da sai an hada ma'anarsu da ta wasu hadisan ne ake iya gane manufarsu, a zahirinsu kamar suka ne amma badininsu yabo ne. Kamar hadisin nan da yake cewa: Imam Ali (a.s) ya ce: "Mace sharri ce dukanta, sharrin da yake cikinta shi ne babu makawa daga gare ta!" . A nan ke nan sharrin yana da ma’anar da ta saba da ma’anar da bahaushe yake nufi da sharri, domin sharri a nan yana da ma’ana kyakkyawa wacce idan muka duba zata iya hawa kan abinci, abinsha, tufafi, da duk wani abu na bukatuwar dan'adam na rayuwa. Don haka a nan sharri yana nufin abin da ya zama dole ga rayuwar mutum. 
Mai daraja Allah ya kara jan zamaninsa Ayatul-Lahi Jawadi Amuli  yana fassara hadisin nan da ya yi magana kan cewa: "Hankulan mata suna cikin kyawunsu, amma kyawun maza suna cikin hankulansu”. Wasu sun dauka aibi ne ko tawaya ga mace, amma sai ga shi ya kawo bayanai kusan shafi 300. Hadisin ba ya yabon namiji ko sukan mace, kamar yadda ba zai yiwu a juya shi ba a ce yana yabon mace yana sukan namiji. Sai dai yana nuna nau’in aiyuka da fagen da kowanne ya kware ne. 
Halarta lamarin Allah a cikin halittunsa wani lokaci yana kasancewa ta fuskacin hankula wani lokaci kuma ta fuskacin dabi’u don haka babu wani martaba sai ta kasance mai komawa zuwa ga ubangijin bayi. Babu ma’ana waccan halartar ta kasance an kaskantar da ita domin tana da wani kyawu da siffofi da sukan kai ga wani hadafin da Allah yake son tabbatarsa a duniyar halittu!. Wannan hadisin ba yana kasa mutane gida biyu ba ne, sai dai yana nuni da siffar nau’in aiyukan da kowanne ya kware kansa ne!. 
Domin namiji yana iya tsayar da aiyukansa bisa gini da hankali ba don ya rasa janibin dabi’ar kayatarwa ba, kamar yadda mace take iya kyautata aiyukanta ta hanyar kayatarwa ba don ta rasa janibin hankali ba, domin da mai yin amfani da kayatarwa da mai amfani da hankali duk suna amfani da biyun ne yayin aiyukansu. 
Kamar dai fadin Allah ne cewa: "Maza su ne masu tsayuwa da al’amuran mata…” ba don mace ita ma ba ta tsayuwa da al’amuran namiji ba!, sau tari nassin shari’a yakan yi amfani da galibi kamar yadda yakan zo wani lokaci domin kafa dokoki don tsara rayuwar ma’aurata biyu, don haka nassin shari’a yana bukatar zurfafawa domin sanin sa. Musulunci ya fadi hakan amma sai ya sanya nauyin kofar gida zuwa waje a hannun namiji, ya sanya nauyin kofar gida zuwa ciki a hannun mace, sai ya kasance idan gida ya gyaru, to mace ce ta gyara shi, idan ya bace to ita ta bata shi, wane karfi ne ya fi wannan ku gaya mini!?. 
Wannan kuwa ba don komai ba sai domin cikin gida yana bukatar kayatarwa da sanya tausasawar zuciya da tausayawa domin ciki da waje su daidaitu, kamar yadda waje take bukatar kutsawa fagen dagar neman abin rayuwa domin ciki da waje su daidaitu. Don haka bai kamata ba dan kayi-nayi ya shiga hawa kan doron Kur’ani don kawai ya san kalmomin larabci, domin Kur’ani yana da zurfafan ma’anoni da gano su yake bukatar makomar da take iya fassara shi kamar yadda muka sani shi ne Annabi (s.a.w) sai kuma wadanda ya yi nuni da su bayansa daga Ahlul-baiti. 
Rayuwar maurataiya kamar saka ce da kowane daya daga ma’aurata yana da fagen da ya kware, kuma idan wani ya karbi kwarewar wani sai a samu rashin cin nasara. Maganar Annabi Ibrahim (a.s) da mala’iku ba ta sanya ba shi kyautar dansa Ishak (a.s) ba amma dariyar matarsa  kawai ta sanya mala’iku sun yi mata albishir da dansa Ishak (a.s) domin halarar adon Allah da yake tattare da wannan dariya ta Sarah (s), sai wannan ya nuna mana cewa kowa ce halitta mace da namiji yana da nasa fagen kwarewa. 
Kamar yadda Allah ya halicci namiji haka nan ya halicci mace, Zurara ya tambayi Imam Sadik (a.s) cewa: Wasu mutane suna cewa an halicci Hauwa daga kashin kirjin Annabi Adam (a.s) na hagu. Sai ya ce: Tsarkin Allah ya tabbata kuma ya barranta daga hakan, shin wanda yake fadin hakan yana ganin cewa Allah ba shi da ikon ya halicci mata ga Adam ba ta kirjinsa ba?... har dai inda yake cewa: Sannan sai Allah ya halicci Hauwa, sai Adam (a.s) ya ce: Ya Ubangjiji wane abin halitta ne wannan kyakkyawa wanda na samu debe kewa da kasancewarsa kusa da ni da kallonsa? Sai Allah madaukaki ya ce: Ya Adam (a.s) wannan baiwata Hauwa ce shin kana son ta kasance tare da kai? Sai ya ce: Na’am kuma ni mai gode maka ne kan hakan matukar ina raye, sai Allah madaukaki ya ce masa: Ka nemi aurenta domin ita baiwata ce kuma ta dace da kai a matsayin macen sha’awa, sannan sai Allah ya halitta masa sha’awa…” . 
Akwai wasu abubuwa masu muhimmanci a nan da zamu lura da su cewa: Batun halittar Hauwa daga Adam (a.s) daga kirjinsa na hagu bai inganta ba. Halittar Hauwa ta kasance ne daban mai zaman kanta, ba ta tsuro daga halittar Adam ba. Kallon da annabi Adam (a.s) ya yi wa Hauwa shi ne ya sanya shi samun nutsuwa da alaka da ita daga baya. Sai dai ba kallon sha'awa ba ne, domin an sanya mishi sha'awa ne ma bayan ya samu nutsuwa da ita. Kuma wannan yana nuna mana cewa sadaki mafi daraja shi ne koyar da matar da aka aura, a sanar da ita ubangiji da siffofinsa da aiyukansa da kuma nauyin da ya hau kanta da Allah ya dora mata. 
Bayan aure sai Adam (a.s) ya ce da Hauwa ta zo wurinsa yana kiran ta, sai Allah ya umarce shi da ya tashi ya je wurinta. Wannan yana nuna cewa namiji ne yake zuwa ya nemi auren mace, kuma shi ne zai rika zuwa gidansu ko wurinta, kai shi ne ma ya fi kamata ya rika bin ta ko nemanta ko da a daki ne. Da wannan ne zamu gane cewa mace da namiji daga asali daya suke ba wai namiji ne asali ba mace kuma reshe, kuma duk suna mikuwa zuwa ga mahalicci ubangiji daya wanda ya yi su duka kai tsaye. Sai dai yin magana da Adam (a.s) yana nuna cewa namiji yana da wata baiwa ta samun wahayi daga Allah a matsayin dan sakonsa duk da kuwa wilayar Allah da soyaiyarsa da kusancinsa ba su kebanta da shi ba. 
Namiji halitta ce mai dauke da karfin Allah da buwayarsa don haka ne aka dora masa alhakin kare iyali da ciyar da su da sauran hidimomi da aka dora masa wanda ayar Kur'ani ta yi nuni da hakan da cewa: "... Maza su ne masu tsayuwa da al'amuran mata ... ". Haka ma zamu ga mace a matsayinta na adon Allah an dora mata nauyin samar wa namiji nutsuwa don ya iya aiwatar da wadancan nauye-nauye da suke kansa cikin sauki. 
Kuma mace halitta ce ta Allah (s.w.t) da ta kasance wani abu ne mai kamar maganadisu da namiji yake fizguwa zuwa gare shi. Kuma wannan daraja ce ga mace kuma kima ce ga namiji ba kaskanci ba ne, don haka zuwa gurin mace alama ce ta daukaka ga namiji kuma daraja ce ga mace a lokaci guda. 
Haduwa wadannan halittu biyu namiji a matsayinsa na nagatib da mace a matsayinta na pozitib yana hada mana cakudewa tsakanin girman Allah da adon Allah domin gina natija mai kyau da al'umma ta gari wacce take dauke da sunayen Allah da sakonsa domin cika duniya da hasken ubangiji, sai wannan kasa da duk halittu su haskaka da hasken Allah madaukaki. Sannan wannan yana nuna mana hakikanin sirrin mutum ba namiji ba ne, ba kuma mace ba ne, sirrin asasin mutum shi ne ruhin da yake halittar Allah wanda idan aka sanya masa tufafin jiki to a lokacin ne zai tashi da surar namiji ko mace daidai gwargwadon jikin da aka sanya masa. 
Shin jiki zai iya sanya tasiri a ruhi ko kuwa? Idan mun duba sosai zamu iya ganin hakan, domin shi jiki ba kawai kamar fatanya ba ce a hannun mai noma da idan ya ga dama ya yi amfani da ita idan kuma ba ya so ya wurgar da ita. Domin jiki halitta ce wacce sharadi ne ga rai idan zai yi aiki sai da shi, don haka jiki yana da rawar da yake takawa. Da wannan ne zamu ga muhimmancin wannan bahasi domin ya shafi bayanin halittu da sakamakon da zasu samu a ranar kiyama. Sannan da wannan ne zamu gane cewa binciken da ya shagaltar da marubuta cewa; "shin da namiji da mace suna da daidaito ne ko suna da sabani" ba shi da muhimmanci. 
Haka nan da wannan bayanin muna iya gane cewa ruhin mutum shi ne asali jiki reshen samuwarsa ne, sai dai tun da jiki yana bambanta tsakanin namiji da mace saboda bambancin da ke tsakanin kyawu da kwarjini don haka sai aka samu bambanci a hukuncin shari'a a wasu janibobin sakamakon hakan, kuma da la'akari da ruhi (rai) ne aka samu rayuwar wannan duniyar, Barzahu, da lahira. Da wannan ne aka samu bambanci tsakanin masu imani da gaibi (Allah) da kuma wadanda ba su yi imani da shi ba. Sai mulhidai (wadanda ba su yi imani da Allah ba) suka tafi a kan cewa mutum yana zama mutum ne da jiki kuma tun da jiki iri daya ne to babu wata ma'ana hukuncinsu ya bambanta. Amma masu imani suna ganin cewa mutum yana zama mutum ne da ruhinsa ba da jikinsa ba, duk da kuwa jiki abu ne wanda yake dole ga ruhi kamar yadda muka kawo. Don haka idan Allah madaukaki yana magana da mutum to yana magana da shi da la'akari da ruhinsa ne a matakin farko ba jikinsa ba, sai dai a wasu hukunce-hukuncen suna da bambanci bisa la'akari da jikinsu . 
Wannan kimar ta halittar mutum namiji da mace ta sanya su zama halifofin Allah a wannan duniya, sai suka kasance su ne masu gaje wannan duniya da izinin Allah don haka ne maganar da Allah ya yi da Adam (a.s) ba ta shafe shi kawai ba, sai muka ga ta shafi Adam da Hauwa (a.s) yayin da yake yi musu gargadin shedan da yaudararsa ya gaya musu cewa shedan makiyinsu ne su biyun. Kuma shi ma shedan da ya tashi yi musu rantsuwa ya yi musu su duka biyun ne bai takaita da Adam (a.s) ba! Fadinsa madaukaki: "Shedan makiyi ne gare ku"  da fadinsa: "Sai ya rantse musu da Allah cewa ni ina daga cikin masu yi muku nasiha" . 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: