bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      22:49:00
Magana a kan ‘yan uwantaka da kaunar juna na daya daga cikin abin da addinin musulunci ya muhimmantar ya kuma ba shi matsayi na musamman tun a farko-farkon fara kiran Manzon Rahama Muhammad (s.a.w.a)
Lambar Labari: 268
GABATARWA:
Magana a kan ‘yan uwantaka da kaunar juna na daya daga cikin abin da addinin musulunci ya muhimmantar ya kuma ba shi matsayi na musamman tun a farko-farkon fara kiran Manzon Rahama Muhammad (s.a.w.a). Daya daga cikin tushe kuma ginshiki na karfafuwar addini shi ne yan uwantaka da kaunar juna a tsakanin mabiya addinin musulunci. Haka nan yana daya daga cikin manya-manyan hadafofin musulunci, kuma hanya guda daya rak wadda za ta samar da wasu jama’a muminai wadanda za su ginu a kan imani da kaunar juna ta yadda za su iya kaiwa ga asasi na tauhidi.
MENE NE MA’ANAR YAN UWANTAKA:
Wata alaka ce ta kud da kud wadda take shiga tsakanin mutum biyu ko fiye, suna kasancewa a karkashin inuwa guda saboda wani dalili da ya hada su, wato dai alakar tana iya zama ta hanyar dangantaka ta jini, unguwa, wajen aiki, gari, kabila ko addini. Sai dai kuma ‘yan uwantaka ta addini ta fi duk sauran karfi, saboda ita ta bambanta ta hanyar cewa ita alaka ce wacce take tsayuwa ta hanyar shari’a da son Allah, ta yadda dukkan musulmai a ko’ina suke a fadin duniya to ‘yan uwan juna ne, sabanin ‘yan uwantaka ta jini, gari ko  kabila domin su a cikinsu za a iya samun sassabawa da adawa da bambance-bambance na addini a tsakanin juna.    
MUHIMMANCIN YAN UWANTAKA DA KAUNAR JUNA A MUSULUNCI
‘Yan uwantaka da kaunar juna a musulunci babbar ni’ima ce mai tarin muhimmanci kuma wata babbar hanya ce wacce take kiyaye al’umma daga dukkan nau’oi na cutarwa da rarrubuwa, domin za mu ga cewa ta hanyar ne a kan samu hadin kai mai karfi, kuma a kan kasance tare har a yi aiki domin bunkasa addini da warware matsaloli da bukatun al’umma, wanda hakan zai kara taimakawa al’umma su samu yalwatar arziki, dankon-zumunci da kyakkyawar alaka da tarbiyya, kuma su nisanta daga dukkan kaidin makiya na ciki da na waje. Kamar dai yadda za mu iya ganin haka a cikin nassosi na Qur’ani da hadisan Ma’asumai (as).
Ya zo a cikin Qur’ani mai girma in da Allah Subhanahu wa Ta’ala yake cewa: 
[كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنْذِرِينَ وَأَنْزَلَ مَعَهُمُ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ فِيمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ......] ( سورة البقرة الآية 213 ).
Tarjamar Aya: Mutane sun kasance al’umma guda daya, sai Allah ya aiko Annabawa masu ba da bushara da gargadi, kuma ya saukar da littafi da gaskia a tare da su domin ya yi hukunci a tsakanin mutane cikin abin da suka sassaba wa juna a cikinsa…  (suratul Bakara aya ta 213).
Ya zo a cikin tafsirin Allama Tabataba’i (Al-Mizan fi Tafsiril Qur’an) bayanin cewa: Wannan ayar tana bayani ne a kan dalilin shar’anta addini tun a asali, da kuma yadda aka kallafa wa mutum bin shari’ar addinin, kuma abin da ya kawo sabani a tsakaninsu yana bukatar bayani kamar haka: Cewa lallai shi mutum – wanda yake wani nau’i ne na hallita da aka dora shi a kan fitira ta zaman tare da taimakon juna – ya kasance a farko-farkon haduwarsa al’umma ce da ke dunkule waje guda, sai daga baya a bisa tsari na fitira dinsa da kokarinsa na ganin ya handame abubuwa ga kansa shi kadai ya sassaba da juna, to daga nan ne sai bukatar samar da dokoki wadanda za su kawar da wannan sabanin da rigingimun da ya shiga tsakaninsu ya taso, kuma wadannan dokokin sai suka dauki wani nau’i na addini, suna masu yin bushara da kyakkyawan sakamako da gargadi ga yin ukuba, haka nan ma saboda a samu dacewa sai aka shar’anta yin ibada, aka aiko da Annabawa da Manzanni, amma sai sannu a hankali suka shiga sassabawa game da ilimomin ko sanin addini (ma’arifuddin), al’amuran mafara da na makoma (mabda’u da ma’ad). A dalilin haka sai aka samu sabani a cikin haduwar kai da ake da ita ta addini, sassabawar kabilu da kungiyoyi, kama-kama kuma sai sabanin ya ci gaba da yawaita har ya dauki sabon salo, wannan sabanin na biyu bai kasance ba sai saboda kiyayya ga wadanda aka ba wa littafi, zalunci da tsaurin kai, bayan komai na daga sanin addini da asullansa sun bayyana a gare su, kuma hujja ta tabbata a kansu, a saboda haka sabanin kashi biyu ne: Sabani ne a cikin al’amarin addini bisa la’akari da kiyayyar masu kiyayya wadanda suka yi watsi da sha’awa da fitirarsu, sai kuma sabani a cikin lamurran duniya wanda shi ma a bisa fitira wanda kuma wannan shi ne ya haifar da samar da shar’anta addini, sai Allah subhananu wa Ta’ala ya shiryar da muminai zuwa ga gaskia wadda aka yi sabani a cikinta da izininsa, kuma Allah shi ne mai shiryar da wanda ya so zuwa ga hanya madaidaiciya.
Don haka addinin Allah shi ne dalili kwaya daya rak wanda zai samar da dacewa da rabo ga mutum, kuma shi ne mai kawo gyara a cikin lamurran rayuwarsa, yana gyara fitira da fitira, yana daidaita karfinta mabambanci a yayin dagawarsa, yana tsara wa mutum salon rayuwarsa ta duniya da lahira, da ta madi dinta da ta ma’anawi. Wannan dai shi ne tarihin rayuwar mutum a dunkule (rayuwar zamantakewa da ta addini), game da abin da wannan ayar ta yi tsokaci a kai. (Tafsirin Al-Mizan; mujalladi na 2, shafi na 113).
A nan ne za mu samu cewa ashe tun a asali fitira ta dam adam da kuma a addini hadin kai da kuma taimakon juna su ne abubuwan da suka kasance a tsakanin mutane gabaki dayansu. Duk da cewa hatta kafirai sun sha kasance wa abokan zama ga muminai musamman idan muka kalli bangaren ‘yan adamtaka, wanda kuma har taimakon juna ma yakan iya shiga a tsakaninsu, madamar dai ba su kasance kafirai masu cutar da addini ko cutar da ma’abota addinin ba, sai dai duk da haka su kafirai ba za su taba kasancewa wadanda za a zama abu guda da su ko a kulla ‘yan uwantaka ta addini da su ba . A nan ne za mu ga koluluwar ma’ana da muhimmancin ‘yan uwantaka, domin kuwa ita wata wasila ce ta hakkakuwar abin da Allah yake so. Gabaki dayan Annabawan da Allah ya aiko sun tsayu tsayuwar daka wajen ganin hakkakuwar wannan lamari na ‘yan uwantaka a addini, haka nan ma lokacin da Annabi Muhammad (s.a.w.a) ya zo mana da musulunci ya karfafi wannan lamari, kuma ya kwadaitar tun a farko-farkon kiransa, ta yadda ya hada kan al’umma suka zama tsintsiya madaurinki daya, wadanda suka kasance kafin wannan lokacin a can baya suna gaba ne da yakar juna, amma sai ga su a cikin inuwa guda ta musulunci suna kauna tare da taimakon junansu, sannan suka manta da duk abin da ya faru a baya na yake-yake da rigingimu.
A wata ayar kuma Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:
[إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ] (سورة الحجرات الآية 10).
Tabbas muminai ‘yan uwan juna ne, a saboda haka ku yi sulhu a tsakanin ‘yan uwanku biyu, kuma ku yi takawa ga Allah, domin rahamarsa ta shafe ku. (Suratul Hujurat aya ta 10)
Ya zo a tafsirin Amsal, sheikh Nasir Makarim Shirazi yana cewa:  Jumlar (Tabbas muminai ‘yan uwan juna ne); wadda ta zo a cikin wannan aya mai girma, cewa daya ce daga cikin take na asasi kuma tushe ne na musamman a musulunci, haka nan ma lallai take ne mai zurfi, cike da hikima, tasiri tare da cikakkiyar ma’ana mai tarin yawa…..
Za mu ci gaba insha Allah.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: