bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:22:17
ba wanda zai ce wannan siyayyar ta tashi daga matsayinta na siyayya ta komo kyauta ba. Don haka dangantakar da ke tsakanin auren mutu'a da na da’imi sun yi kama da wannan misalin (Matajir, 11, 299).
Lambar Labari: 273

A yayin yin raddi (maida martani) ga waxanda suka ce aure mutu'a na iya komawa aure da’imi idan ba a ambaci lokaci ba, Shehul Ansari ya ce: auren mutu'a da na da’ima abubuwa ne biyu masu bambanci bayyananne. Ko da yake ana anfani da kalmar 'Aure' a dukkannin su, amma wannan ba zai sa su zama tamkar abu xaya ba. Bambancin dake tsakaninsu bai tsaya a kan cewa wannan na da sharaxi wancan kuma ba shi da sharadi ba. Dangantakar da ke tsakaninsu kamar tsakanin siyo abu ne da kuma karvar abu kyauta. A kowanne daga cikinsu sakamakonsa ko abin da yake tuqewa gare shi shi ne 'mallaka'. Amma cewar siyo abu da kuma samun kyautar abu suna da yanayi xaya, ba yana nufin dukkansu xaya ba ne. Ba za mu ce bambancin da ke tsakanin siyowa da samun kyauta kawai shi ne, samun kyauta yana nuna 'mallakar abu ba tare da sharaxi ba' kuma siyan abu na nufin 'mallakar abu da sharaxin biyan kuxi' kawai ba. Idan wani ya ce: 'Na siyar' sannan ya manta bai ambaci farashi ba, ba wanda zai ce wannan siyayyar ta tashi daga matsayinta na siyayya ta komo kyauta ba. Don haka dangantakar da ke tsakanin auren mutu'a da na da’imi sun yi kama da wannan misalin (Matajir, 11, 299).
A cikin littafin Sharhul lum'ah, Shahid Sani ya kawo cewa hadisin da ake hakaitowa daga Imam ja’far: (s.a) ba wai ya yi nuni cewa su ma’auratan sun so su xaura auren mutu'a, sai kuma suka qi ambatar lokaci ba ne, a a, abin nufi a wannan hadisi shi ne, auren da aka ambaci lokaci shi ne mutu'a wanda kuwa ba’a ambaci lokaci ba, to wannan ne da’imi (Sharhul Lum'a 5, 287).
Babu mafi tsawo ko qanqantar lokacin da auren ke iya xauka. Babu wani bambanci tsananin tsawon auren ko da kuwa akwai tabbacin cewa ma’auratan ba za su kai wannan lokaci a rayuwa ba, ko kuma ya zama ya yi qanqantar da ba za a iya samun damar yin jima’i ba. Ma’ana dai, kowane lokaci aka xauka ya yi, matuqar dukkansu sun fahimci yanayin kuma sun gamsu (Ibid 285).
Da zarar an qulla auren, matar nada gaba xayan sadaki, an samu damar yin jima’i ko ba a samu ba in dai lokacin bai wuce ba, matar ta mallaki sadakin matuqar ta miqa kanta ga mijin domin jima’i sannan ba ta haifar da wata matsalar da hakan zai qi yiwuwa ba. Wannan yanayin ya yi kama da karvar hayar gida, amma ba a zauna a gidan ba har kuxin hayar ya qare. Idan lokacin mutu'ar ya qare matar ta kuvuta daga haqqin auren (Matajir 11, 300 Jawahir 5, 170).
Bai halatta ma’auratan su iyakance adadin jima’in da za a yi ko wani abu mai kama da haka, ba tare da sun yanke lokacin auren ba, tun da wannan ba zai nuna tsawan lokacin auren mutu'ar ba. A ra’ayin mafi yawan malamai, idan irin wannan auren ya kasance, ba za a iya canja shi zuwa da’imi ba, tun da an yi kuskuren iyakance lokaci.
Amma idan an ambaci iyaka tare da iyakance adadin jima’in da za a yi, wato iyakar wa’adin auren an faxa kuma aka qara da ambatar adadin jima’in da za a yi a tsawon wannan auren, to auren ya yi wannan hukunci an ciro shi daga faxin Manzo (s.a.w): 'muminai su yi riko da sharuxansu da kyau (yayin da suka ambace su a yarjejeniyar `ya`yansu)' (Sahihul Bukhari N.P 1378/1958, 111,120). A wannan sharaxi ko iyakokin, da zarar mutum ya kammala adadin jima’in da suka iyakance to qarawa a kan hakan haramun ne ko da kuwa lokacin da aka xibawa wa’adin auren bai qare ba. Babu wani cin karo da juna tsakanini ci gaba da auren da kuma hana jima’in.
Abu mai rikitarwa game da abin da aka ambata a baya shi ne, yiwuwar ita matar da wa’adin aurenta bai qare ba, kuma jima’i da ita ya zama haramtacce, sai matar ta ba mijin damar sake yin jima'i da ita. Shin akwai damar yin jima’i ko babu? A nan akwai ra’ayoyi biyu, Ra'ayi na farko ya tafi a kan cewa akwai hani mai tsananai kan yin jima’in, domin sharaxin kulla auren da aka yi tun asali bai bayar da damar ci gaba da jima’i ba, dan haka maganar neman yardar matar ba shi da muhimmanci, tun da ba zai yiwu a kawar da sharaxin qulla aure domin haltta jima’i ba. A ra’ayi na biyu kuwa, jim’i ya halatta. tun da a auren mutu'a, savanin da’imi mace ba ta da ‘yancin farar da jima’i, abin da yake matsala a cikin abin da ya shafi jima’i a irin wannan yanayin shi ne rashin yardar matar na aiwatar da wani abu wanda yake babu shi a sharaxin aure. Amma shi auren mutu'a a kan kansa ya yarda da jima’i yayin da aka qulla shi don haka Idan aka cire kangiyar (ta sharaxi), shi kenan komai sai ya tafi (Matajir 11, 300).
Idan tsawon wa’adin mutu'a ya haxa da iyakance adadin jima’i, duk lokacin da adadin ya qare, mijin ba shi da wani haqqi a kanta, Ba kuma sai an faxa ba cewa idan ba a aiwatar da dukkanin adadin jima’in da aka sharxanta ba, kafin qarewar wa’adin auren, duk da haka auren ya qare (Ibid).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: