bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:28:06
إِيلَافِهِمْ رِحْلَةَ الشِّتَاءِ وَالصَّيْفِ (2) Sabawar su da yin tafiya cikin sanyi (hunturu) da zafi (bazara).
Lambar Labari: 275
سورة قريش

SURATUL QURAISH (SURA TA 106)

Wannan sura da aka sani da suratu quraish ko ace surar quraishawa da Hauwa, quraishawa qabilu ne da ke yankin larabawa lokacin Manzo (SAW), amma yanzu sun yaxu sassa daban – daban na duniya, domin duk wanda ka ji sharifi ne a tsatson sa na ainihi daga Manzo (SAW) baquraishe ne, quraish kaka ne ga Manzo (SAW) da sunan sa ne wannan qabila ta shahara, quraish na daga salsalar Annabi Ibrahim (AS) ta tsatson annabi Isma'il (AS), da sunan wannan qabila aka ambaci wannan sura, yankin na da raunin tattalin arziqi, babu rayuwar wayewa da ci gaba a yanki sama da kilo mita 1000 gabas da yamma kudu da arewa sahara ce, waje ne busashshe, don haka ne domin su rayu sai sun haxa da tafiye-tafiye zuwa Sham da Yemen lokacin sanyi da zafi don kawo abun rayuwa, shi yasa zaka samu cewa Manzo (SAW) ya yi tafiya sanda yana shekara 25 tare da ammin sa Abu Xalib (AS), sai Allah ya ni'imta su da zuwa a ziyarce su yayin da Allah ya sanya aikin Hajji a Makka bayan buxe Makka da Manzon sa (SAW) ya yi, har yau zamu ga arziqin Saudiyya bayan man fetur akwai shga da fice yayi ayyukan hajji da umra, sabida samun kuxin shiga da fita da ake yi wannan kawai ya ishe su ba sai sun yi ta safara ba, duk da cewa ba laifi bane yin tafiye – tafiye, amman yanzu ga hutu ya same su ba sai sun tafi ko ina ba, sai Allah ya saukar da wannan sura ya na mai yi musu wasiyya da su tsaya su bauta masa.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)

Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

لِإِيلَافِ قُرَيْشٍ (1)

Sabawar quraishawa (da wata al'ada).

إِيلَافِهِمْ رِحْلَةَ الشِّتَاءِ وَالصَّيْفِ (2)

Sabawar su da yin tafiya cikin sanyi (hunturu) da zafi (bazara).

فَلْيَعْبُدُوا رَبَّ هَذَا الْبَيْتِ (3)

Su bautawa ubangijin wanna xaki (Ka'aba).

الَّذِي أَطْعَمَهُمْ مِنْ جُوعٍ وَآمَنَهُمْ مِنْ خَوْفٍ (4)

Wanda ya ciyar da su daga yunwa, ya kuma amintar da su daga (dukkan) wani tsoro. (sakamakon fashi da ake musu wasu lokutan sannan sun fi qarfin mamayar manyan dauloli sabida zaman su babbar daula).

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id

+989368244976, +2348068985568

Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: