bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      08:23:57
Bana nufin kiran sa da sunan irfanin shi’anci, babu banbanci cikin kasantuwar mai imani dan shi’a ne ko dan sunna.
Lambar Labari: 282
Tsokaci kan irfanin muslunci cigaba kan kashi na farko
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Dukkanin yabo da godiya sun tabbata kan ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata kan fiyayyen halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Ingantaccen irfanin muslunci karkashin hasken kur’ani da Ahlil-baiti kadai yana kasancewa igiya mai sadar da bawa da ubangijin sa, Allah matsarkaki ya halicci mutum yayi huri cikin sa daga ruhin sa- shi ruhi wani Mala’ika ne mafi girma daga Jibrilu (as) ya danganta shi zuwa gare shi domin daukaka shi, mutum da sabuwar tsiruwar sa yana cikin mafi kyawun tsari, albarku sun tabbata ga Allah mafi kyawun masu halitta.
Bana nufin kiran sa da sunan irfanin shi’anci, babu banbanci cikin kasantuwar mai imani dan shi’a ne ko dan sunna, domin akwai wadanda suke karbar irfani daga Ahlil-baiti (as) kamar misalin Sufaye; domin cewa sun kasance tsakankanin irfani da sufanci kamar yanda na ambata, akwai mas’aloli da yawan gaske da suke da kamanceceniya da juna, sai dai cewa akwai mihwari jigo da yake banbance tsakanin irfani na asali da kuma sufanci da yake gwamutse cikin makarantunsa, muna da makarantun sufanci fiye da dari uku da suke raya sufancin su  daga kyallen su suna karba daga murshidin su da shehin su, shi kuma Shaik yana karbowa daga shehin sa, silsilar sufanci tana tukewa da karkarewa zuwa ga Albarki sannan kuma ta tsallaka zuwa ga Imam Rida (as) sannan zuwa Sarkin muminai Ali (as) makarantun sufancin sunna da na shi’a baki dayan su tarihin sufancin su yana komawa zuwa ga Sarkin muminai kan cewa shi ne waliyin dukkanin waliyyai da kuma daga gare shi aka karbi kyallen, tabbas Sarkin muminai ya karbo kyallen daga Manzon Allah sannan shi kuma Manzon Allah (s.a.w) ya karbo daga Allah matsarkaki madaukaki, da wannan zaka ga akwai fuskar kamanceceniya da juna mai yawan gaske tsakanin irfani na asali da muke Imani da shi da sufanci, daga nan zaka kiya samun dan sunna da yake kan irin irfani da muke Imani da shi, hakan na kasantuwa karkashin kur’ani mai girma da Ahlil-baiti tsarkaka, saboda hakan a kowanne lokaci muke mai da hankali kan cewa mu irfanin da muke imani da shi wanda kofofin sa suke bude ga gobe mai zuwa da sasanni sababbi insha Allah, lallai an samu masu tahkiki cikin wannan fage, ma’ana irfanin da ya ginu kan kur’ani mai girma da tsatso tsarkaka, da zamu koma tarihin irfanin muslunci za mu samu cewa shi yana daga cikin daya daga ilimummukan muslunci, lallai irfani yana danganewa da dayan biyun sinfofi daga ilimummuka.

Na farko: ko dai ya dangane zuwa ga sinfin ilimummukan assasar su wadanda muslunci ya shuka irin su kamar sauran ilimummuka, misalin fikihu da ilimin tafsiri da hadisi da abin da ya yi kama da haka.

Na biyu:  ko kuma ya dangane zuwa ga sinfin ilimummukan da mutane suka assasa su wadanda mutum ya shuka irin su ya kuma ba da gudummawa cikin habbaka su da tace su, sannan muslunci da musulmai ya kara musu cigaba kamar misalin ilimin likitanci da physics da falsafa da abin da ya yi kama da haka.

Nayi Imani cewa muslunci kammalallen addini ne
 ﴿اليوم أكملت لكم دينكم﴾، ﴿ومن يبتغِ غير الإسلام ديناً فلن يُقبل منه﴾،
Yau ne na cika muku addininku. Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gare shi ba.

Hakika ilimin mutanen farko da na karshe da dukkanin abin da yake ingantacce cikin dukkanin ilimummuka da fannoni kadai dai daga littafin muslunci yake ma’ana cikin kur’ani mai girma, yana tsono hasken imgantaccen ilimin irfanin muslunci daga Assaklaini-littafin Allah da tsasto tsarkaka, saboda haka tushe na farko uwa ga ilimin irfanin muslunci shi ne littafin Allah da sunna tsarkakka da hanyar A’imma tsarkaka.

Umar Alhassan Salihu
faroukumar@gmail.com


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: