bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      09:32:37
lallai kowanne Annabi yana da makiyi, lallai Allah ya aiko Annabi domin shiriyar da mutane da tsayar da adalci sannan kuma ya umarce shi da yakar dawagitai tun farkon da’awarsa har karshen numfashinsa
Lambar Labari: 285
Annabawa sune mabubbugar albarkoki ita albarka alheri ne mai tarin yawa madawwami tabbatacce kamar yanda yake a luggance, shi kuma malami magajin Annabawa ne cikin albarkarsu, su albarkantacce ne cikin rayuwarsa da alkalaminsa da kafarsa da bayaninsa da fuskarsa domin shi kamar misalin kyandir ne (candle) yana kone kansa haskaka mutane, ya zama wajibi malami ya kasance mabubbugar alherai da albarkoki cikin assasawa da gudanar da ayyukan addini da sakafa da taimakon jama’a kamar misalin gina makarantu da asibitoci cikin gari da masallatai da husainiyoyi da yada ilimummuka na gaskiya da dukkanin shakalansu da makamantan haka.
 7-gado na jihadi: lallai kowanne Annabi yana da makiyi, lallai Allah ya aiko Annabi domin shiriyar da mutane da tsayar da adalci sannan kuma ya umarce shi da yakar dawagitai  tun farkon da’awarsa har karshen numfashinsa, zargin mai zargi bai damunsa kan sha’anin Allah, kuma kiyayya masu girman kai ba ta dakushe himmarsa, haka lamarin yake kan malami lallai shi wani yanki daga yankin shiriyar da mutane zuwa hanya madaidaiciya da yakar dawagitai da jabberai da dukkanin mai yunkurin bautar da mutane da cin gallarsu da shagaltar da su daga barin bautar Allah da neman kusanci zuwa gare shi, hakika Allah ya fifita mujahidai kan mazauna da lada mai girma. Malamai kamar Annabawa suna yakar makiyan Allah makiyan addinin sa.
8- gado cikin nauyin ukuba: hakika Annabi sakamakon barin abin da ya kamata da yayi ya fita daga aljanna  kamar misalin Adamu (as) Annabta ta fita daga tsatsonsa kamar yanda ta faru da Yusuf (as) yayi kuka da raraji tsawon rayuwarsa har ta kai ga an kira da shi da Nuhu, to haka zalika malamai lallai yanda lamarin yake ana gafartawa jahilai zunubi saba’in gabanin gafartawa malami zunubi daya, idan har ya zamanto kyakkyawan aikin rabautattu mummanan makusanta ce kamar yanda ya zo a riwaya, to haka zalika kyawawan aikin jahilai munanan aiki ne ga malamai, mafi kankantar abin da za a yi wa malami mai aikata zunubi shine raba shi da jin dadin ganawa da Allah, malami nawa ne aka cire masa ni’imar ilimi sai ya wayi gari ya fita daga zirin malamai yayin da ya zamanto bay a aiki da iliminsa ya kuma wofinta da nauyin da yake kansa daga shiriyar da mutane da nusantar da su.
Ya zo cikin maduakakin hadisi cewa malamin da bay a aiki da iliminsa yake kuma sabawa ubangijinsa yana jarrabtuwa da dayan uku: ko dai mutuwa yana saurayi, ko zama hadimin sarki kamar misalin malaman fada, ko kuma ya kasance cikin fili gona.    
9-gado cikin hukuma: Annabta shugabanci ne cikin harkokin addini da duniya da nassi daga Allah matsarkaki, Annabi shine jagoran mutane cikin addinin su da duniyar su, lallai addini tsari ne kuma daula ne ya zo cikin madaukakin hadisi cewa malamai sune jagorori, sune magada Annabawa cikin shugabancin su ga jama’a zuwa alherai da kawo gyar, lallai da sannu bayin Allah nagargaru zasu gaje kasa kamar yanda nassin Kur’ani yayi bayanin hakan lallai kuma galaba tana ga Allah da manzanninsa:
 ( لاغلبن انا ورسلي )
Tabbas ni da manzannina za mu yi galaba.
Malamai sume masu jin tsoran Allah
 ( انما يخشى الله من عباده العلماء )
Kadai masu jin tsoran Allah daga bayinsa sune malamai.
Ilimi yana kira zuwa ga gyaruwa da kawo gyara kamar yanda shi gyara dama yana tareda ilimi, bayin Allah salihai wadamda za su gaji kasa sune malamai nagargaru mafi alheri, lallai su ne jagorori masu shiriyarwa kuma hannunsu ragama al’amura yake sune zasu riki madafin iko karkashin sanya idanuwansu tafiyar da hukuma zai kasance sune magada Annabawa.
 10- gado cikin dabakoki: Shaik Saduk (r) cikin littafinsa Attauhid yana cewa: hakika annabawa daba-dabake ne hawa-hawa ne a cikinsu akwai wanda yake an aiko shi ga iya kansa akwai kuma wanda iya danginsa akwai wanda iya yankinsa akwai kuma na iya kasarsa, akwai kuma Annabawam da aka aiko su ga baki dayan duniya sune Ulul Azmi ma’abota litattafai na duniya baki daya a zamaninsu har zuw akan cikamakin Annabwa da manzanni Muhammad shi sakonsa ya kasance ga baki dayan mutane lallai shi rahama ne ga dukkanin halittu, kuma halal dinsa halal ce har zuwa tashin Alkiyama haka ma haram dinsa haram ce har tashin alkiyama.
Malamai magada Annabawa daga cikinsu akwai wanda ake kasancewa cikin mukamin tseratar da kansa da wasunsa.  
 ( قوا انفسكم واهليكم نارا)
Ku ceci kawukanku da iyalanku daga wuta.
Da kuma jagorantar siyasar mahallinsa da kuma kasancewa limami a masallaci da warware matsalolin mutane da rayuwa cikinsu da tseratar da kasa zuwa gabar azurta da alheri, ta iya yiwuwa sakonsa ta kasance ta dukkanin duniya ta kuma kasance baki dayan duniya ta amfana da ita da ilimin da ke tattare da ita mai albarka, kamar misalin maraji’an taklidi Allah ya saka musu da alheri, kadai Allah ya na wurga ilimi cikin zuciyar wanda yake so, su zukata kwaryoyi mafi alherinsu it ace mafi kiyayewarsu, wajibi kan dukkanin duniyar musulmi suyi duba mafi nisan duba cikin mutane su fadada tunaninsu da azamarsu da nishadinsu da siyasarsu  sun shiri da tsari ga kowacce al’umma su himmatu al’amuran musulmi lallai duk wand aya wayi gari bai damu da al’amuran musulmi shi ba musulmi bane yaya kuma ga malamai wadanda su ne jagorori makiyayaز
Wannan Kenan sannan daga cikin alfahari ga malamanmu shi ne kasancewa sune suka gaji Annabawa har ya zamanto cikin hakkinsu an ce:
 ( علماء امتي كانبياء بني اسرائيل )
Malaman cikin al’ummata kamar misalin Annabawan Banu Isra’il ne.
 A wata riwayar kuma
 ( افضل من انبياء بني اسرائيل )
Sun fi daraja daga Annabwan cikin Banu Isra’il.
Wannan wani takaitaccen bayani ne ga wasu ba’arin sasannin gadon Annabawa sannan akwai gomomin sasanni kamar yanda cikin kowanne sashe guda daruruwan sasanni suke reshentuwa. Ba a baku komai daga ilimi ba face kankani.
Kamar yanda sukai zamani da ma’asumai goam sha hudu ma’ana manzon Allah (s.a.w) Fatima Ali Hassan da Husaini da mutane tara daga `ya`yan Husaini (as) domin ai gabansu ne kalaman imaman tsira suka kasance a zamaninsu kuma a cikin majalisansu suka sha ilimi wanda wannan na nuni da cewa wadanda sukai zamani daya da su suka zauna gabansu sun kwankwadi ilimi da kyawawan dabi’u daga garesu.
Wannan wani dan takaitaccen bayani ne daga sasannin gadon annabawa akwai gomomin sasanni da suka rage wadanda zamu yi bayaninsu nan gaba.
Karshen zancenmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.
Umar Alhassan Salihu
+2348162040719

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: