bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      09:42:28
Bahasi shaidu ya ta’allaka da ilimin Irfani, saboda haka za mu yi tambaya mene ne Irfanin muslunci?
Lambar Labari: 287
 Dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata kan fiyayyen baki dayan halittu da iyalansa tsarkaka
Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma yana cewa:

﴿يرفع الله الذين آمنوا منكم والذين أُوتوا العلم درجات﴾
Allah yana daukaka darajar wadanda suka yi imani da wadanda suke da ilimi.

Cikin sharar fage zamu Ambato shaidu daga wurin Ahlil-baiti (as) daga nan kuma sai mu tsallaka zuwa ga Imam Husaini shugaban shahidai da kuma abin da ya kasance daga shaidu cikin Karbala mai tsarki a yinin Ashura da daren ta.
 
Bahasi shaidu ya ta’allaka da ilimin Irfani, saboda haka za mu yi tambaya mene ne Irfanin muslunci?

Maganganum dangane da Irfani”
Akwai mutanen da sukai wasti da Irfani mudlakan, musammam ma cikin hauzozin ilimi da muke da su, akwai kuma wadanda suka karbe shi mudlakan, akwai kuma wadanda suke karbarsa tare da dabaibayin sharadi.

Shin Irfanin muslunci yana daga cikin ilimummukan muslunci ko kuma dai yana daga ilimin da dan Adam ya samar da shi?

Irfani a cikin isdilahi da kuma ilimance tarihinsa yana komawa zuwa ga falsafa, sannan ita kuma falsafa tanada tsohon tarihi cikin zauruka karatuttukan zamani na Rumawa da Girkawa a yammacin turai, haka wurin Fahlawiyyun da Indiyawa a gabashin duniya, hikima da falsafa suna da tarihi mai tsaho da fadin gaske, almajiran malami na farko ma’ana malam Arasto sun kasu zuwa sinfi uku, sinfi da yake biye da shi yake karbo falsafa daga daga gare shi wadanda aka fi sani da suna Masha’iyyawa, da kuma sinfi na biyu cikin makaranta da filinta sun karbi falsafa daga gare shi sune wadanda suka shahara da sunan Rawwakiyun, da kuma sinfi na karshe wadanda suka kasance kamar suna kallon malaminsu ne suna karbar falsafa da hikima daga gare shi da mahangar Ish’raki, sune wadanda suka shahara da sunan  Ish’rakiyyun,

Irfani ya samu ne daga mahaifar ish’raki, saboda haka ne ma ilimin Irfani yake komawa zuwa ga Falsafa da tarihinta, da wannan ne zai iya zama ilimin da dan Adam ya samar, ma’ana tubali na farko da aka sanya shi a matsayin isdilahi kuma kamar matsayin tadwini na ilimi kadai ya kasance daga hannun mutum, tabbas babu shakka cikin kasancewar dukkanin ilimummuka daga Allah matsarkakke suke daga kuma annabawan sa suke- wannan shi ne abin da muka yi imani a kai- sai dai cewa a matsayin rubutaccen ilimi da sanyawar ilimi kadai sun kasance daga hannun dan Adam, sannan daga cikin ilimummuka akwai wadanda suka kasance a hannun Allah kamar yanda ya zo cikin madaukakin hadisi:
 
«إنّما العلم آية محكمة، أو سنّة قائمة، أو فريضة عادلة»،
Shi ilimi kadai dai aya ce bayyananniya, ko kuma sunna tsayayya, ko farilla adala.

Ma’ana ilimummukan muslunci nau’i uku ne: ilimin sanin Akida, da ilimin Akhlak da ilimin fikihu.

Maganganu dangane da mutumin da ya assasa ilimin Irfani:
Akwai sabani cikin musulmai kan wane ne ya assasa ilimin irfani? Shin wai shi wannan ilimi na irfani yana daga cikin jerin ilimummukan muslunci ko kuma dai kirkirar dan Adam ne? Daga cikin manya masana- musammam ma daga masanan gabashin turai akwai wanda ya tafi kan cewa ilimin irfanin muslunci lallai fa ba daga musluncin ya samo asali ba, bari dai wani abu ne da aka cudanyo shi daga wajen muslunci aka shigar da shi cikin muslunci, an ce: daga malaman kiristanci yake, wasu kuma sun ce: daga sufancin Indiyawa da Budawa ya samo asali, Irfani ya shigo cikin muslunci ne daga budanci, daga cikin su kuma akwai wanda ya mayar da shi zuwa ga Yahudawa, akwai kuma wanda ya komar da shi zuwa ga falsafa, masana falsafa da hikima sun sassaba kan haka, sai dai cewa mu abin da muke imani da shi shi ne cewa ilimin Irfani muslunci kadai dai shi daga muslunci yake, muslunci ne ya samar da shi, domin cewa shi yana iya sabawa ta fuskanin maudu’i da kuma fuskanin dokoki da hanyoyi, kamar yanda kuka sani shi sassabawar ilimummuka kadai dai yana kasancewa cikin maudu’i, da mahmuli da agraz ilimummuka sashen su ka iya sabawa daga sashe, maudu’in ilimin irfani yana sabawa da sauran ilimummuka, sannan shi irfanin muslunci ya kasu zuwa makaranta biyu: makarantar sunna da makarantar shi’a, adadi mai yawan gaske daga malamai sun tafi kan cewa lallai fa shi irfani nan ba wani abu bane face sufanci, dama fuskar sufanci ta biyu shine irfani, daga manyan masana da suka tafi kan wannan ra’ayi akwai Shahid Mutahhari (a.r) ta yanda dangane da irfanin muslunci ya bayyana cewa: lallai shi irfani da hankalin nazari kadai shi ne irfani, sai dai kuma cewa ta hanyar hankalin ilimi kadai dai shi ba wani abu bane da ya wuce sufanci, ma’ana dai Arifi shi ne Sufi, sannan zaka samu akwai wadanda suka zare takobin yakar irfani da wadanda ake kira da Arifai sakamakon sun fassara irfani da sufanci, shi kuma sufanci abin wurgi ne a makarantar Ahlil-baiti (as) muna da hadisai masu tarin yawa daga Ahlil-baiti (as) kan cewa dukkanin wanda ya taimakawa Sufi daidai yake da wanda ya taimaki Yazidu bn Mu’awiya kan kisan Imam Husaini (as), sannan cikin wannan zamani da muke ciki- musammam ma bayan samun nasarar juyin-juya halin muslunci a Iran da jagorancin Imam Komaini (rd) zamu ga cewa an bude kofa dangane ilimin irfani, saboda haka wajibi mu zage dantse mu san ingantaccen irfani lafiyayye, wanda ya ginu kan kur’ani da Ahlil-baiti, ma’ana muna karbar irfanin muslunci wanda maudu’in sa ya doru kan tubalin sairi da suluki zuwa ga Allah matsarkaki, sannan baki dayan  dokokin sa da mas’alolin sa ana karbo su daga kur’ani mai girma da Ahlil-baiti tsarkaka.     

Babu shakka kan cewa daukakar mutum da girman sa kadai suna kasancewa ta hanyar hankalin sa da zuciyar sa, sakamakon Allah ya halicci mutum cikin mafi kyawun tsari da zubi, ya rakkaba shi da turbaya daga kasa domin ya kasance mai tawali’u, kamar yanda ya rakkaba shi da Mala’ika daga samaniya da ruhu daga gare shi domin ya daukaka, lallai a wannan lokaci yana kasancewa tsakankanin baka biyu bakan nuzuli da bakan su’udi, lallai shi yana sauka daga madaukaka cikin bakan nuzuli ya zuwa kasancewa cikin gidan duniya makaskanciya, sannan bayan haka daga wannan gida na duniya daga turbaya da kasa da mala’ikantaka yana tsallakawa ya hau zuwa malakutul A’ala, ya zuwa subuhiyya da kuddusiyyar Allah, sai ya kasance cikin hallarar Allah madaukaki, domin cewa ita duniya hallarar Allah ce saboda haka ka da ka sake ka aikata sabo cikin hallarar sa, ya daga zuwa bakan su’udi, cikin wadannan baka guda biyu bakan su’udi da nuzuli kadai anan irfani yake kasantuwa, irfani a dunkule kadai yana tajalli cikin fadin sa madaukaki:  
﴿إنّا لله وإنّا إليه راجعون﴾،
Daga Allah mu ke gare shi za mu koma.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: