bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:45:44
Tsawun lokaci Manzon Allah (s.a.w) tareda Khadija da Aliyu bn Abi Dalib (a.s) suke fita gefen Makka domin yin sallah da sauran ibada, sukan yi sallar Azuhar a gefen ka’aba
Lambar Labari: 308

DA’AWAR MANZON ALLAH (S.A.W) A BOYE.

Imam Aliyu (a.s) a wannan lokacin da aka fara yiwa Manzon Allah (s.a.w) wahayi, ya karbi musuluncinsa sayyida Khadija kuma bayan komawar Manzon Allah (s.a.w) Gida daga kogun Hira da taji labarin Risalal Manzon Allah (s.a.w) ta karbi musulunci.

Tsawun lokaci Manzon Allah (s.a.w) tareda Khadija da Aliyu bn Abi Dalib (a.s) suke fita gefen Makka domin yin sallah da sauran ibada, sukan yi sallar Azuhar a gefen ka’aba kusa da ka’abar kuma kuraishawa a lokacin basa wani bijiro masu. A wannan yanayin Manzon Allah (s.a.w) ya yi Magana da wasu dai dai kon mutanen wannan yankin sannan ya kira su zuwa ga musulunci. A wannan lokacin Manzon Allah (s.a.w) baya aibata gumaka sannan bai fara Magana akan cew mushirikai batattu bane saboda shirker da suke yi ba, musamman akan akidar su. Su kuma mushirikai basu ma damu da Akida da kuma abinda Manzon Allah (s.a.w) da Sahabbansa suke yi ba a wannan lokacin, duk da suna kallon abinda suke yi amma ba wani bijirowa da suka rikayi a lokacin, kawai dai abinda suke yi shine idan Manzon Allah (s.a.w) ya zo wucewa ta kusa dasu sai a rinka nuna shi ana dariya suna cewa: Muhammad kuma yanzu da sama Magana(1)[1].

Babban dalilin da yasa kuma Manzon Allah (s.a.w) ya daukin wannan matakin a wannan lokacin shine musulunci a wannan lokacin yana da raunin sosai, idan kuma Manzon Allah (s.a.w) ya ce zai dauki matakin da ba wannan ba a lokacin tabbas za a nemi musuluncin a rasa.

Wannan yanayin na kira a boye ya dauki tsawun shekaru uku ne har zuwa lokacin da samari da kuma talakawan kuraishawa suka yi imani da Manzon Allah (s.a.w) sannan kuma musulmi suka ya waita sosai. A wannan lokacin ne ayar (Anzir) ta sauka, akayiwa Manzon Allah (s.a.w) wahayi akan ya kira mutanensa na kusa da shi wato danginsa zuwa musulunci shi kanshi wannan kiran a bayyane yake, daga nan ne kuma kiran Manzon Allah (s.a.w) ya fara a bayyane(2)[2].

FARKON KIRAN MANZON ALLAH (S.A.W) ZUWA GA MUSULUNCI A BAYYANE.

An karbo daga Aliyu dan Abu Dalib (a.s): bayan saukar ayar ( wa anzir a shi ratakal akrabin), Manzon Allah (s.a.w) ya kira ni ya ce man: Ya Ali! Ubangiji ya bani umarnin na kira danginmu zuwa ga musulunci, saboda isar da wannan sakon na Ubangiji mai girma ka shirya abinci sannan ka kirawu yayan Abdul Maddalib zuwa gidana zanyi Magana dasu.

Aliyu (a.s) yake cewa: hakan kuwa nayi, a wannan lokacin yayan Abdul Maddalib kimanin mutum Arba’in ne (40) inda suka taro a Gidan Manzon Allah (s.a.w), bayan gama cikin abinci ne yaso ya fara Magana da su, amma Abu lahab ya hana yanata wasu maganganu marasa kan gado.

Washe garin wannan ranar a karo na biyu Manzon Allah (s.a.w) ya sake kiransu gaba dayansu a matsayin bakinsa a wannan karon bayan gama cin abinci sai ya fara da cewa: Ya ku yayan Abdul Maddalib! Ni bansan wani wanda ya zo wa da mutanensa wani abu fiye da abinda na zo muku da shi ba. Na zo muku da rabauta ta Duniya da lahira, Ubangiji ya bani umarni da in kira ku zuwa ga musulunci.

Bayan haka ne kuma Manzon Allah (s.a.w) ya yi wa Danginsa alkawarin cewa duk wanda ya amshi kiransa kuma ya yi imani ya musulunta shine zai zama wazirinsa sannan kuma shine zai zauna a matsayin halifansa a bayanshi kenan. Manzon Allah (s.a.w) ya mai maita wannan kiran har sau uku, amma a tsakaninsu ba wanda ya amsawa masa sai Aliyu bn Abi Dalib (a.s). A karshe Manzon Allah (s.a.w) ya gabatar da Aliyu bn Abi Dalib (a.s) a matsayin halifansa magajinsa, sannan ya nemi mutanensa da su saurari Aliyu da suyi masa biyayya. Wasu daga cikin Manyan kuraishawa wadanda suka zo wannan taron suka kama dariya suna cewa Abu Dalib: Yana baka umarni kayiwa danka biyayya! Wannan al’amarin daya faro tsakanin Manzon Allah (s.a.w) da kuma Danginsa a Tarihi ana kiran shi da (Yaumudar ko kuma Yaumul Anzar).

Bayan wannan abinda ya faru kuma Manzon Allah (s.a.w) ya fara kiransa zuwa ga Musulunci a bayyane inda su kuma wadannan sukaci gaba da bautar gumakansu.

Manzon Allah (s.a.w) wata rana ya tafi kusa da dutsen Safa, dutsen Safa dutsene mai tsawu sosai, sai Manzon Allah (s.a.w) yahau kan wannan dutsen ya kwala kira yana cewa:Ya sibah! Mutanen makka suna amfani da wannan Kalmar ne kawai lokacin da wani hadari ya tinkaro su, saboda haka cikin damuwa suka taro kusa da Manzon Allah (s.a.w). Manzon Allah (s.a.w) ya ce musu: Ya ku mutane! yanzu idan na baku labarin cewa a bayan dutsen nan makiyan ku sun tahu zasu kawo muku hari, shin zaku gazgata maganata? Gaba dayansu suka amsa masa cewa eh mana! Saboda mu dai bamu taba sanin wata karya da kayi mana ba. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: To ni na ganinku kuna neman fadawa azabar Allah, Ni kuma na zo ne domin na tseratar da ku daga wutar Jahannama(3)[3].

WAHAL HALUN DA MUSULMAI SUKA FUSKANTA.

Bayyanar musulunci a Garin Makka da zaman musulmi wata kungiya ta wasu samari ya girgiza manyan kuraishawa matuka ta yanda hatta ma da mata ba a barsu a baya ba wajen karbar wannan sakon. Saboda haka manyan kuraishawa basuyi kasa agwiwa ba wajen daukar mataki ba, inda suka yanke shawarar dan danawa musulmai kudar su a hannu. Da farko sun dauki matakin kulawa da samarin su da kuma matansu ta yanda ba zasu iya kaiwa da komuwa ba wajen Manzon Allah (s.a.w) wato yanda za a hanashi magana dasu. Sai kuma zuwa ga matafiya ta yanda suma za a hana su sauraren Manzon Allah (s.a.w), da kuma yima duk wanda ya yi imani da Muhammad azaba ta yanda za a tilasata wadanda suka yi imani da Manzon Allah (s.a.w) ko mawa ga bautar Gumakansu na asali(4)[4].

A wannan fito na fito din da mushirikai suka yi da Manzon Allah (s.a.w) ba wani abu suka yi ko Karin yi ba sai kawai su bada kariya daga Akidarsu; Duk da cewa akwai wasu daga cikin musulmai da suke bayyana imanin su a fili mushirikai sunyi ko Karin azabtar dasu sosan gaske, inda a wannan lokacin an samu wani gungu daga cikin musulmai wanda suka fita tsakanin Dutsen safa da marwa suna sallah da sauran ibadojinsu.

Wani gungu daga cikin mushirikai kuma sunzo wucewa ta wannan wurin kawai suka afkawa wannan gungun na musulmai, inda wajen kare kansu daya daga cikin musulmai mai suna Sa’ad bn Abi Wakas; ya dauki wani kashin rakumi ya daki wani cikin mushirikai da shi inda yajima wacan mushirikin ciwu da wannan kashin , wannan ya kara sawa mushirikai kaimin kara kara matsawa musulmai lamba sosai, wanda hakan ya yi sanadiyyar hana musulmai fitowa hatta ma wajen gari wajen duwatsun da suke zuwa don yin salla da sauran ibadarsu. saboda haka Manzon Allah (s.a.w) bashi da wani zabi wanda ya wuce zama tareda Sahabbansa a cikin gida a kulle. Kuma suka zauna a nan har zuwa tsawun wani lokaci. Wannan Gidan kuma yana kusa da dutsen safa ne. daya daga cikin musulman da suka zauna da Manzon Allah (s.a.w) a wannan wurin dashi akwai Arkam bn Abi Arkam, sun zauna da Annabi wannan wurin tsawun wasu yan watanni(5)[5].

Aminci ya kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabin mu Annabin Rahama, Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da kuma iyalen gidansa tsarkaka wadanda Allah ya tsarkake su ga barin duk wani sabo (a.s). aminci kuma ya tabbata wadanda suka bi shiriyarsu har yazuwa ranar sakamako.[1] Asadul gaba, J na 1, shafi na 19. Da kuma Addabakatil kubra, J na 1, shafi na 199.

[2] Suratu sha’ara aya ta 214. Da kuma Tarikul Yakubi, J na 2, shafi na 24.

[3] Musnad Ahmad bn Hambali, J na 1, shafi na 281. Sahihul Bukari, J na 6, shafi na 29. Dama Tarikul Dabri, J na 2, shafi na 68.

[4] Bidaya wannihaya, J na 3, shafi na 74. Da kuma Alka,il fittarik, J na 2, shafi na 66.

[5] Dabakatul kubra, J na 3, shafi na 9. Da kuma siratul Halbiyya, J na 1, shafi na 283.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: