bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:48:23
Rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka musu wajan warware matsalarsu kuma kawo ‘ya’ya duniya zai kara matsalar ne kawai, wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa kuma ba a kansa ba ne duniya take cece-kuce.
Lambar Labari: 31
Tsarin iyali da kaiyade su bahasi ne da ya tayar da jijiyar wuya da sabani tsakanin fikirori da addinai da mazhabobi a daya bangaren kuwa tsakanin al'ummu da gwamnatoci, muhimmancin bahasin ne ya sanya ni bayar da wani lokaci don bincike kansa gwargwadon yadda ya samu ba tare da tsawaita ba. Mafi muhimmancin bayani sun hada da ma'anarsa, dalilansa, halaccinsa, hanyoyin yin sa, bayanai kan tarihinsa, da tasirinsa cikin al'ummu ko daidakun mutane haka nan ma a gwamnatoci.

TSARIN IYALI KO KAIYADE IYALI
Tsara Iyali shi ne: Tsara haihuwar matan da suke saurin daukar ciki, da kuma marasa lafiya rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka musu wajan warware matsalarsu kuma kawo ‘ya’ya duniya zai kara matsalar ne kawai, wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa kuma ba a kansa ba ne duniya take cece-kuce. 
Amma kaiyade iyali: Shi ma ya kasu kashi biyu ne; Kaiyade Iyali da ya shafi mutum daya da gidansa da kuma kaiyade yaduwar nau’in dan adam a duniya da takaita yawaitar mutum a duniya ta hanyar kafa wata doka da zata hana yaduwar dan adam da yawaitarsa da kaiyade yawan dan adam. Wannan kashi na biyu shi ne abin da ake jayaiya a kansa, kuma duk wannan yana bayani ne kan Tsara Iyali ko iyakancewa. 
Don haka zamu iya cewa Tsarin Iyali Aiki ne na zabi ta wasu hanyoyi na musamman wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba domin rage ko tsayar da haihuwa da yaduwar dan adam. Hanyoyin sukan hada da daina saduwa, zubar da ciki, dakatar yiwuwar haihuwa, ko bayar da tazara. Wasu suna ganin: Tsarin Iyali wani aiki ne da yakan bayar da dama ga mutum ya kaiyade Iyalinsa ko tsara su domin taimaka wa ga warware matsalolin duniya da warwararsu ta dogara kan hakan, amma a wasu lokutan gwamnatocin kasashe ne sukan dauki alhakin gudanar da shi ga al’ummunsu, ya zama doka a kasa. 
Kafin bayanin Shari’ar musulunci da matakinta kan Tsara Iyali ba makawa mu yi bayani game da hanyoyin da mutane suke dauka wajan kaiyade ko tsara iyali wadanda sun hada da: -
1-Zubar da ciki: Wannan ita ce hanyar da ake dauka a mafi yawancin kasashe wato zubar da ciki ta hanyar shan kwayoyi ko wata hanyar daban. 
Hanyar zubar da ciki hanya ce da ake amfani da ita wacce ta shahara tun karni na sha tara. Akwai wasu masana da suka bayar da gudummuwa wajan samar da hanyoyi daban-daban na kaiyade iyali kamar; Adam Raciborski, likita a Faransa a 1843, da Hermann Knaus a Austria a 1929, da kuma Kyusaku Ogino a Japan a 1930. Amma game da Afrika a binciken da na yi ban sami wani bincike kwakkwara da aka rubuta game da kaiyade iyali a yankin Afrika da tarihinsa ba kamar yadda yake game da Asia mai nisa. Da akwai kuma wani nau’in kaiyade iyali da ya shahara a zamnin da a yankin Jaziratul-Arab na binne ‘ya’ya mata da ransu don tsoron talauci ko tsoron kada a ribace su a yaki. 
2- Azalu: Shi ne mutum ya kauce daga matarsa yayin kwanciya ya fitar da ruwan wajan farjinta yayin kawowa, daga cikin wani nau’i na Azalu a wannan zamani shi ne yin amfani da kwandom wato Robar da zata hana mani shiga farji. 
3- Jinkirta aure: shi ne kin yin aure da wuri domin kada a haihu har sai mace ta kusa tsufa ta manyanta tana mai shekaru masu yawa ta yadda da ta fara haihuwa shekarun da zata bar haihuwa zasu riske ta da wuri, Wannan ita ce hanyar da aka fi amfani da ita a Kasar Sin (Cana)
 4- Daina jima’i da mata baki daya domin sai an yi jima'i za a samu ciki da haihuwa. 
5- Amfani da kwayoyin hana daukar ciki ko allura: Wannan hanya ce da ta yadu a duk duniya. 
6- Hanyar lissafin kwanakin haila: Ita ce, Lissafin kwanakin haila da masani Ojino ya gano ta hanyar lissafin kwanakin hailar mace da tabbatar da tsayaiyun kwanakinta domin gano kwanakin da kwanta yake sauka, sai a nisanci wadannan kwanakin da kwana biyu kafin da bayan saukar kwan. Wato idan mace tana da haila tabbatacciya mai aiyanannun kwanaki tsayaiyu to wannan matar ita wannan hanyar take yi wa amfani banda sauran mata. Sai a san kwanakin da take haila, to daga ranar da take fara haila zuwa ranar sha biyu ba ta daukar ciki amma daga sha biyu daga ranar da ta fara haila zuwa sha shida to a wannan kwanaki tana iya daukar ciki sai a nisanci kusantarta. 
1 (11,12,13,14,15,16, 17) 30
Kwanakin daukar ciki
Kwanakin wata kwana talatin daga ranar da mace ta fara haila idan mai haila tabbatacciya ce ta fuskacin lokaci da adadin kwanaki. 
7- Hanyar Amerikawa: Ita ce hanyar amfani da wasu kwayoyi kewayaiyu da a kan sanya su cikin mahaifa suna da yanayi daban-daban kewayaiyu ko kamar kulli-kulli da a kan sa a mahaifa don hana daukar ciki. Wannan hanya ana amfani da ita tun lokacin Arasdo ga dabbobi, amma da aka jarraba a kan mutum bai yi aiki ba, Jamusawa sun aikata ta su ka bari da suka ga cutarta ta fi amfaninta. Kamar yadda wani Bajafane ya gano yadda take amfani sai suka ci gaba da amfani da ita, amma daga baya Amerikawa su ne suka ci nasara sosai a wannan hanya, idan an cire wannan kwayoyin halittar to bayan wata biyu ana iya daukar ciki. 
Wannan su ne hanyoyin da ake amfani da su wajan kaiyade ko tsara iyali kuma ta yiwu akwai wasu hanyoyin da mu ba mu san su ba da duniya mai nisa ko maras ci gaba take amfani da su. 
Yawancin wadannan hanyoyi da ake amfani da su musulunci ya halatta su sai dai wasu daga ciki da shari’a ta haramta kamar zubar da ciki da kuma ganin farjin muharramar mace ko ajnabiiya. Kuma duk abin da ba a haramta ba halal ne sai dai idan zai kai ga aikata haram. 
Wato wadannan ka’idoji ne da ake amfani da su a Ilimin Usul da cewa komai halal ne sai dai abin da aka yi bayani kan haramcinsa . Wannan ka’ida ce da aka tabbatar da ita a Kur’ani da hadisan Manzo (s.a.w) Saboda haka duk sa’adda babu wani dalili kan haramcin kaiyade iyali ko tsara su ta daya daga wadannan hanyoyi to ya halatta a aiwatar da ita. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: