bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:28:41
Batun mamaki da dariyar da Allah ya yi wa wasu mutane kan ayyukan da suka yi. Batun dariyar da Allah (s.w.t) ya yi wa wani wanda ya yi masa wayo
Lambar Labari: 312
Dariyar Allah
Duk wata siffa da Allah zai siffantu da ita dole ne ta kasance tana da kamala da babu wata tawaya gare shi da ta kunsa, idan muka samu ruwaya ta zo da siffar tawaya da iyaka da nakasu ga Allah (s.w.t) to nan take zamu yi hukunci da rashin ingancinta da shaidawa da rashin zuwanta daga ubangijin talikai da manzonsa mai hikima da daukaka.
Idan muka ba wa Allah wata sifar tawaya to yana nufin mayar da shi cikin ababan halitta da suka rasa kamala, rasa kamala kuwa yana nufin ke nan ya bukaci mai cika shi domin duk mai tawaya yana da mai cika shi wanda ya jingina da shi don samun kamalarsa, don haka sai ubangijin talikai ya tashi ba Ubangiji ba ke nan, alhalin shi ne ubangijinsu.
Dariya tana daga cikin abin da ruwayoyin da suka zo daga ingantattun litattafan ‘yan Sunna da suka tabbatar wa Allah madaukaki. Wannan lamarin na dariya ya zo a cikin ruwayoyi mabambanta tun daga Buhari da Muslim da sauran litattafai da suka kunshi batutuwa kamar haka:
Batun mamaki da dariyar da Allah ya yi wa wasu mutane kan ayyukan da suka yi. Batun dariyar da Allah (s.w.t) ya yi wa wani wanda ya yi masa wayo har ya samu Allah ya shigar da shi aljanna. Batun dariyar da ya yi wa mai kisa da wanda aka kashe saboda wanda ya yi kisa shi ma daga baya ya tuba ya shiga aljanna. Ya kai ga Abuzariin yana cewa ya tambayi manzon Allah (s.a.w) shin Allah ma yana dariya. Sai ya ce: Ba mu rasa ubangijin da yake dariya ga alheri ba, (Buhari: j 5, h 3578. J 4, h 4707. Muslim: j 6, kitabul imara; b 35, h 1890. Muslim: kitabul a’ayan: b 83, h 273. Sunan Ibn Majah). Hadisan sun tattara abubuwa da suka ci karo da kamalar Allah da girmansa kuma hankali kuButacce ba zai karBe su ba, da suka hada da:
Cewar Allah yana mamaki ya yi dariya kamar mutum. Yana yaudaruwa da har bawansa zai ta yaudare shi har sai ya kai shi cikin aljanna. Sannan wane Ubangiji ne mai rahama da zai sharadi da bawansa ka da ya tambaye shi rahamarsa! Kuma me ye na karya wannan alkawarin da Allah yake yi ya sake yin wani sharadin da alkawarin da bawa kuma ya yi ta karyawa duk a matsayi daya kan lamari daya!.
Wane irin lamari ne zai samu bawa har ya gaya wa Allah magana yana ce masa yaya zaka yi mini izgili kana ubangijin talikai?!. Sai Allah ke nan ya kasance a matsayin wanda bawansa yake tuhuma! Kamar dai bawan ya ki yarda da Ubangiji yana ganin shi ma zai iya yaudararsa kamar yadda ya yaudari Allah ya yi masa wayo!.
Wannan shi ne sakamakon abin da zai kasance a irin wadannan ruwayoyin da suka saBa wa littafin Allah da sunnar annabinsa mai inganci.
Cirata Daga Wuri
Akwai hadisai da aka samu a cikin Buhari da Muslim da suke nuni da samuwar wuri ga Allah madaukaki, wadannan ruwayoyin suna nuna yana saukowa daga sama zuwa kasa a kowane dare. Wadannan hadisai dukkansu suna komawa zuwa ga ruwayar Abuhuraira da zamu ga suna kunshe da wasu bayanai kamar haka:
Allah yana sauka a kowane sulusin dare na karshe don tambayar mutane bukatunsu domin ya biya musu ita.
A wata ruwayar ya zo cewa daga karshe sai Ubangiji ya bude hannayensa ya ce: Waye zai ba wa Allah rance, (Muslim: j 2, Kitabu salatil musafirin; babut targib fiddu’a wazzikr, Hadisi: 758).
A ruwayar uwar muminai A’isha ya zo cewa: Ubangiji yana kusantowa kusa da bayinsa ne a ranar Arfa fiye da kowace rana! (Musulim: j 2, kitabul hajj; b fadhlul hajji wal umra wa yaumu arafa).
A cikin dukkan wadannan hadisai idan mun hada su zamu ga sun kunshi wasu abubuwa kamar haka:
1- Ba wa Allah jiki; 2-Bukatar Allah ga wuri; 3-Bukatuwarsa ga jiha; 4-Ba wa Allah iyaka.
Ruwayoyin sun zo da sura daban-daban wasu ma sun yi nuni da cewa yana saukowa ne bayan wani Bangare na dare ya wuce. Sai dai abin da duk yake cikinsu yana saBa wa abin da yake na yakinin hankali da koyarwar littafin Allah mai inganci, (Umdatul qari: j 7, b 14, sh 196 – 197).
GABOBIN ALLAH
A cikin Buhari da Muslim akwai ruwayoyin da suka zo suna nuna cewa Allah yana da gaBoBi kamar dai wani samamme da yake da jiki, kamar wani mutum da yake da Bangarori da gaBoBi kamar fuska, hannu, dan yatsa, da sauransu. Idan mun duba a fili zamu ga bahasosin da suka gabata sun yi nuni da wannan ta yadda zamu ga wasu sun yi nuni da samuwar gaBa ga Ubangiji madaukaki.
Fuskar Allah
Buhari da Muslim sun ruwaito hadisai da suke ba wa Allah madaukaki fuska da kama, wannan fuskar ta yi kama da fuskar mutum, a cikin hadisin da Abuhuraira ya karBo an siffanta Allah (s.w.t) da cewa yana da sura irin ta annabi Adam (a.s) da ya halitta mai tsawon zira’i sittin. Ruwayar tana nuna cewa a ranar lahira duk wanda zai shiga aljanna ma zai kasance da tsawon annabin Adam (a.s) ne, kuma tun lokacin annabin Adam (a.s) mutane suna rage tsawo ne har yau.
Ruwayar ba wa Allah fuska ta maimaitu a wata ruwayar da take hana wani zagin wani mutum saboda surarsa irin ta Allah ce, domin Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa sura da kama irin tasa. Haka nan ta maimaitu a cikin ruwayar wanda ya mari wani mutum sai aka hana shi marin fuska domin Allah ya halicci mutum da kama irin tasa ne, (Buhari: j 8, h 5873. Muslim: j 8, h 2841. Muslim: j 8, h 2641) (Buhari: j 8, h 5873. Muslim: j 8, h 2841. Muslim: j 8, h 2641).
A cikin wadannan ruwayoyin zamu ga akwai ba wa Allah sifa, sura, kama, da fuska irin ta mutum wacce take lizimta siffanta shi da jiki.
Sannan abin mamaki gare su da fitar da hukunci daga wannan kamannin da yake ganin tun da fuskar mutum ta yi kama da ta Allah madaukaki to bai kamata ba a mari mutum ke nan.
Haka nan tsawon Adam (a.s) zira’i sittin ne, kuma fadinsa zira’i bakwai ne, kuma tun da yana kama da Allah to zai kasance ke nan tsawo da fadin Allah madaukaki ya zama sananne ke nan.
Idan da mutum na farko yana da tsawo da fadi haka don me ya sa duk mutanen da ake hakowa masu tsawon tarihi tun lokacin annabi Adam (a.s) aka same su da tsawo irin na wannan al’ummar babu wani bambanci, ko bambanci kadan.
Idan da annabi Adam (a.s) ya kasance da tsawon zira’i sittin ne, to abin da tsawon hannunsa ya kamata ya kasance shi ne zira’i sha bakwai da kashi daya cikin bakwai na tsayi ba zira’i bakwai ba domin ya yi daidai da tsarin halittar tsayin mutum. Idan ya kasance kamar yadda ruwayar ta kawo to zai kasance mutum mai muni matukar gaske alhalin Kur’ani mai daraja yana cewa: "Lallai mun halicci mutum cikin mafi kyawun kirar halitta”, (Tin: 4).
Idon Allah
Ruwayoyin da suka zo a Buhari da Muslim suna nuni da cewa Ubangiji madaukaki ba makaho ba ne kamar Dujal, domin shi Dujal idonsa na dama makaho ne da ya yi kama da kwayar inabi, (Buhari: j 4, h 3256 – 3257. J 5, h 4141. Muslim: j 8, h 2933. Buhari: j 9, h 6983).
A sakamakon wadannan ruwayoyin ne ‘yan Sunna suka tafi a kan cewa Ubangiji yana da idanuwa masu gani. Kuma kiyasin idon Allah da na Dujjal ba abin da yake nuni sai da hakan. Abu mai muni a cikin wannan ruwayar yadda take kawo Dujjal tana kamanta Allah da siffofin da suka saBa da nasa.
Kafadar Allah
Ya zo a cikin Buhari da Muslim da Ibn Majah cewa Ubangiji yana dora kafadarsa kan ta bawansa sai ya gaya masa cewa ka tuna zunubi kaza da kaza da ka yi a duniya, to ni na suturta maka su a duniya yau kuma ina gafarta maka su.
Wani mutum ya tambayi Abdullahi dan Umar kan wannan lamarin sai ya ce haka ne, na ji annabi yana fada, sai ya kawo wannan ruwayar, (Buhari: j 6 kitabut tafsir; aya 18, h 4407. J: 8, b 60, h 5721 – 5722. Muslim: j 8, h 2766 – 2768).
Hannun Allah
Hadisan Abuhuraira da Abdullah dan Umar da suka zo a Buhari da Muslim da wasu Sunan sun ba wa Allah madaukaki hannu suna nuni da cewa hannunsa na dama a cike yake, amma hannunsa na hago yana dauke da ma’auni ne da yake rage rabon wani da shi ya kara kason wani da shi.
Daya ruwayar kuwa tana nuni da cewa zai dauki sammai da kassai da hannunsa sai ya rika jimke hannunsa yana budewa yana cewa ina masu jiji-dakai! ina masu takama! Har manzon Allah ya kasance yana yin dama da hagu a kan mimbari. Da sauran ruwayoyi da suka zo da wannan lamarin suna masu siffanta Allah madaukaki da hannaye, (Buhari: j 9, b 22, h 6983. B 19, h 6976, h 4407. Ibn Majah: j 1, b 13, fima an karat aljahmiyya. D.s.s).
Yatsun Allah
A cikin ruwayar Abdullahi dan Umar game da zuwan malaman yahudawa gun annabi (s.a.w) sai suka ce Allah zai dauki sama, kasa, ruwa, shuka, kasa, kowanne a kan wani dan yatsansa kamar yadda suka samu a littafin Attaura. Ya ce sai manzon Allah ya yi murmushi har hakoransa suka bayyana yana karfafa hakan, sai kuma aya ta sauka tana gaskata hakan, (Buhari: j 6, b 297, h 4533 – 4534. Da wasu babobi masu yawa. Muslim: j 8, kitabu sifatul munafiqin, b sifatul qiyama wal janna wannar, h 2786).
Tabbatar wa Allah ‘yan yatsu kamar sauran gaBoBi lamari ne mai ruwayoyi masu yawa a cikin Buhari da Muslim da kuma sahihai da sunan na litattafan ‘yan Sunna. Wannan maganar tana lizimta siffanta Allah da iyaka da gaBoBi da jiki, lamarin da zai mayar da shi mabukaci mai iyaka.
Kwankwanson Allah
Wasu ruwayoyin Buhari da Muslim suna tabbatar wa Allah kwankwaso. Ruwayar Buhari da Abuhuraira ya karBo tana cewa lokacin da Allah ya yi halittu sai zumunci ya tashi ya cakumi kwankwanson Allah, sai Ubangiji ya ce masa yi sannu dai. Sai zumunci ya ce: Me ye matsayin wanda ya yanke zumunci. Sai ya ce masa: Ba ka yarda da in sadar da wanda ya sadar da kai ba, in kuma yanke wanda ya yanke ba. Sai ya ce: Na yarda. Sai ya ce: Haka yake, (Buhari: j 6, kitabut tafsir: b 1, h 4552).
Kwaurin Allah
Ruwayoyin ganin Allah sun gabata a bahasin ganin Allah da suka zo a littafin Buhari da suke nuni da cewa muminai zasu ga kwaurin Allah ranar kiyama kuma da shi ne zasu gane ubangijinsu. Wasu ruwayoyin sun yi nuni da cewa da Ubangiji ya yaye kwaurinsa sai kowa ya fadi ya yi masa sujada, babu wanda zai kasa sai mai riya da son jin yabon kansa, (Buhari: tafsir, b 24, h 7001, h 4635).
Abin da ya fi komai mamaki a hadisan siffanta Allah madaukaki da kwauri shi ne cewar idan muminai suka zo ba sa gane shi, har ma suna yin musu da shi kan cewa shi ne Allah ubangijin bayi, daga nan ne sai ya bude kwaurinsa da ya rufe da bargon takama da mayafin ji da kai, sai su gane shi ne ubangijinsu sannan sai su yi sujada.
Mummunar fassarar da aka yi wa ayar nan mai cewa "…ranar da za a yaye kwauri…” ta sanya jingina wa Allah wannan gaBa. Maimakon mayar da wannan ma’anar ga harshen larabci da take nufin marhalar tsananin tsoro da firgici da fuskantar hadari. Larabawa suna fadin haka da nufin an kai marhalar da mutum zai dage zaninsa don ya gudu domin babu wata mafita da ta rage sai hakan. Don haka duk wata marhala da ta kai tsananin wahala to suna kiran ta da "… yaye kwauri…” domin idan ba a yaye shi ba to gudu ba zai yiwu ba.
Kamar dai fadin nan na larabawa cewa "قامت الحرب على ساق” wanda yake nuni da yaki ya kai matukar wahala da tsanani. Don haka yaye kwauri yana nuni da abin da muka kawo. Idan mun duba zamu ga kowane yare yana da kinayar da yake amfani da ita wurin isar da sakon sa.
Da Kur’ani ya sauka da yaren Hausa da bahaushe zai ji an ce masa "… ranar da aski zai zo gaban goshi…” ne. Kuma da masu wannan kanzagin da wuce gona da iri sun yi kokarin siffanta Allah da cewa yana da gashi mai yawa a kansa, kuma a wannan ranar ne za a kusa gama askin don haka aska ta zo gaban goshi ke nan. Ta yiwu ka samu wasu masu shisshigi su kirkiro hadisai da suke nuni da cewa ta keyarsa aka fara askin ko ta gefan kansa.
Don haka wannan karkata da kauce wa hanya madaidaiciya game da siffofin Allah madaukaki ta fada wa al’umma sakamakon nisantar su da wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ta biyayya ga littafin Allah da alayensa a bayansa.
Kafar Allah
A game da hadisin da ya zo yana bayani kan neman da jahannama take yi na a kara mata mazauna sai ruwayar take cewa ba zata cika ba har sai Allah ya sanya kafarsa cikinta sai ta ce ya isa!. Ruwayar ta zo da cewa jahannama ba zata koshi ba, don haka za a yi ta zubawa har sai da Allah ya sanya kafarsa a ciki sai ta cika ta yi magana cewar ta cika hakan nan.
Ruwayoyin da suka zo da wannan lamarin a cikin Buhari sun yi amfani da lafazin kafa, wasu kuwa sun zo da lafazin tafi ne. Kuma ko dai me ye ya kasance; kafa ce ko tafi, ba wa Allah madaukaki jiki da gaBoBi da wannan ruwayar ta yi shi ne babbar matsala, (Buhari: j 6, b 33, h 4567 – 4568).
Ba mamaki wasu mutanen su ce don me ya sa ba za mu yi tawilin wadannan hadisan ba don a samu wata mafita da wata ma’ana mai kyau da zasu bayar ta yadda zamu fassara su da bayanin da zai kore samuwar jiki ga Allah madaukaki?. Kamar mu fassara ma’anar yaye kwaurin Allah da wahala da tsanani da hadari da ake fuskanta, ko mu fassara ma’anar ganin sa da sauraron ni’ima kamar yadda gani yake da ma’anar sauraron wata ni’ima a harsuna masu yawa. Misali da harshen Hausa idan wani ya zo ganin wani babba a ofishinsa, to gani a nan yana nufin zai nemi wani abu da yake son samu wurinsa, ba kawai ya kalle shi da ido ba!.
Sai dai hakan ba zai yiwu ba a irin wadannan hadisan domin ‘yan Sunna ba su ruwaito wasu hadisai da za a fassara wadannan hadisai da su ba, don haka zamu lura da wasu abubuwan kamar haka:
1-Da an samu wasu wurare da suka ruwaito hadisai da suke nuna ba za a ga Allah da idanuwa ba misali, to a nan sai mu fassara hadisin ganin Allah da ido da waccan ma’anar, domin sai mu gane cewa ke nan wancan ganin ba na ido ba ne, yana nufin na sauraron ni’ima ne. Amma ba mu samu hadisai masu kore ganin Allah ba daga ‘yan Sunna, don haka babu wata hanyar tawili ke nan.
2-Ruwayoyin da suka ruwaito masu ba wa Allah jiki da Bangarori zamu ga suna karfafa ma’anar zahiri karara ba tare da sun bar wata hanyar da za a iya yin wani tawili ba. Misalin mutumin da aka hana marin sa saboda Ubangiji ya yi kama da shi, a nan da wane irin tawili za a fassara wannan ma’anar ta yadda zata fita daga ma’anar zahiri. Haka nan ganin Allah kamar yadda ake ganin wata daren sha biyar, ita ma yaya za a iya bayanin ta da ma’anar da zata saBa wa zahirin kalmar da take nufi?.
3-Idan mun duba wadannan ruwayoyin zamu ga ba tun yau suke ba, domin sun bayyana ne lokacin Buhari (w 256) zuwa Nisa’i (w 279) kuma su ne dai har yau muke karantawa a littattafan Sunna, don haka ba sababbi ba ne. Kuma a lokacin Imam Bakir, Imam Sadik, da Imam Ridha an kawo wadannan ruwayoyin an karanta a gabansu amma ba su nuna ingancinsu ba, balle kuma su yi tawilinsu, sai suka yi inkarin su kai tsaye, suka yi nuni da karya ce aka jingina wa manzon Allah (s.a.w). Da sun inganta daga annabin rahama (s.a.w) kuma suna iya karBar tawili da mun samu hakan daga jawabinsu.
4-Idan ma muka yi tawilinsu to zamu ga su malaman ‘yan Sunna da suka ruwaito su sun hana duk wani tawili kansu, suna masu kore duk wani bayani da zai yi tawilinsu ko ya kawar da su daga ma’anarsu ta zahiri. Don haka babu wata ma’ana ga wanda shi bai yarda da ingancinsu daga annabin rahama ba kuma bai yarda da abin da suka kunsa ba ya shiga yin tawilinsu. Masu ruwaito su suna ganin duk wani inkarinsu ko yin tawilinsu to saBa wa addini ne, wasu ma suna ganin sa zindikanci ko kafirci da fita daga mazhaba.

Hafiz Muhammad Sa’id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com).

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: