bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:41:41
Wannan sura da aka sani da suratul fil ko mu ce surar giwa da hausa ta sauka ne lokacin da sarkin Yemen Abrahata, wato gwamnan daular Habasha
Lambar Labari: 316
سورة الفيل
SURATUL FIL (SURA TA 105 )
DALILIN SAUKA
Wannan sura da aka sani da suratul fil ko mu ce surar giwa da hausa ta sauka ne lokacin da sarkin Yemen Abrahata, wato gwamnan daular Habasha wacce a sannan itace daula ta uku mafi qarfi a duniya, Daulace wacce tun daga Ethiopia a yanzu ta tsallake red sea (ruwan maliya) har zuwa Yemen, a wannan lokaci ne wakilin daular Habasha da ke Yemen ya so gina wata Coci ya umarci larabawa baki xayan su da su dinga zuwa taro wannan coci duk shekara maimakon Ka'aba sabida ya rusa addinin masu bautar gumaka, tunda a sannan ka'aba na cike da gumaka a wannan lokacin sabida canja addnin Annabi Ibrahim (AS) sai yan tsiraru, yayin da shi mai bautar Allah ne mabiyin addinin sama, yayin da ya gina wannan coci sai wani balarabe ya yi mata kashi, ya ji haushi ya ga cewa bari ya gyara musu zama da rushe ka'aba. Gwamnan Habasha da ke Yemen Abrahata ya yi tanadi mai karfi da shirin gaske inda ya tanadi giwaye, a wannan lokacin Sayyadi Abdul Muxxalib ne babba a garin Makka lkacin da Abrahata ya nufo makka don ya kai mata hari an haifi Manzo Allah (SAW) da kwanaki 50, a sannan Sayyadi Abdul Muxxalib ya yi tawassuli da Manzo (SAW) kan Allah ya tarwatsa musu qarfin da Abrahata ya tunkaro su da shi domin ba ta yadda za su iya cin masa sabida mugun tanadin da ya yi da kuma qarfin da yake da sh, sabda Abdul Muxxalib wasiyyi ne daga cikin wasiyyan isma'il, na daga cikin waxanda Allah kewa ilhama, sabida haka ya san cewa wannan jariri (SAW) shi zai zama Annabin qarshen zamani, yayin da su ka zo Makka sais u ka tura babbar giwar su ta shiga don rusa Ka'aba sai ta kasa shiga ta dawo, sai sai Allah ya yi musu ruwan duwatsu daga tsuntsayen da su ka fito daga yankin ruwan Jidda, duk tsutsuwar da ta yi ruwan dutsen sai ta koma, wani abun mamaki shine: kowanne tsuntsu na xauke da duwatsu uku, xaya a bankn sa, xaya a qafar sa ta hagu xaya a ta dama, yana zuwa sai ya jefa waxannan duwatu kan mutum xaya, idan dutsen ya sauka a kan mutum sai naman say a dinga yayyankewa wani kuma ya shiga ta kan say a fita ta duburar sa ko ta bayan sa, ba wanda ya kai Yemen sai Abrahata da mutanen say an kaxan, sannan shi ma yam utu a Yemen inda naman jikin say a dinga gutsurewa yana yayyankewa, wannan abun mamaki da yawa ya ke, sabida aikin da duwatsun ke yi ba yadda al'ada ta saba gani dutse yayi bane, bayan hallakar da su sai Allah ya saukar da wannan sura yana cewa:
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَابِ الْفِيلِ (1)
Baka ga yadda ubangijin ka ya yi da mutanen giwa ba.
أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِي تَضْلِيلٍ (2)
Shin (Allah) bai sanya makircin su cikin tavewa ba.
وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْرًا أَبَابِيلَ (3)
Ya aiko mus tsuntsaye gungu – gungu a kan su ba.
تَرْمِيهِمْ بِحِجَارَةٍ مِنْ سِجِّيلٍ (4)
Tsuntsayen na jifan su da duwatsu na yumvu.
فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَأْكُولٍ (5)
Ya sanya su kamar karmamin (wasu na cewa kamar vauren) da  aka radaddaga.

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: