bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:48:43
Allah mai hikima ne don haka dole ne hikimarsa ta bayyana a cikin ayyukansa, wato dole ne ayyukansa su tsarkaka daga duk wani rashin hadafi da manufa
Lambar Labari: 318
Halittar Mutum da duniya baki daya wata hikima ce ta Allah wanda yake masani kamar yadda duk wani aiki na shi mai hikima yana tattare da wata manufa tasa, wanda wannan manufa kuma daga karshe tana komawa ne ga kan shi abin halitta, ba wai zuwa ga mahalicci ba kamar yadda muka sani cewa shi mawadaci ne ba ya bukatar komai wato amfanin halittar yana komawa ne zuwa ga bayinsa. Gaskiyar wannan al’amari kuwa yana iya bayyana karkashin wadannan abubuwa guda biyu masu zuwa:
1- Allah mawadaci ne marar iyaka saboda haka ba shi da wata bukata zuwa ga komai.
2- Allah mai hikima ne don haka dole ne hikimarsa ta bayyana a cikin ayyukansa, wato dole ne ayyukansa su tsarkaka daga duk wani rashin hadafi da manufa.
Tare da kula da wadannan asali guda biyu da muka ambata a sama zamu isa zuwa ga sakamakon da yake nuna mana cewa Allah madaukaki bai halicci mutum da duniya ba sai tare da manufa ba, Allah mdaukaki ya halicci mutum da duniya baki daya domin wata manufa da amfani wanda kuma wannan amfani yana komawa ne ga su abin halittarsa. A kan wadannan ka’idoji ne guda biyu Allah yake fada a cikin Kur’ani mai girma cewa:
"Shin mutane suna tsammanin mun yi halitta ne haka nan babu wata manufa, sannan kuma ba zaku koma zuwa garemu ba” (Muminin:115).
A nan wannan tambayar zata zo ga zukata cewa to shin menene manufar halittar mutum? A wajen amsar wannan tambayar a takaice muna iya cewa: Sanin Allah da siffofinsa kyawawa, da kuma siffatuwar ruhin mutum da wadannan siffofin wadanda su ne ake cewa kyawawan dabi’u wadanda suke kunshe a cikin ruhin ‘yan Adam daga nan muna iya fahimtar manufar halittar shi mutum.
Domin kuwa sanin Allah yana tattare da wani nau’i ne na samun alaka da wata cibiya ta kamalar mutum. Sannan siffatuwar mutum da wadannan siffofi masu kyau wani nau’i ne na bayyanar ‘yan adamtaka na mutum, kuma wata alama ce da take nuna cewa ya isa zuwa ga kololuwar kamalar da yake iya samu.
Mutum yana da wasu makamai da zai iya amfani da su domin samun kammala, wadannan makamai kuwa su ne kamar haka:
A: Tarbiyar Kyawawan Dabi’u
Allah madaukaki ya halicci mutum kuma ya sanya masa son Allah da siffantuwa da siffofin kammala da kyamar siffofin da ba su da kyawu, wannan abin da mutum yake ji kodayaushe yana sanya masa wata natsuwar ruhi da samun alaka da Ubangiji a kowane lokaci, sannan ilimin yau da kullum wadanda suke karkata zuwa ga addini wadanda kodayaushe suna kara sanya wa mutum komawa zuwa ga duniyar gaibu da kwadayi zuwa ga kyawawan siffofi wadan su ne ake cewa kyawawan dabi’u, duk yana nuni ne ga wannan al’amari. A hakikanin gaskiya wannan abin da mutum yake ji a cikin ruhinsa na karkata zuwa ga kyakkawa wani jari ne ga shi mutum wanda sakamakon tarbiyarsa, sai mutum ya kara samun kammala, sannan kuma idan mutum ya rasa wannan sai mutum ya ja baya ya kuma yi nisa da samun kamala.
B: Hankali
Hankali da tunani fitila ce ga mutum wacce take haska masa domin isa zuwa ga kamala. Sakamakon amfani da wannan haskakawa ta hankali mutum zai iya gane hanyar isa zuwa ga kamala, sannan kuma ya kama hanya domin isa zuwa ga kamalar.
C: Annabawa Da Manzannin Da Allah (S.W) Ya Aiko
Annabawa da manzannin Allah sun kasance sun zo da duk abubuwan da zasu iya kai mutum zuwa ga kammala da cin nasara, suma matsayin wani jari ne na uku wanda mutum zai iya amfani da shi domin ya samu cin nasara da kammala, sannan wani bangare na koyarwar annabawa shi ne tarbiyantar wannan halittar da mutum yake da ita ta son kyawawan dabi’u da kusantuwa zuwa ga Allah. Kai sun kasance kamar kwararen mai binciken kasa da yake amfani da na’urori domin fito da abin da yake so daga cikin kasa. Wadannan abubuwa da Allah ya halitta wa mutum sakamakon koyarwar annabawa ne zai bayyana.
Imam Ali (a.s) yana bayyanar da wannan hakika inda yake cewa: "Allah madaukaki ya aiko da annabawa domin su bukaci mutane a kan su cika alkawarin da suka dauko daga Allah, sannan su tuna ni’imomin da suka manta da su, sannan su farkar da tunanin da ya faku”. (Nahjul balaga huduba ta farko)
Wannan alkawura kuwa su ne wadannan halitta da Allah ya yi wa mutum na karkata zuwa ga Allah da kyawawan dabi’u. Don haka halittar mutum tana tattare da wannan nau’i na halitta wacce take wani alkawari ne da Allah ya dauka da mutane.
A cikin wadannan abubuwa kuwa da Allah ya halittacikin zatin mutum akwai kadaita bautar Allah madaukaki kuma yana daga cikin muhimmansu. Gaskiyar al’amari ma wannan shi ne sakon dukkan manzanni da annabawa domin kuwa muna iya takaita dukkan ayyukansu a kan kira zuwa ga kadaita Allah (Tauhidi) kamar yadda yake cewa:
"Hakika mun aika Manzo a cikin kowace al’umma a kan a bauta wa Allah shi kadai, sannan a guji biyayya ga dagutu (duk abin da ba Allah ba) (Nahl:36).  Kula da ma’anar wannan aya zamu iya gane muhimmancin tauhidi ko kadaita Allah da kore duk wani wanda ba Allah ba a cikin bauta, shi ne kuma muhimmin sakon da Allah ya aiko manzanninsa da shi zuwa ga al’ummarsu kuma zamu ma iya takaita dukkan ayyukansu a cikinsa. Sannan kuma dukkan addinan Ibrahimiyya kira ga tauhidi shi ne a sama wajen da’awarsu.
Duk da cewa a cikin tsawon tarihi an yi kokari domin karkatar da wannan asali wato tauhidi ta yadda har ya zamana ana bautar mutum kamar yadda mutanen annabi Isa (a.s) suka sanya matsayin abin bauta a garesu, Amma masu tsarkin zuciya daga mabiyan dukkanin addinan da Allah ya aiko ba su manta da wannan asali ba na tauhidi da kadaita Allah a wajen bauta, sun dauke shi wani abu wanda yake babu kokwanto a cikinsa. A kan haka ne ma Allah yake ce wa cikamakon manzanninsa (s.a.w) wajen tattaunawarsa da kiristoci da mabiya wasu addinai cewa ya kira su zuwa ga kadaita Allah kamar haka: "Ka ce ya ku ma’abuta littafi ku zo zuwa ga kalmar da ta daidaita tsakaninmu cewa kada mu bauta wa kowa sai Allah sannan kada mu hada shi da kowa, sannan kada mu riki wasu daga cikimmu a matsayin abin bauta sabanin Allah, idan kuwa suka juya sai ku ce musu to ku sheda mu musulmi ne” (Aali Imran:64).
Matakai Hudu Na Tauhidi
Tauhidi shi kansa yana da matakai daban-daban, kamar tauhidi a cikin bauta wanda dukkan annabawa sun hadu a wajen kira zuwa ga hakan wanda kuma yake kuma yana daya daga cikin rassan tauhidi na musamman. Sannan a takaice zamu yi bayani a kan sauran sassan tauhidi kamar haka:
A-Kadaita Allah a cikin zatinsa: wato yin imani da cewa Allah shi kadai yake kuma ba wasu abubuwa suka hadu suka yi shi ba (Tauhidi Ahdi da wahidi).
B-Kadaita Allah a cikin yin halitta: Yin imani da cewa babu wani mai halitta sai Allah madaukaki kuma ba ya bukatar taimakon kowa wajen yin hakan.
C-Kadaita Allah a wajen tafiyar da al’amura: Halitta da tafiyar da duniya duk yana hannun Allah, domin kuwa shi ne ya halitta mutum da duniya baki daya, don haka shi ne yake da hakkin tafiyar da ita. Wadansu da suke da hannun wajen tafiyar da duniya dukkansu suna yin hakan ne da izini da umurninsa.
D-Kadaita Allah A Cikin Bauta: Wato yin Imani da cewa babu abin da ya cancanta a bauta wa sai Allah, sannan duk wanda ba shi ba bawansa ne kuma mai rauni ne, Saboda haka dole ne kowa da komai su mika wuya zuwa ga Allah.
A dukkan cikin matakai na kadaita Allah, mataki na karshe ne a nan zamu yi magana a kansa domin shi ne maudu’in bahsinmu, saboda muhimmancin na musamman yake da shi.
Kamar yadda muka ce kadaita Allah a cikin bauta shi ne abin da zamu yi magana a kansa, ba wai yana nufin cewa akwai shakku a cikinsa ba ne ta yadda zamu yi kokari domin gusar da wannan shakku. Domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a baya wannan asali wani karbabben abu ne ga dukkan addinai da suka zo daga Allah kuma sun hadu a kan wannan take suna masu cewa "Kai kwai muke bauta”.
Kai ba za a iya kiran mutum musulmi ba sai idan ya amince da wannan asali na kadaita Allah a cikin bauta, domin kuwa kin amincewa da wannan yana daidai da kin amincewa da musulunci baki daya.
Sannan idan muka manta da amincewar dukkan musulmi a kan wannan asali na kadaita Allah a cikin bauta, duk da cewa dukkansu sun hadu a kan wannan asalin. Halarcin wasu abubuwa kamar neman ceto daga annabawa ko kuma yin taro domin girmama ranar haihuwarsu da makamantan wadannan idan muka sanya a matsayin abin da zamu yi Bahasi a kansu, domin kuwa wasu daga cikin musulmi suna ganin cewa wannan shirka ne a cikin bautar Allah saboda suna ganin cewa neman ceto daga wani annabi ko kuma girmama ranar haihuwarsa wani nau’ ne na bautarsa.
Saboda haka a nan dole ne mu tantance hakikanin wannan girmamawa da muke yi wa Manzo a ranar haihuwa ko kuma neman wani abu da ake yi daga manzannin, ta yadda zamu iya gane shin wannan bauta ce ta yadda zai iya zama shirka ko kuwa kawai girmamawa ce ba tare da an bauta masa ba, ta yadda zai iya zama halas kuma ma mustahabbi.
Wannan kuwa yana iya yiwuwa ta sakamakon bayyana hakikanin ibada a ilimince, ta yadda duk inda muka ga ibada zamu iya ganewa da kuma abin daba ibada ba ne. Sannan mu iya bambamce girmamawa da kuma ibada, Domin kuwa idan ba a bayyanar da hakikanin ibada ba, to ba za iya yin hukunci ba a cikin irin wadannan wurare.
Ma’anar Ibada
Bayyanar da ma’anar kowane abu dole ne ya kasance a takaice kuma ta yadda zai kunshi dukkan ma’anar abin ya kuma hana wani abu wanda ba shi ba shiga cikin ma’anar. wato ta yadda zai iya tattaro duk wani abu wanda yake cikinsa sannan yak ore duk wani abu wanda ba ya a cikinsa. Wato ta yadda za a iya bayar da wata ka’ida wacce zata iya sanyawa a gane abin da yake ibada da kuma abin da ba ibada ba ne. Saboda haka idan muka samu irin wannan ka’ida zata taimaka mu warware da yawa daga cikin matsalolin damuke fuskanta dangane da ibada da abin da ba ibada ba.
Muna iya fahimtar ma’anar ibada ta hanyoyi guda uku kamar haka:
A-Tahanyar komawa zuwa ga littafin luga kamus.
B-Ta komawa zuwa ga wuraren da a ka yi amfani da kalmar ibada.
C-Bambance hakikanin ibadar masu kadaita Allah da kuma masu bautar gumaka.
Fadakarwa a kan bin da muka fada a sama kuwa shi ne a cikin hanya ta farko ba zamu iya samun ka’ida ba wacce zata taimake mum u iya gane menene hakikanin ibada. Saboda haka hanya ta uku ce kawai zamu iya bi domin mu gane mene hakikanin ibada. Amma dai zamu yi magana a kan kowace daya daga cikin hanyoyin.


Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: