bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:50:31
Amma Kuyud abadi a cikin Kamus yana cewa Ibada ita ce biyayya kuma Ibn Faris yana karawa da cewa, ibada ita ce nuna tausasawa da kuma kaskantar da kai
Lambar Labari: 319
A-Komawa Zuwa Ga Littattafan Lugga (Kamus)
Daya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen gane ma’anar ibada ita ce yin amfani da Littattafan lugga wato kamus din kalmomi. Ibn Manzu a cikin littafinsa na lugga wato lisanul arab yana cewa: Ibada ita ce nuna kaskantar da kai da tawalu’u.
Amma Ragib a cikin mufradat ya yi bayani da cewa lafazin ibada yana nuni zuwa ga kaskantar da kai da girmamawa amma fiye da abin da aka ambata a baya, wato ibada nuna kaskantar da kai ne na karhse.
Amma Kuyud abadi a cikin Kamus yana cewa Ibada ita ce biyayya kuma Ibn Faris yana karawa da cewa, ibada ita ce nuna tausasawa da kuma kaskantar da kai (a duba lisanul arab da Mufridat Na Ragib da Kamus Lugga da Makayisu Kalmar Abd).  
Wannan ma’anoni ba zasu iya bayyanar da hakikanin ma’anar ibada ba, domin kuwa bayyanar da kaskantar da kai ko kuwa marar iyaka ne, ba ya zama ibada, ta yadda idan mutum ya yi hakan ga wanin Allah ya yi shirka. Domin kuwa nuna kaskantar da kai da girmamawa ga iyaye wani abu ne wanda yake mai kyau kuma wani umarni ne ma da shari’a ta yi a kansa, amma ba yana nufin ana bauta musu ba. Kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: "Ka kaskantar da kafadunka zuwa gare su domin tausayi da girmamawa” (Isarai:24).  Sannan Allah madaukaki a cikin Kur’ani mai girma yana umurtar Mala’iku da su yi wa Adam (a.s) sujjada, sannan Annabi Yakub da ‘ya’yansa sun yi wa Annabi Yusuf sujjada (Bakara:100).
Saboda haka idan muka takaita kalmar ibada da ma’anar girmamawa da kaskantar da kai to muna iya cewa mala’iku sun bauta wa Adam haka nan Annabi Yakub da ‘ya’yansa sun bauta wa Yufus (a.s) (muna neman tsari a kan hakan) wato sun bauta wa wanin Allah kuma wannan ya mai da su sun yi shirka da Allah, sannan kuma Allah ya yi umarni da a bauta wa waninsa…
Wannan kuwa a fili yake babu wani mai tauhidi da yake iya fadar wannan magana. Saboda haka daga nan zamu iya gane cewa bayyanar da ma’anar ibada da aka yi a sama da cewa girmmawa da kaskantar da kai, ya shigo da abin da yake ba ibada ba ne, don haka ba ya bayyanar da hakikanin ma'anar ibada.
Mai yiwuwa a yi tunanin cewa ai Adam yana matsayin kibla ne amma sujjada an yi wa Allah ne madaukaki, amma wannan tunanin ya sabawa zahirin ayar Kur’ani mai girma. Domin kuwa idan haka ne babu ma’anar bijirewar da shaidan ya yi inda Allah yake cewa: "Zan bauta wa wanda ka halitta da yumbu sujjada?” (Isra:61).
Amma abin da muka fada ba yana nuna rashin girma aikin da marubuta Littattafan lugga ba ne, domin kuwa manufar su shi ne, bayyanar da ma’anar kalma a takaice, ba wai bayyanar da ma’anar kalma ba a ilimince. Yanzu kuwa zamu ci gaba da bayani a kan hanya ta biyu:
B-Bincike A Kan Wuraren Da Aka Yi Amfani Da Kalmar Ibada
Bincike kuwa a kan wuraren da aka yi amfani kalmomin ibada shi ma ba zai iya bayyanar mana da hakikanin ma’anar ibada ba, wato ba zai iya ba mu wata ka’ida ba ta yadda zamu bambance abin da yake ibada da wanda ba shi ne ba. Domin kuwa sakamakon takaitawar da ake yi wajen amfani da kalmomin a cikin adabin larabci ko kuma aron kalma da ake yi, tabbas ba zai bayyanar da ma’anar ibada ba ta yadda zai iya zama shirka idan a ka yi shi ga wanin Allah. Misali a kan ce wa mutumin da yake da cin abinci da yawa ko kuma mai son makami da suna bawan ciki ko mai bautar makami. Amma kowa ya sani cewa a wadannan ma’anoni wadanda ake amfani da su wajen mai cin abinci da yawa ko mai son makami ba suna nufin hakikanin ibadar da muke nufi ba a nan. Amma sakamkon wadannan mutane duk sun mayar da gurinsu wajen wadannan abubuwa shi ne ya janyo mutane suke cewa suna bautar wadannan abubuwa da aka ambata a sama. Haka nan ma Kur’ani mai girma ya yi amfani da wadannan kalmomi a wurin da ba suna nufin ma’ana ta hakika ba ne, inda yake cewa:
"Ya 'yan Adam yanzu bai dora alkawari a kanku ba cewa kada ku bauta wa Shaidan, domin kuwa shi makiyi ne a gareku?” (Yasin: 60)
Mutane da suka nutse wajen bin sha’awace-sha’awacen duniya da fushi suna masu bin shaidan ne, amma yin amfani da kalmar ibada a nan wani nau’i ne na aron kalma da yin amfani da kalma a wajen da ba hakikanin ma’anarta ba ne. A nan an yi haka ne ta yadda za a gargadi masu yin wadannan ayyuka ne kawai. Amma babu wani lokaci da za a iya kiran mai karya ko mai bin sha’awarsa da mai bautar shaidan, ta yadda zai iya zama daya da mushirikai.
Saboda haka bin wadannan hanyoyin biyu duk da cewa ba za a ce ba shi da wani amfani ba, amma ba zai isar da mu ba zuwa ga abin da muke nema na bayyanar da hakikanin ibada. Saboda haka dole ne mu bi hanya ta uku domin mu samu abin da muke nema.
 
C-Bincike A Kan Hakikanin Siffofin Ibada
A cikin hakikanin Ibadar da masu kadaita Allah ko masu bautar gumaka suke yi muna iya haduwa da wasu siffofi na ibada guda biyu, kamar yadda muna ganin duka wadannan guda biyu suna yin bauta ne. Wadannan alamomi kuwa sun kasu gida biyu wato na zahiri da na boye, wadannan alamomi guda biyu kuwa, sun kasance kamar oksijin da haidurojin ne a wajen ruwa, wato abin da suka hadu suka ba da hakikanin abin da ke ruwa, suma wadannan alamomi na ciki da na waje haka suke a wajen ibada, domin kuwa su ne suke bayyanar da hakikanin ibada da abin da ba ibada ba.
Alama ta farko kuwa wacce a cikin kowace ibada muna ganin wannan a zahiri shi ne, kaskantar da kai da girmamawa wanda ake bayyanar da shi da gabobi da harshe. Amma a nan ibada da girmamawa duk abu guda ne. Saboda haka dole mu tafi domin gano alama ta biyu wacce take bambace hakikanin ibda da abin yake kama da ita ta yadda zamu iya isa hadafinmu na asali.
Wannan alama ta biyu kuma alama ta ciki ita ce, wacce take sanya mai ibada ya kaskantar da kansa a gaban wanda ya halitta shi da nufin yi masa bauta ta yadda zai kawar da duk wani abu na jin kansa kawai yana kallon mahaliccinsa ne, ta yadda ta hanyar harshensa da duk gabobinsa yake bayyanar da wannan kaskantarwa.
Amma sanin hakikanin wannan al’amari yana samuwa ta hanyar niyyar da ta sanya a ka aiwatar da wannan na’u’i na girmamawa da kaskantar da kai wanda yake bayyanar da mushirikai da kuma masu kadaita Allah madaukaki. saboda haka idan muka gano wadannan dalilai da suka sanya aka yi wannan aiki to zai zame mana sauki mu iya gane ibada da kuma abin da yake ba ibada ba.
Dalilan masu kadaita Allah wajen yin wannan ayyuka na kaskantar da kai, yana da alaka gwargwadon saninsu da Allah abin bauta da kuma imaninsu da tsarkake shi. Wadannan niyyoyi nasu kuwa na cikin zuciya muna iya kasa su zuwa gida biyu kamar haka:
Manufar Arifai A Kan Ibadar Ubangiji
Manufar arifai da sufaye a kan bautar Allah shi ne tsananin nuna soyayyarsu ga Allah mahalicci. Wato sanin hakikanin kyawon Ubangiji shi ne yake fizgo dukkan samuwar zuwa ga abin kaunarsu ba tare da la’akari da ladar da zasu samu wajen bautar ba ko ba tare da tsoron wata azaba ba suke bautarsa. Wato; so da kaunar Mahalicci da kyawawan siffofinsa ne suke fizgo su zuwa ga kaskantar da kai da girmama shi da bautarsa.
Ya zo a cikin Hadisai inda ake kiran wannan nau’i na ibada da ibadar masu ‘yanci wacce take ta tsarkaka daga duk wani nau’in bukatar zuci. Kamar inda yazo cewa: "Wasu mutane sun bauta wa Allah kawai don soyuwa zuwa gareshi, wannan ita ce "Ibadar ‘yantattu” (Wasailush shi’aJuzu’I na 1shafi na 55 babi na 9a cikin babukan mukaddima a kan ibada hadisi na 1).
Wannan manufa ta ibada kamar yadda aka yi bayani a sama ba manufa ba ce wacce ta hada kowane mutum a kanta, ba dukkan masu kadaita Allah ake samunta ba. Kawai ana samunta ne ga wasu mutane na musamman wadanda suka isa zuwa ga wani mataki na kamalar dan Adam, wato ba su da wata manufakan yin ibada sai kawai son abin bauta da siffofinsa kyawawa. Saboda haka a nan dole ne mu yi bayani a kan alamomin ibada da suka hade kowane mutum.


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: