bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:41:49
Idan ya hadu da dayan shakku ingantattu wajibi ne ya bi a sannu kamar yadda muka ce
Lambar Labari: 325
Sauran Shakkun Da Salla Take Inganta Da Su
 108> (m.1209) Idan mai salla ya ci karo da sauran shakkokin da salla take inganta da su, bai halatta ba a gare shi ya yanke sallar, da zai yanke ta, ya yi sabo. Idan kuma ya sake wata sabuwar salla kafin yin wani aiki da yake bata salla, kamar juya wa daga alkibla, ko makamancinsa, to sallarsa ta biyun ma ta baci. Idan kuwa sake ta ya kasance bayan yin wani aiki da yake bata salla, to sallarsa ta biyu ta yi.
 109> (m.1210) Idan da dayan shakkun da suke wajabta sallar ihtiyadi ya hau kansa, sai ya kammala ta kuma ya sake ta (wato ya yi wata sallar ta biyu maimakon sallar raka'ar ihtiyadi) kafin ya zo da sallar ihtiyadi, to ya yi sabo. Idan ya yi sallar ta biyun ne kafin ya zo da wani aiki da yake bata salla, sallarsa ta biyun ma ta baci, idan kuwa ta kasance bayan zuwa da aiki mai bata salla ne, sallarsa ta biyun ta inganta.
 110> (m.1211) Idan ya hadu da dayan shakku ingantattu wajibi ne ya bi a sannu kamar yadda muka ce, kuma kada ya shiga cikin wani aiki bayansa wannan kuwa saboda sanya ran gusar da shakkunsa, amma idan kokwantonsa bai gushe ba ta hanyar jinkirtawa to babu laifi ya shiga cikin aikin da yake binsa a sannu-sannu cikin tunani, idan kuwa ya yi kokwanto a cikin sujjada, ya halatta ya jinkirta sannu-sannu har zuwa bayanta.
 111> (m.1212) Idan zato ya same shi game da dayan bangarori biyu da farko, sannan zaton nasa ya koma shakku, to ya yi aiki da hukuncin mai shakku. Idan kuwa ya yi shakku da farko sai ya yi ginin aikin bisa hukuncin da yake kansa, sannan kokwantonsa ya canza zuwa zato game da dayan bangarori biyu (wato ko raka'a kaza ko kaza), sai ya yi gini bisa bangaren da yake zato ya cika sallarsa.
 112> (m.1213) Idan ya yi kokwanton cewa shin mai zato ne shi ko mai kokwanto sai ya yi aikin mai kokwanto.
 113> (m.1214) Idan bayan ya gama salla sai ya san cewa ya yi kokwanto a yayin da yake salla tsakanin raka'a ta biyu da ta uku bisa misali, sai ya yi gini a kan ta uku, sai dai bai san cewa shi mai zato ne bisa ukun, ko mai kokwanto ne tsakanin bangarorin guda biyu ba, to ya wajaba ya zo da sallar ihtiyadi.

Hukunce-hukuncen Sallar Ihtiyadi
 114> (m.1224) Wanda sallar ihtiyadi ta wajaba a gare shi, to wajibi ne da zarar ya kare salla, take ya yi niyyar sallar ihtiyadi. Sai ya yi kabbara ya karanta fatiha sannan ya yi ruku'u ya yi sujjada guda biyu ya yi sallama, idan kuma raka'a biyu ce sai ya kara raka'a daya a kai sannan ya yi tahiya ya yi sallama.
 115> (m.1225) Ba a karatun sura a cikin sallar ihtiyadi kuma ba a yin kunuti, kuma wajibi ne a boye karatu a cikin ta, kuma kada a bayyana niyya, amma bisimillah bisa ihtiyadi na wajibi a karanta ta a boye.
 116> (m.1226) Idan mutum ya tabbatar da ingancin sallar da ya yi kafin ya yi sallar ihtiyadi, to sallar ihtiyadin ba ta wajaba gare shi ba, idan kuwa ya tabbatar da haka ne alhali yana cikin sallar ihtiyadi, to ba wajibi ba ne ya cika ta.
 117> (m.1227) Idan da zai san tawayar sallarsa, kafin ya yi sallar ihtiyadi, idan bai aikata aikin da yake kore ta ba to wajibi ne ya zo da abin da ya tawaya sannan ya yi sujjadar rafkanwa, saboda sujjada ba a mahallin ta ba, amma da ya aikata mai bata salla kamar ba wa alkibla baya to wajibi ne ya sake sallar.
 118> (m.1228) Idan ya san cewa sallarsa ta tawaya da gwargwadon sallar ihtiyadi, kamar idan kokwantonsa ya kasance tsakanin raka’a ta uku da ta hudu, sannan ga shi ya riga ya yi sallar ihtiyadin, sai daga baya ta bayyana a gare she cewa raka'a uku ya yi, to sallarsa ta inganta.
 119> (m.1229) Idan ya san tawayar sallarsa ta kasance sama da sallar ihtiyadi bayan ya riga ya yi ta, kamar idan ya yi kokwanto tsakanin biyu da hudu, sai ya yi sallar ihtiyadi raka’o’i biyu, sannan ya gano cewa raka’a uku ya yi to wajibi ne ya sake sallarsa,
 120> (m.1230) Idan ya san tawayar sallarsa ta fi sallar ihtiyadin yawa, bayan ya riga ya yi ta kamar idan kokwantonsa ya kasance tsakanin uku da hudu sannan ya yi sallar ihtiyadi raka’a daya, daga baya sai ya gano cewa raka’o’i biyu ya yi, idan ya riga ya zo da wani aikin da yake kore salla bayan da ya yi sallar ihtiyadin, to wajibi ne ya sake sallar. Amma idan bai aikata abin da ke kore sallar ba, to wajibi ne ya zo da raka’o’in nan biyu sannan ya sake sallar.

Sallar Matafiyi
 121> (m.1281,ds) Ya wajaba ga matafiyi ya rage (kasarun) sallar azahar da la’asar da isha sai ya yi ta raka’o’i biyu maimakon hudu bisa sharudda guda bakwai.
1.    Kada tafiyarsa ta kasance kasa da farsakhi takwas na shari'a. farsakhi na shari’a shi ne kilo mita biyar da biyu bisa uku (2/3) a mafi karancin nisa. Amma wanda tafiyarsa da dawowarsa suka kasance farsakhi takwas idan har tafiyarsa ba ta zama kasa da farsakhi dudu ba to wajibi ne ya yi kasaru, amma idan tafiyar tasa ta kasance farsakhi uku dawowarsa kuma farsakhi biyar to wajibi ne ya cika sallarsa.
2.    Ya kasance ya yi kuduri ko ya yi aniyar farsakhi takwas tun daga fara tafiyar tasa. Da a ce ya yi nufin yin tafiya kasa da farsakhi takwas, yayin da ya isa wajen sai ya ga bari ya tafi wani wajen da idan aka hada da na farko zai zama farsakhi takwas to wajibi ne ya cika sallarsa.
3.    Kada ya wuce ta garinsa kafin ya isa farsakhi takwas, kuma ba zai tsaya a wani waje ya yi kwana goma ko sama da haka ba a yayin da yake kan hanya.
4.    Kada tafiyarsa ta kasance ta sabo, da a ce zai yi tafiya don aikata haram kamar sata a bisa misali, to wajibi ne ya cika sallarsa.
5.    Kada ya kasance daga cikin matafiya ma’abota sahara da kauyuka wadanda suke neman ruwa da ciyawa don ciyar da kansu da dabbobinsu, sannan su ciratu zuwa wani wajen ba tare da sun zauna a wani bagire (wuri) na musamman ba, irin wadannan za su cika sallarsu.
6.    Kada sana’arsu ta kasance tafiye-tafiye, kamar matuki da dan dako (mai haya da abin hawa) ko mai yawon karbar haraji gari-gari, da makiyayi da matukin jirgin ruwa, da makamancinsu, duk za su cika sallarsu.
7.    Ya isa zuwa iyakar haddin rangwane (haddu al-tarakkhus) ta yadda zai yi nesa daga garinsa ko mahallin da zai zauna kwana goma nisan da ba zai iya hango katangar garin ba, ko jin kiran sallarsa ba.
 122> (m.1338) Abin da ake nufi da gari shi ne mahallin da mutum ya zaba don rayuwa a cikinsa, daidai ne a nan  aka haife shi kuma nan ne mazaunin iyayensa ko kuwa ba nan ba ne..
 123> Salla a garin mutum da inda zai zauna kwana goma ko sama da haka tana kasancewa cikakkiya.
 124> (m.1351) Idan matafiyi ya yi nufin zama kwana goma a wani waje sannan ya canza niyyarsa kafin ya sallaci salla mai raka’o’i hudu ko kuma ya yi kokwanton wanzuwa a wurin, ya wajaba ya yi kasarun sallolinsa. Amma idan ya canza nufinsa bayan ya riga ya sallaci salla mai raka’o’i hudun, to wajibi ne ya ci gaba da cikawa mutukar yana wajen.
 135> (m.1363) Idan matafiyi ya yi nufin zama kasa da kwana goma a wani waje bayan haka sai ya yi nufin kara zama kasa da kwana goma, sai ya yi ta yin haka har ya cika talatin, wajibinsa a nan shi ne ya cika sallarsa daga rana ta talatin da daya.

Sallar Ramuwa
 126> (m.1379) Wanda sallar farilla ta kubuce masa a cikin lokacinta, wajibi ne ya rama ta, in banda abin da mace tabari a lokicin jinin al’ada ko na biki, wadannan bai wajaba a rama su ba.
 127> (m.1381> Bai hallata a yi sakaci da jinkirtar ramakon salla ba, sai dai ba wajibi ba ne a gaggauta rama ta.
 128> (m.1339) Ya wajaba a kan babban da namiji ya rama salloli da azumin da suka kubuce wa mahaifinsa bayan mutuwarsa, ko kuma ya yi jinga da wani a kan hakan, idan ya kasance bai bar ta ba saboda sabo kuma yana da ikon rama ta.
 129> (m.1542) Ya wajaba ga kowa ya gabatar da ayyukansa na wajibi na addini wadanda aka farlanta masa a lokacin rayuwarsa. Hakika shi abin tambaya ne a kan dukkan wani sakaci da sassauci ko kasala a kan wannan, amma bayan mutuwarsa, ya halatta a yi jinga don yi wa wanda ya mutu salla da ma sauran ibadojinsa da bai yi ba a lokacin rayuwarsa.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: