bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:51:32
Idan mutum na son aure ya kasance mai nishaxi da al'kahairi da jin daxi, ya zama ya fitar da shi daga cikin kaxaita, dole ne ya kasance an samu dacewar tunani xaya da manufa xaya
Lambar Labari: 328
1-    DAIDAITAR TSARANTAKA DA JUNA
Manzon Rahama (SAW) ya ce : "ku auri tsararrakin ku"
     A kan wannan ya shafi daidaita da juna, kafin aure ya kamata a lura da waxannan abubuwan kamar haka :
a-    SU KASANCE MUMINAI (MIJIN DA MATAR).
 shi imani shi kaxai ma ya isa daidaita koda an sava wajan arziki da asali (mumini tsaran mumini ne) kuma muminai sashin su tsarin sashi ne
 Imaman Ahlul bait (AS) suna auren kuyangun su, saboda su nutsar da mutane a kan cewa mumini daidai yake da mumina, fifiko na bisa yardarsu da tsarkaka

b-    DACEWAR TUNANI
Idan mutum na son aure ya kasance mai nishaxi da al'kahairi da jin daxi, ya zama ya fitar da shi daga cikin kaxaita, dole ne ya kasance an samu dacewar tunani xaya da manufa xaya.

c-    DAIDAITAR TATTALIN ARZIKI
Wannan al'amari ne da ya wajaba maza su dinga lura da su, domin auren wadda take daga masu qarancin arziki ba a cika samun daidaitar aure ba, kamar talakan namiji ya auri 'yar masu hali, babu wani hani saidai ta vangaren kyawawan xabi'u, abin qi ne domin zai mata dalilin suvucewar ni'ima da jin daxin da ta kasance a ciki ya sanya ta cikin fatara da rashi, an yi wasiyya ga namiji ya auri macen da take da madaidaicin arziqi qasa da shi.
Wannan na daga qasqan da kan namiji da xaukakakr matsayin sa, zai xaukaka da auren macen da basa daga masu matsayi,dukiya ko tana da qarancin su, saboda da matar zata rayu a qarqashin mijin, tana mai xaukaka da jin daxi da al'fahari da shi.
Aliyyu Bin Hussai (AS) ya auri wata mata  daga qabila da ba maxaukakiya ba, sai mutane suka zargeshi kan haka, suna ganin qasqanci ne a gareshi, sai Imam ya ce musu : "Aliyyu Bin Hussai ya qasqantar da kansa, Allah kuma zai xaukaka shi"

d-    DACEWAR GIRMAN JIKI DA SHEKARU
Girman jiki al'amari ne muhimmi wajan aure saboda wajibi ne ya zama akwai dacewa tsakanin namiji da matar da za a aura, ta yadda baza a samu matsala daga xaya ba, tafiya da qarfin jiki ga ma'aurata, wajibi ne a yi la'akari da shi ta yadda za a samu jin saxin rayuwar aure.
Bambanci da ake son a samu tsakanin namiji sa mace, shekara huxu ko shida ne, amman wanna baya nufin wajibi ne sai an samu haka ko qasa da haka ba, domin kamar yadda muka faxa  abaya cewa aure wajibi ne agina shi, a kan daidaita da dacewa tsakanin ama'aurata ta vangaren jikin su, tunanin su, da halaiyyar su.
Kamar : kyau, matsayi, dukiya da iko da sauran su.


2-    KULA, ISA DA IYA XAUKAR NAUYIN AURE
Haqiqa yin aure da kafa iyali na nufin karvar aiki da gudanar da shi da lura da iyali, ta wani vangaren kuma aiki ne na tarbiyyantarwa da koyarwa, saboda haka kowane kuskure ko jahilci wajan yin wannan aikin  zai iya kawo matsala da cutuwa, kamar yadda yake taqaitawa wajan bada wanna tarbiyyar da rashin qwarewa da al'amuran na sanadin iya lalata iyalin da za a kafa.
Abinda yake wajibi kuma muhimmin abinda ya kamata a kula da shi wajan zaven abokin aure shine, a san iyayen sa da isar sa wajan iya tarbiyyantarwa, saboda haka wajibi ne a lura da waxannan muhimman al'amuran suna isa da iyawar xaukin nauyin zama uba ko uwa ingantattu.


ABUBUWAN LURA WAJAN NAMIJI KAFIN MACE TA AURE SHI
Ya ke 'yan mata, shin kin yi tunani kan namiji da zaki aura kuwa?  Wanda kike so ya zama uban 'ya'yan ki a nan gaba wanda kike son kare rayuwar ki tare da shi, ba wai sheakara xaya ko biyu ba, a a duk tsayin rayuwar ki, an san rabuwa ta inganta a lokacin da ake gujewa cutarwa, qufar hana a buxe take duk da ba haka aka so ba tun farkon al'amari kuma mai yasa ba a yi tunani ba a kan abinda za a zo ana nadama? Mai yassa ba a sa hankali ba tun farkon lamarin?
Kamar yadda bai zama dole a bar aure ba saboda gudun matsalolin da za a fuskanta da abokin zama, domin ya zama dole a gina iyali ta kowane hali, sai dai ya zama dole mu yi taka tsantsan don kada mu jefa kan mu cikin halaka, ba tare da tunani ba.
Dangane da zaven abokin zama dole ne ki sa hankali, sai ki haxa da neman taimakon mahaifin ki, ki shigar da su cikin al'amarin zavin miji, idan kuwa ba haka ba, shine zaki ga rayuwar aure ta wayi gari cikin qanqanin lokaci, farko sai matsaloli da tawayoyi da ci baya, su dabaibaye ta, daga qarshen al'amari su ture a kai ga rabuwa.

DALILIN DA YA SA DOLE YARINYA TA YI TAKA TSAN-TSAN.
Da aure ne ake hutar da tunani ake samun nutsuwa da cikar mutumtaka,, saboda haka wajibi ne ki faxaka a kan me kike so? Mene aikin ki? Da wa zaki yi hulxa? Shin zai yiyu ki yi huxa da qulla alaqa da shi? Shin zai iya zama namiji na gari a wajan ki ko uba na gari a wajan 'ya'yan ki? Tantancewa a wajan zaven namiji abu ne da ya zama dole, ba wai kuma gareki ba ya ke 'yar uwa, har da 'ya'yan ki saboda haka yin bincike da tantancewa abu ne da ya zama dole.

SHARUXXAN  NAMIJN DA ZA'A AURA A MUSULUNCI
Zamu kawo nasihohi da nusarwar 'ya'yan Manzon Rahama (SAW) 'ya'yan gidan sa ma'asumai, ba zai yiyu mu kawo dukkanin su ba, saidai mu kawo su a taqaice kamar haka :
1-    TA VANGAREN ADDININ SA
Wajibi ne namijin da zai nemi auren mace musulma ya zama musulmi, ko kuma muce musulma bazata auri wanda yake ba musulmi ba, domin zai iya sa ta bar addinin ta koda auren ba na musuluncin bane, amman ya halatta namiji ya auri wadda ba musulma ba, amman ba na da'imi ba saidai na wani xan lokaci.
Imam Baqir (AS) ya ce : "ku auri masu shakka a kan addini, amman kada ku aurar masu,  domin mace na xaukar xabi'un mijin ta, sai ya tilasta mata a kan addinin sa"1

2-    XABI'UN SA
Wajibi ne mijin da zaki aura ya zama mai kyakykyawan hali, domin shine zai xauki matsayin miji kuma uban 'ya'yan ki, kiyi tunani a kan shi sosai kuma kina da aminci a kan xabi'un sa?
Wani mutum ya zo wajan Imam Sadiq (AS) yana shawartar sa a kan aurar da 'yar sa ga wani mutum makusancin sa (uban 'yar) amma yana da mummunan hali, a kan ya aurau masa ko a a? Sai Imam (AS) ya ce masa : "kada ka aurar masa idan yana da mummunan hali"2
Don haka 'yar uwa ya zama dole ki bincika a kan mijin da ya zo neman ki da aure, ki ga yana da kyakykyawan hali, domin duk mutumin da ya xanxana zaqin savo da laifuka wanna ba wanda za a aura bane, saboda ba zai iya xaukar nauyin rayuwar aurataiyya da shugabancin gida ba.
    Wani mutum ya zo wajan Imam Sadiq (AS) yana shawartar sa a kan aurar da 'yar sa sai Imam (AS) ya ce masa : "ka aurar da ita ga namiji mai tsoron Allah domin idan ya so ta zai karrama ta idan yana qin ta ba zai zalunce ta ba" 1
A bisa kowane hali kamar yadda Manzon Rahama (SAW) ya faxa cewa a auri mutumin da kyawawan halin sa zasu curu zuwa ga 'ya'yan sa.
Meye fa'idar aurar mutum sananne mai kyau da matsayi ko mai dukiya amman xabi'un sa munana baya xaukar matar sa da qima da  daraja.

3-    AL'ADAR SA
Al'ada ko wace iri ce tana da tsari wajan chanja rayuwar aure, domin matar da ta kasance mijin ta xan bariki ne wanna zata qare rayuwar ta ta aure cikin azaba da wahala.
Akwai ruwayoyi da suka zo da yawa a kan 'yan bariki misali xan giya, musulunci ya hana mutum ya ba da 'yar sa ga xan giya, kamar yadda ruwaya ke qarfafa haka da cewa ;
"wanda ya aurar da 'yarsa ga xan giya haqiqa ya yanke dangantakar ta (ya vata zuriyar ta)2 mashayin giya ba za a aure shi ba ko ya nema".
 Da kuma cewa "duk wanda ya sha giya alhalin Alla (SW) ya haramta ta a kan harshe na ba wanda za a aura bane koda ya nema"3
Musulunci ya tsoratar a kan aurar mai shan giya, har ma da mace mijin ta da zai je ya sha tana da haqqin ta hana shi kanta, domin da zasu samu xa zai iya kasancewa baida tsarki. Yana daga sabbaba mummunan sakamako da masifu a aurar xan giya da xan caca.

4-    TUNTNIN SA DA MUTUMTAKAR SA
Kula da tunanin namijin da za a aura da mutumtakjar sa abu ne mai matuqar muhimmanci a cikin lamarin aure, saboda haka wajibi ne ga mace ta tantance tsakanin wanda zata aura, gaskiyar sa, mai ya fuskanta a rayuwar sa, tunanin sa a kan addnin sa, sassaucin sa, sakin hannun sa.
Matsalolin da ake samu tsakanin ma'aurata na tasowa ne, daga savanin tunani musamman ma abinda ba a yi zurfin tunani a kai ba aka yanke hukunci, ba tare da yin tunani a kan abokin zama ba.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: