bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:25:09
Xaya daga cikin mas’alolin da ake tuhumar shi’a da ita, ita ce batun Raja’a, wato dawuwa
Lambar Labari: 339
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maxaukakin sarki. Tsira  da amincin Allah su qara tabbata ga fiyayyen halitta Manzon Rahama Muhammad xan Abdullahi (s.a.w) da iyalen gidansa tsarkaka waxanda Allah ya tsarkake su tsarkakewa.
      Xaya daga cikin mas’alolin da ake tuhumar shi’a da ita, ita ce  batun Raja’a, wato dawuwa bayan mutuwa wanda da yawa daga cikin al’ummar musulmi basu yarda da ita ba, sannan kuma batu ne da ya daxe yana jawu cece kuce tsakanin al’ummar musulmi wasu ma suna ganin ‘yan shi’a ne kaxai suka yadda da wanann batu na raja’a, hakan kuma yana jawu cece  kuce tsakanin vangaroren biyu wato shi’a da sunna, shi’a dai sunyi imanin cewa akwai raja’a kamar yadda ya tabbata a alqur’ani da ruwayoyi. A wannan rubutu da mukeyi zamu yi qoqarin yin bayani akan wannan batu na raja’a da ya shige wa mutane duhu tun da kan ma’anar raja’a xin  har zuwa kan hadafin  yin raja’ar ma, muna neman Allah ya bamu da cewa da taufiqi.
                                           MA’ANAR RAJA’A
      Raja’a a luga tana nufin ko mowa ko kuma sake ko mowa: misali kamar wanda yayi tafiya yaje wani gari ya xan zauna a wannan garin zuwa wani xan lokaci bayan wani xan lokaci sai ya tafi garin su, bayan yaje garin su sai ya sake dawuwa wannan garin kaga za a ce ya dawu kenan wannan ma’anar a lugance kenan.
             MA’ANAR RAJA’A A MAHANGAR RUWAYOYI.
Domin tabbatar da batun Raja’a zamu iya bin hanyoyin ruwayoyin Sunna da Shi’a wanda hakan zai iya kaimu ga abinda muke son kaiwa gareshi. A ruwaya ta Ahlulbaiti (a.s) batun Raja;a a fili yake, akan haka Imam Sadik yana cewa: duk wanda baiyi Imani da Raja’a ba, baya daga cikinmu(1).
   Duk da cewa wasu daga cikin Malaman Shi’a sunzo da ruwayoyi akan wannan batu na Raja’a zakaga sun kawu ruwaya mafi karanci daga addu’o’in Ma’asumai (a.s). wannan binkice zamu iya ganinsu a cikin addu’o’I da zayarurin Ma’asumai (a.s) kamar: a ziyarar Jami’ul kabir, ziyarar Imam zaman, ziyarar, idin karamar sallah da babbar sallah, ziyarar uku ga watan sha’aban, da kuma ziyarar arba’in, kai dama yawan ziyarori da addu’o’in Ma’asumai kamar yadda muka fada tun a farko.
                       MANUFAR RAJA’A DAGA IMAMAI;
Raja’a aiki ne na Ubangiji, kuma dan Adam ba komai na sirrin Allah yake iya fahimta ba;
    وما أوتيتم من العلم الا قليلاBa a zo musu da ilimi ba sai dan kadan.
Ba zamu iya fahimtar yin Raja’ar Imamai ko wasu daga cikin Muminai ba; Amma haddi akalla zamu iya samun haske akan abinda Raja’a take nufi, kuma hakan zai taimaka mana wajen Imani da ita.
   Muminai da yawa sunyi Imani da Raja’a a wannan duniya, wasu kuma akan haka zamu iya cewa ba imani bane na hakika a a tilasce ta hakan, wato tunda wani bangare ne nayin Imani to sunyi Imani, amma ba wai sun fahimci hakikanin abinda hakan yake nufi bane.
   Imani da yin Raja’a mafi karanci zai bamu fa’idar cewa mumini zai samu natsuwa wajen yimasa sakayya ga wadanda suka zalunci shi, kuma hakan zai taimaka mashi kaiwa ga babban matsayi, misali ga wadnada sukayi shahada kafin bayyanar Imam Mahadi (a.s) jin cewa za a tashesu idan Imam din ya bayyana tabbas wannan abin farinciki ne garesu.
  Imani da Raja;a zai kuyar damu cewa daga karshe za a kwato hakkin duk wani wanda aka zalunta, saboda haka ya kamata duk wani mutum yayi Imani da batun Raja’a kodan saboda kwatar hakkin wanda aka zalunta.
    Sai kuma Raja’a a islxilahi: ‘Yan shi’a isna ashariyya sunyi imani da wasu daga cikin Imaman su masu tsarki zasu dawu da kuma wani vangare biyu na al’ummar Annabi Muhammadu (s.a.w), wato vangaren Muminai da kuma na kafirai. Tabbas wannan dawuwar zata kasance bayan bayyanar Imam Mahdi (a.j).
    Anan  zamu duba ayoyi da kuma ruwayoyi na sunna da shi’a akan batun jara’a xin insha Allah, zamu fara da qur’ani da raja’a.
                                      QUR’ANI DA RAJA’A
     Domin tabbatar da wannan mas’alar zamu iya shiga littafin Allah da kuma sunnar Manzonsa (s.a.w) da kuma tsayuwa akan hankali domin tabbatar da wannan aqidar.
    Zamu iya kasa ayoyi qur’ani akan wannan batun zuwa kaso uku:
Nafarko: Ayoyin da suke magana kai tsaye akan qudurar Ubangiji: Ayoyin da suke nuna ikon Ubangiji yana da iko akan komai idan muka kalle su zamu iya tabbatar da cewa raja’a abu ne mai yuwuwa ba wai mara yuwuwa ba{ أليس ذلك بقادر على أن يحيى الموتى}(1) . (( Shin Ubangiji bashi da ikon raya matacce?! Idan muka kalli irin wanann ayoyi suna da yawa a cikin alqur’ani mai girma akan batun ikon Allah ya raya matacce bayan ya mutu. Misalin haka zamu iya ganin yadda Allah maxaukakin sarki yayi da Annabinsa Uzairu lokacin da ya wuce ta wani gari, bayan da  ya dawu sai ya tarar gaba xaya mutanen garin sun mutu garin ma ya zama kufai. Annabi Uzairu ya shiga mamaki yana ganin ya za a yi haka ta faru yanzu fa ya wuce ta garin lafiya lau amma kuma a ce duk sun mutu ba kowa, a wanan halin ne Allah ya xauki ransa don ya nuna masa aya har sai da yayi shekara xari a wurin sannan Allah ya tashe shi ya tambaye shi tun yaushe yake a wurin ya ce: ai shi wuni xaya yayi koma qasa da haka. {أوكالذى مرّ على قرية وهي خاوية على عروشها قال أنى يحيى هذه الله بعد موتها فأماته الله مأة عام ثمّ بعثه قال كم لبثت قال لبثت يوما أو بعض يوم قال بل لّبثت مائة عام فانظر الى طعامك وشرابك لم يتسنّه وانظر الى حمارك ولنجعلك ءاية للناس وانظر الى العظام كيف ننشزها ثم نكسوها لحما  .
 (( Hadda zuwa qarshin ayar ayar)). Da kuma batun Annabi Ibrahim shima yanda ya tambayi Ubangiji ya nuna masa yadda yake raya matacce Allah ya ce masa: baka yi imani bane ya ce: A’a ina son dai zuciya ta ta samu nutsuwa ne, sai Allah ya ce masa: to ka samu tsuntsaye guda huxu ka cakuxa naman su a wuri guda sannan ka koma daga gefe ka riqe kan ko wane ka kira sunan sa zaka ga yadda Allah yake da masani ne kuma mai hikima ne. {واذ قال اباهيم ربّ أرنى كيف تحيى الموتى قال أولم تؤمن قال بلى ولكن ليطمئنّ قلبى قال فخذأربعة من الطّير فصرهنّ اليك ثم اجعل على كلّ جبل مّنهنّ جزءا ثم ادعهنّ يأتينك سعيا واعلم أن الله عزيز حكيم    
((   Yayin da Ibrahim ya ce: Ubangijin ka nuna man yadda kake raya matattu! Ya ce: baka yi imani ba ne? sai ya ce: A’a ina son zuciya ta ta samu natsuwa ne. sai ya ce: ka samu tsuntsaye huxu ka dake naman su wuri guda sannan ka rike kan ko wane ka kira sunan sa zaka ga yadda Allah yake mai girma kuma mai hikima)). Ayoyi suna da man gaskiya akan wannan batu na raja’a ba wani sabun abu bane a tarihin ruwar xan Adam tun daga farin faruwar mutum wanan kenan.
Sai abu na biyu: Shin akwai wata shida akan Raja’a?  Ayoyin da suke bada labari akan ba wai kawai kaxai yuwar wannan al’amarin na raja’a ne kawai ba kai harma Ubangiji yana da ikon yin hakan kuma hakan ta faru da daman gaske.
Duba qisar wasu mutane da suka yi gudun hijira saboda tsoron mutuwa, a cikin suratu bakara ayata:243,  inda Allah yake cewa: (( Shin bakaji labarin wandanda suka fita daga garinsu domin gudun mutuwa ba, sai Allah ya ce musu ku mutu, bayan sun mutu, sannan Allah ya tashesu, tabbas Allah mai falala ne akan mutane, sai dai mafi yawancin mutane basuda godiya)).
   Saboda haka batu akan Raja’a ba wani sabon abu bane, Allah yanada iko ya dawu da mutane bayan son mutu.
 A nan zamu dakata muna fatan mutane zasu ilimantu da  amfani da wannan rubutu, insha Allah zamuci gaba da kawu muku irin wadannan rubuce-rubuce masu amfani, Allah yasa mudace. Aminci ya tabbata ga wadanda sukaji shiriya kuma suka bita. Allah ka kara tsira da aminci ga shugabanmu ga Annabi Muhammad (s.a.w) da iyalen gidansa tsarkak.
  Aminci ya tabbata ga waxanda suka bi shiriya har ya zuwa ranar sakamako.comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: