bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      22:04:52
Haka zalika zaka cikin Bajhul Balaga ya zo daga sarkin muminai (as) {cewa su mata suna da tawayar hankali da addini da rabo} tawayar hankali ana fa’idantuwa da shi ta fuskanin bada shaida
Lambar Labari: 348
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Dukkanin godiya ta tabbata ga ubangiji mabuwayi tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta da iyalansa tsarkaka.
Daga cikin abinda batu kansa ya shahara a wannan zamani da muke ciki shi ne batun tawayar diya mace ta fuskanin ibadarta da hankalinta da rabon da take da shi a gado, wannan shi ne abinda ake iya fara fa’idantuwa da shi a marhala ta farko daga ba’arin wasu ayoyi daga kur’ani mai girma da madaukakan hadisai, yaduwar mas’alar tawayar hankalin mace daga namiji ta yanda zamu samu cewa wasu hadisai  daga littafin Biharul-anwar cewa suna bayyana `ya`ya mata a matsayin masu
ناقصات العقل والدين
 (suna da tawayar hankali da addini)
Haka zalika zaka cikin Bajhul Balaga ya zo daga sarkin muminai (as) {cewa su mata suna da tawayar hankali da addini da rabo} tawayar hankali ana fa’idantuwa da shi ta fuskanin bada shaida ta yanda mace biyu take daidai da namiji daya  shaidarta rabin ta namiji ce, amma batun tawayar rabonta to hakan ya kasantu ne sakamakon fadinsa madaukaki: (namiji yanada rabon mata biyu) nisa:17
Ta yanda kason namiji ke kasantuwa ninki biyun na mace, sannan dangane da tawayar ibadarta haka yana da dangantaka da barin sallarta da azumi kwanakin jinin haila dukkanin wadannan tawaya da take da ita yana kasantuwa ne da kallonmu na gama gari na farko-farko, amma da zamu kalleta da kallo na dandake bincike daga sauran bayanan da suka zo daga ayoyin kur’ani mai girma da  madaukakan hadisai da sannu zamu samu cewa maganar tauyewarta cikin mahallan da suka gabata yana daga cikin abinda dalilai basu karfafarsu, bari dai akwai ma dalilai kan akasin hakan, ita mas’alar tawayar hankalinta bisa la’akari da bada shaidarta akankin kanta bata iya wadatarwa face sai Ankara da wata macen ta biyu yar’uwarta zuwa gareta sannan zata bada cikakkiyar shaida wannan wani abu ne da aka fahimto shi daga ayar kur’ani cikin fadinsa madaukaki:
أن تضل احدهما فتذكر احدهما أخری.
Domin mantuwar dayansu sai dayar ta tuna mata.
Muna cewa zahirin wannan aya da kuma abinda za a iya fahimta daga gareta shi ne cewa shaidar ta kasance ta adalci babu banbanci daga kasantuwar me bada shaidar namiji ko mace ce, bata zai kasance ko dai daga mantuwa ko kuma gafala, sakamakon ita shaida ta alakantu da abinda yake hissi bana hankali ba wannan wani abu ne da babu shakka cikinsa, ta yanda mai bada shaida cikin wata kaziyya ko dai ya kasance abin ya faru gabansa ido da ido ko kuma dai bai gani ba, tana iya yiwuwa ya ga wani abu daban ya danganta shi da kaziyyar, sai dai cewa  wannan bai da danganta da hankali babu banbanci mace ko namiji, daga cikin abinda ke tabbatar da hakan shi ne fadinsa madaukaki:
(hakika gabani mun bada alkawali ga Adam sai ya manta bamu samu azama daga gare shi ba)
Haka ma ya zo cikin fadinsa madaukaki:
(Yace haka ayarmu ta zo maka sai ka manta ta haka yau za a manta dakai)
Ita mantuwa ka iya faruwa ga namiji hakama mace, kadai ankirayi mutum da suna (insan) sakamakon yawan mantuwarsa, daga yanayiyyika na dabi’ar mutum shi ne mantuwa da gafala wacce tana faruwa da dukkanin su biyu mace da namiji, da kasantuwar bada shaidar mata biyu a lokaci guda dalili zai kasance dalili kan tawayar hankali ga mace, da zamu samu cewa wannan gwama mata biyu zai bamu cikakken hankali kammalalle wanda wanda yake ganin hakan, sannan idan ta farko ta manta wane lamini ake da shi ne cewa ta biyun ita ma ba zata manta ba, sannan bugu da kari a muhallin tabbata da hujja zamu samu cewa ba a wadatu da mutum guda ba dole mutum biyu su kasance shaidu, to kaga a nan wurin ma mazaje biyu aka gwama da juna, shin hakan Kenan yana nuna tawayar da namiji Kenan?  Sai akara sanya lura!
Amma batun cewa mace tauyayyiya ce ta fuskanin ibada da addini da dalilin barin yin ibada kwanakin al’adarta, to anan ma indan Mukai kallo na bincike da dandakewa zamu samu sabanin da akasin haka, ta yanda hakikar lamari shi ne cewa shi ne cikar ibadarta da da’arta ga ubangijinta hakan ya kasance sakamakon rungumarta ga da umarnin ubangijinta da suka kallafu kanta cikin maudu’in barin sallarta da azumi a wannan lokaci, wannan kiyayewa ta ta yana nuni da kamalar addini ba tawaya ba, ba da ban hani da ya zo daga Allah ba da tabbas mun sameta tana azumi da sallah kuma tana mai sauke ibadarta hatta lokacin al’adarta.
Sannan idan muka dawo kan batun tawayar kasonta ana mai kafa dalili da ayar kur’ani (namiji yana da kason mata biyu) to sai muce hakikanin ma’anar ayar yana bayyana ne daga komawa ga abinda ya zo daga hadisan Ahlil-baiti (as) ya zo cikin littafin Tahzibul Ahkam na Shaik Dusi juz 9 sh 274 cikin babin mirasul aulad hadissi na 2
An karbo daga Muhammad bn Yakub daga Aliyu bn Muhammad da Muhammad bn Abu Abdullah daga Ishak bn Muhammad Naka’i yace: fahfaki ya tambayi Abu Muhammad (as) me ya sanya mace raunanna abar tausayi take samu kaso guda daya amma shi kuma namiji sai ya debe kaso biyu? Sai Abu Muhammad (as) yace: hakika ba kallafa ma mace jihadi da ciyarwa ba kadai dai suna kan namij, sai cikin zuciyata nace hakika an gaya mini cewa Ibn Abul Auja’i ya tambayi Abu Abdillah (as) irin wannan mas’alar sai ya bashi wannan amsar, sai Abu Muhammad (as) ya fuskanto ni yace: na’am hakika wannan tambayar Abul Auja’i ce  amsa daga garemu daya ce idan ma’anar tambayar ta kasance daya, abinda na farko ya tafi kai shi ne wanda na karshe ke tafiya kai hakama akasi cikin ilimi bai daya, ga manzon Allah (s.a.w) da sarkin muminai falalarsu take.
Akwai wasu dalilan daban da aka ambata cikin wannan maudu’i wanda zaka same su cikin hadisai Ahlil-baiti (as) kamar yanda ya zo daga mai gaskiyarsu Sadik (as) lokacin da aka tambaye shi me ya sanya Allah ya sanya sadaki ga diya mace. ya zo daga Imam Rida (as) kan dalilin hakan sai yace: ita mace idan tayi aure an dauketa sai namiji ya dinga bayarwa, saboda haka Allah ya cika kan maza saboda, ita mace iyalin namiji ce idan ta bukatu wajibi kansa ya bata ya ciyar da ita.
Umar Alhassan Salihu
Faroukumar66@.gmail.com
   

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: