bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      08:05:14
Haka nan mu sani abin da muke gani na lalacewa, talauci, musibu, daidaicewa, fitintinu, rashin albarkar rayuwa, rashin zaman lafiya, da sauran abubuwan da suka addabi wannan duniyar bai takaita da gazawar dan adam kan matakan da yake dauka ba kawai, lamarin ya hada da rashin kyawawan halaye da keta hurumin Allah (s.w.t) da yake wakana a duk fadin wannan duniyar. Da al’umma ta yi imani ta gyara halayenta da ta samu ludufi da tausayawar Allah mai girma, don haka akwai tasirin rashin tsarkin badini a rayuwar al’ummu wurin samun dagulewar al’ummarsu da lissafinsu.
Lambar Labari: 35
Idan mun waiwayi baya zamu ga cewa malamai sun yarda da kaiyade iyali da tsarin iyali sai dai wasu daga cikinsu sun tafi kan cewa Idan matar ‘ya ce sai da izininta amma baiwa babu komai ko babu izininta . Sannan alakar umarni da yin aure don hayayafa da yaduwar mutane masu yawa tana da alaka da zamani ne, kuma kowane zamani da yanayinsa kamar dai sauran hukunce-hukunce da suke da alaka da yanayi da wuri da zamani. Sannan babu sabani kan cewa kowane mutum yana da hakki kan tsari da kaiyade iyalinsa sai dai sabanin a kan aiwatarwar hukuma yake. Misali hukumar musulunci ta Iran tana ganin hudu ya wadatar kuma tana wasiiya da hakan sai dai wasu malamai sun saba da hakan  wasu kuma sun yarda  kowanne bisa dalilinsa. 
Mafi karfin dalili da masu ra’ayin cewa hukuma ba zata iya tsara ko kaiyade iyali ba suka kawo daga musulmi da kirista zamu ga yana maganar cewa Allah (s.w.t) ne yake halitta kuma ya saukar da arziki gwargwadon yadda zai amfani wannan halittar don haka arzikin kasashe ya wadatu ta yadda zasu iya daukar nauyin al’ummarsu. Sai dai amsar wannan lamari mai sauki ce idan muka duba cewa: Duk malamai sun yarda kuma sun hadu kan cewa lallai ne babu wata rowa daga ubangiji ga wannan duniya da ya halitta, kuma ya sanya wannan duniyar a matsayin gida guda mai arziki ga masu zamanta, amma matsalar daga dan adam ne da ya gaza ta kowace fuska. Mutum ne ya kasa fitar da wannan arziki, da tace shi, da sarrafa shi, da gudanar da shi, da raba shi bisa adalci, kuma duk da wadannan matsaloli bai tsaya kan nan ba sai ya kasance wasu ‘yan kadan suna rub da ciki da sace abin da aka samu ta yadda ba zai iya wadatar kowa ba. 
 Don haka masu waccan tambaya sun manta cewa matsalar ba ta bangaren mahaliccin ba ce domin shi ya yi komai kuma ya ajiye shi inda ya dace, amma ya danka amanar wadannan abubuwan a hannun mutum ne da ya ba wa amanar kiyayewa, sai dai mutum ne ya canja wa komai mahallinsa, don haka matsala tana nan yaya za a yi da ita!. Arzikin duniya yana nan ya ishi biliyoyin mutane masu yawan gaske, sai dai fitar da arziki, gyara shi, da tace shi, da amfani da shi yadda ya dace, da raba shi, da mayar da kudinsa ga mabukata shi ne ya yi wahala ga dan adam!. 
Don haka idan arzikin da ake iya amfana da shi sakamakon gazawar hukumomi ya zama yana daduwa da 5% ne al’ummar kasa kuma tana daduwa da 10% ne to dole ne a tsara jama’ar ta yadda zasu wadatu da abin da ake samarwa. Misalin wannan kamar mutumin da yake da albashi 5 000, amma matarsa tana ba shi lissafin kudin kashewa 10 000 ne yaya zai yi? mu kaddara duk sa’adda ya ce mata ba zan iya ba, sai ta ce: Ai Allah na nan kuma ya saukar da arzikinsa a yalwace!. Muna iya cewa: Haka ne Allah na nan amma bai ce a yi abu da ka ba kuma bai yarda da saba wa hankulanmu ba, hasali ma bai shar’anta mana abin da ya saba wa hankali ba kuma duk abin da hankali (ba dokar masu hankali ba) ya yi hukunci da shi to shari’a ta yarda da shi . 
Allah ba ya saukar da hukuncin da ya saba wa hankali don haka addini da hankali abubuwa biyu ne masu sajewa da dacewa da juna. Mu mun saba wa koyarwar Kiristanci da Ash’aranci kan wannan mas’ala matukar gaske muna masu koyi da abin da ya zo daga Ahlul-baiti (a.s). Idan muka kwatanta rayuwa tun daga tamu har ta yaranmu wadanda ya zama wajibi mu tarbiiyantar da su, da ta al’ummarmu, da duk abin da ya shafi kasarmu, zamu ga ta saba da ta yau, kuma kamar yadda sharudda suke canjawa haka nan ne hukunce-hukunce suke cajnawa. A yau duniya tana fuskantar matsalar marasa aikin yi da ta addabe ta hatta ga wadanda suka yi ilimi balle wasunsu. 
Misalin hukuncin kaiyade iyali kamar sauran hukunce-hukunce ne masu kallon yanayi da zamani da aka fi sani da fikihun rayuwa da kuma rayaiyen fikihu. Muna iya bayar da misalin irin wannan mas’ala da aka tambayi Imam Ali (a.s) game da fadin Annabi (s.a.w) "Ku canja furfura kada ku yi kama da yahudawa”. Sai ya ce: "Annabi ya fadi haka ne a lokacin da addini ya karanta (musulmi ba su da yawa) amma yanzu addini ya fadada, ya karfafa, kowa yana iya yin abin da ya zaba” . Da wannan ne zamu ga mafi yawan hukuncin shari’a game da gudanarwa, zaman tare, tafiyar da rayuwar al’umma, da makamantansu suna kallon yanayi ne. 
Wani lokacin zamu ga shari’a tana bayar da umarni ga mutane biyu, sai dai tana yaba wa daya fiye da dayan; misali shari’a tana ganin fifikon attajirin da yake yin salla a kan lokaci fiye da wanda ba ya aikin komai da yake yin salla a kan lokaci . Tare da cewa kowanne ana neman sa da yin salla kan lokaci sai dai daga attajiri ya fi zama abin jinjinawa, saboda haka shari’a tana da maslaha da yanayi da ma yanayin daidaikun mutane da take dubawa a cikin hukunce-hukuncenta. 
Don haka Kur'ani mai tsarki bai yi wurgi da sha’anin yanayi da zamani a cikin hukuncinsa ba kuma bai wurgar da kallon hakikanin rayuwa ba. Kur'ani mai daraja yana tafiya tare da abin da yake wakana na rayuwa bai yi jifa da shi ba, wanann yana nuni da matukar dacewar dokokinsa da sajewarsu da hankali. Don haka ba ma batun kawo ‘ya’ya ba, hatta da auren sai da ya yi maganar bayar da mafita ga wanda ba shi da kudin yin auren ‘ya’ya muminai!. Don haka ne hatta da lamarin auren kansa da shi ne ake samun hanyar haifar da ‘ya’ya sai da ya yi bayanin cewa: "Kuma wanda ba zai iya samun yalwar auren ‘yan mata kamammu muminai ba, to sai ya aura daga abin da hannunku suka mallaka –baiwa- daga ‘yan matan muminai…”Nisa’i: 25. 

Tasirin Badini
Haka nan mu sani abin da muke gani na lalacewa, talauci, musibu, daidaicewa, fitintinu, rashin albarkar rayuwa, rashin zaman lafiya, da sauran abubuwan da suka addabi wannan duniyar bai takaita da gazawar dan adam kan matakan da yake dauka ba kawai, lamarin ya hada da rashin kyawawan halaye da keta hurumin Allah (s.w.t) da yake wakana a duk fadin wannan duniyar. Da al’umma ta yi imani ta gyara halayenta da ta samu ludufi da tausayawar Allah mai girma, don haka akwai tasirin rashin tsarkin badini a rayuwar al’ummu wurin samun dagulewar al’ummarsu da lissafinsu. 
Yana da muhimmanci ka da mu manta da wani abu wanda yake boyuwa ga mafi yawan mutane da ya shafi lamarin cewa duniya ta cika da zalunci mummuna kuma wannan zaluncin ne ya sanya barna ta cika a cikin sarari da cikin ruwa, kuma yana tasiri wurin dauke albarka a rayuwar al’umma. Mafi munin sabo wanda yake shi ne kashe mutum ya zama ruwan dare, tsafi da yake kawar da albarka al’umma ya mamaye ko’ina, zina da take janye albarkar gida ta yawaita, tauye mudu, zambo, cin kudin ruwa da yaudara a kasuwanci ya zama hanyar samun arziki, hada da sabuka masu yawan hadarin gaske na zubar da jini da suka mamaye rayuwar al’umma. 
Idan mun duba matsalolin zahiri da suka kawo wa dan adam bala’i da barazana a rayuwarsa da suka hada da: Rashin ikon fitar da albarkatu kamar yadda ya dace, Rashin ikon sarrafa su daidai, Rashin ikon raba su daidai, Karancin kwarewa, Karancin ma’aikata da aiki, Mummunar gudanarwa, samun dama da yin mummunan amfani da ita, Satar kudin al’ummu, Raba arzikin al’umma ba yadda ya dace ba, Rubabben tattalin arziki, Da sauran abubuwa masu yawan gaske. To a gefe guda zamu ga abubuwan badini da duniya ta ki himmantuwa da duba su da suka hada da: Kisan mutane, Zalunci a kurkuku, Zalunci a waje, Rashin tsoron Allah, Rashin zakka da humusi, Zina da yaduwarta, Luwadi da jawo mani, Gallazawa talakawa, Ha’inci da yawaitarsa, Karya da zambo a rayuwar talakawa da masu mulki, Rashin tuba da neman gafara, da sauran abubuwa masu yawan gaske wadanda suke da tasiri na farko kan wannan lalacewa kuma suke tasiri kan rayuwar al’umma.
Daya daga cikin abubuwan da suka dade suna ba ni mamaki wadadna suke nuni da lalacewar al’umma shi ne lalacewar tarbiiya da ta kai ga matsayin masu fashi suna zuwa wuri su yi fashi amma da sun watsar da wasu daga dukiyoyin fashin a kasa sai al’umma su sanya wawasu maimakon su tara su mayar wa masu dukiyar. Kuma kowane abu sai an kulle shi da makulli hatta da mitar wuta in ba haka ba wasu zasu iya cire ta. Hatta da fayef da muka sanya wa rariyar gidajenmu don mu samu saukin wucewa da motoci sai da aka daddake shi daga rariyar aka tafi da shi. Gaya mini yaya al’ummar da take cikin wannan yanayin take tsammanin samun albarkar Ubangijin Talikai. 
Tunanin wannan al’ummar ya kai ga mai gaya musu gaskiya yana iya komawa makiyi cikin sauki. Misali ya kamata a kowane yanki da ke cikin birane ya zama akwai filin wasa, filin shakatawa, wurin iyo a ruwa, gidan bahaya da wanka, filin asibiti, filin wurin kula da gajiyaiyu, filin makaranta, filin masallaci, filin kasuwa, hanyar wucewa mai yalwa da fadi. Sai dai da wani mai kula da unguwa bai kiyaye hakkin tsarin mahalli ba, sai wani ya zo ya sayi filin wasanni da aka ware wa mutane, sai wani ya ga bari ya gaya masa gaskiya cewa kada ya saya domin na al’umma ne!. To wannan wanda ya gaya masa gaskiya yana iya zama makiyinsa a matsayin wanda yake kyashin samun arzikinsa. Da wani zai kara filin hanya a gininsa sai wani ya yi masa nasiha to shi ma yana iya zama abokin gaba. Al’ummar da take haka shin kuwa da gaske take tana son rahamar Allah! 
Don haka ko da al’umma ta kaiyade kuma ta tsara iyali to tana iya fuskantar dauke albarka daga rayuwarta ta yadda rayuwar zata yi mata kunci matukar gaske matukar ba ta koma ga Allah (s.w.t) ta gyara halayenta ba. Haka nan ma idan muka kaddara cewa ta kaiyade iyalin kuma arzikin kasa ya wadaci al'umma ta fuskancin adadinta sai dai kuma ba a kiyaye raba arzikin kasa ba ta yadda ya rage a hannun na sama. Don haka da bukatar karfafa wa al’umma da yi mata nasiha da daukar mataki daga bangaren masu ikon nagari da malamai nagari kan ganin an kawar da fasadin da take ciki don samun saukin lamurran rayuwarta. Wannan yana nuna ke nan daya matakin yana hannun mutum wato daukar matakan gyara na zahirin rayuwa kamar gudanarwa mai kyau, da kuma daukar matakan gyaran badini da ya shafi tsoron Allah da bin dokokinsa. Sai kuma daya bangaren wanda yake hannun Allah (s.w.t) da ya shafi bayar da walwalar arziki da albarka da samar da nutsuwar rai ga mutane kuma shi ne zai sanya sauki a rayuwar mutane gwargwadon matakan gyarawa da suka dauka!. Allah ya sa mu dace!. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: