bayyinaat

Published time: 10 ,December ,2020      15:52:25
Wannan wani Slogan, Sha'a'ir, Take ne na 'yan gwagwarmaya wanda Maulana Sayyid Zakzaky (h) yazo da shi, kuma asalinsa daga waki'ar Ranar Ashura ne.
Lambar Labari: 363
 • BA'A KAUDA GASKIYA DA BAKIN BINDIGA.

  KASHI NA FARKO.

  Wannan wani Slogan, Sha'a'ir, Take ne na 'yan gwagwarmaya wanda Maulana Sayyid Zakzaky (h) yazo da shi, kuma asalinsa daga waki'ar Ranar Ashura ne.

  Ranar Ashura, Rana ce da aka Hurawa Al'umma Rai, Rana ce da Jini yayi Nasara akan Takobi, Rana ce da Gaskiya tayi Rinjaye akan Bata, Rana ce da Karamar Runduna tayi galaba akan Babba da izinin Allah.

  Sayyada Zainab a fadar Yazidu a cikin jerin maganganun data yamutsa shi da su ta ce masa;

  'يا يزيد! كد كيدك واسع سعيك ناصب جهدك فوالله لا تمحوا ذكرنا ولا تميت وحينا'

  Ma'ana ya kai Yazidu! Ka Kulla duk kulle-kullenka, ka aikata duk abinda zaka aikata, ka tattaro duk kokarinka, na rantse da Allah ba zaka iya shafe ambaton mu ba, ba kuma zaka iya buce wahayin mu ba. Ya jama'a yau ga kalaman waliyyiyar Allah Zainab sun tabbata, ambaton Hussain kullum sai daukaka yake yi. Allah (swt) a cikin Alkur'ani yana cewa;

  "...فأما الزبد فيذهب جفاء و أما ما ينفع الناس فيمكث في الأرض..."

  Wato shi Kumfa yana tafiya ne a banza yabi Iska ya buce,(dama bashi da wani amfani ga mutane) amma abinda zai amfani mutane (Ruwa da Alatun dake cikinsa) suna zama daram a cikin kasa su wanzu.

  Idan kuka lura Rundunar Yazidu da duk yawansu da babakerensu, suna ina yanzu? Ashe duk Kumfa ne Burodi ne mai kumburin banza.

  "كان لم تغن بالأمس"

  Kai kace ba sune masu cika baki ba a jiya, suna can sai kururuwar Nadama a cikin Barzahu da La'antar Junansu sukeyi. Hussainawa kuwa yanzu su ke sha'anin su, suna mamaye kasa, muryoyinsu kawai ke tashi, tutocinsu ke filfilawa, makiyansu yau sune cikin firgici da tashin Hankali.

  KU BIYO NI ZUWA KASHI NA KARSHE. • KASHI NA KARSHE.

  Na'am! A yanzu akwai masu aikin Yazidanci, masu busassun zukata fiye da ta Yazidu, eh, haka ne don ina da kakkarfan zaton cewa da Buhari da El-Rufa'i ne a makwafin Yazidu zasu yi fiye da abinda yayi. Baku gani ba Yazidu da Sayyada Zainab ta buge shi da hujja yayi borin kunya yasa an saki Ribatattun yaki ba, duk kuwa da cewa a lokacin babu kotu da zata hukunta shi, babu masu kwarmaton kare hakkin dan Adam, kuma mulkin sa mai dawwama ne har mutuwa, kuma in ma ya mutu dan sa ne zai gaje shi. Amma duk da wadannan hujja ta karya alkadarinsa yaji tsoron faduwar mulkin sa, ya canza takunsa, har yazo yana la'antar gwamnan sa na Kufa Ubaidullah, yana barranta daga mugun aikinsa (duk da cewa karya yake yaji tsoro ne) yasa aka saki wadanda aka kamo, suka kama hanyar komawa Madina.

  Amma yau Buhari da El-Rufa'i duk irin dimbin hujjojin da 'yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky (h) suka buge su da su, sun kafa kwamitin bincike na JCI, mun buge su, kwamitin ya wanke mu tas, an je kotu ita ma ta basu rashin gaskiya, ta ce a saki Malamin mu Jikan Imam Hussain, kuma a biya shi diiya, a gina masa gida a inda yake so, 'yan Majalissu da sauran manyan mutane a kasa da ma wasu kasashen da wasu malaman Addini sun yi ta kiraye-kirayen a saki Sayyid, amma wadannan masu busassun zukatan, masu mulkin da ba'a gado, mulkin da aka diba masa lokaci, mulkin Dimokuradiyya na hadaka, sun yi kunnen Uwar shegu.

  Rayuwar Sayyid duk da yanayin da yake ciki na rashin lafiya kadai ya isa yasa wadannan mutanen su saduda suyi Nadama, domin wannan ya nuna akwai hannun Allah a cikin lamarin, kamar yadda Allah (swt) ya tsawaita rayuwar Imam Zainul Abidin (as), ku lura ku gani bashi da lafiya akayi wannan waki'ar, kuma da wannan yanayin na matsanancin rashin lafiyar da ta hana shi daukar takobi domin bada kariya ga Babansa, akayi wannan doguwar tafiyar ta kwanaki 22 da shi, ba wadataccen abinci, ba magani, ga wahalar tafiya, amma Allah bai ga damar ya mutu ba, ya tsawaita rayuwar sa har yaga bayan Yazidu da Ubaidullah.

Insha Allahu yadda Imam Sajjad (as) yaga bayan Yazidu da Ubaidullah, haka jikansu Maulana Sayyid Zakzaky (h) zai ga bayan Buhari da El-Rufa'i.
Karshen da'awar mu shi ne Alhamdulillah Rabbil Alamin.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: