bayyinaat

Published time: 11 ,December ,2020      23:00:44
Lambar Labari: 384
Kamar yadda suka saba, nuna Musulunci a mummunar kama, hakanan in sun yi mugun aiki su kan yi kokarin shafe shi da nuna shi a bai-bai, wannan karon ma gwamnatin Najeriya ce a fakaice, ta hannun wani marubuci wanda ba musulmi ba suka buga littafi, wanda a ciki suka yi kokarin nuna wadanda aka zalunta a matsayin 'yan tashin hankali, masu kokarin tarwatsa zaman lafiyar Kasa. Wannan canjin salo na su yazo ne a lokacin da suka fahimci cewa karfi ba zai yi musu maganin harkar musulunci a Najeriya ba, domin kuwa kara mata karfi da goyon baya ma yake yi.

Ganin cewa littafin nasu bai samu karbuwa ba, sai suke yunkurin mai da shi a siga na fim. Sun shirya fim din sosai wanda abin takaici hadda wani shahararren dan fim musulmi a cikin sa, amma ba abinda fim din ya kunsa face cin zarafi ga Addinin Musulunci da Musulmai gabakidaya, domin kuwa sun yi izgili ga wasu abubuwa da suke abin girmamawar Musulunci ne.

Wani abin takaici ma shi ne, fara bayyanar wannan kazamin fim din, yazo a dai-dai lokacin da Musulmin Duniya su ke takaici da jimamin abinda ya faru a kasar Faransa na cin zarafin Manzon Allah (saw) da wata mujalla a kasar tayi, kuma a dai-dai lokacin da a ke sifanta Manzon Musulunci da Musulmi a matsayin 'yan ta'adda, shi kuma Musulunci a matsayin Addinin ta'addanci. Shi wannan fim din gabakidayan wadanda suka shirya shi ba Musulmai ba ne, kuma an shirya shi a yankin da ba na Musulmai ba, wanda yake nufin tilas Musulmai su hade kan su, su man ce da banbance-banbancen da ke tsakanin su, su la'anci wannan fim din su barranta daga gareshi su gano makircin da ke kunshe a cikin sa.

Allah ya taimaki Musulunci da Musulmai ya hada kawukansu ya sa su farka su gano makircin da a ke Kulla musu da hadin bakin wasu baragurbi daga cin su.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: