bayyinaat

Published time: 11 ,December ,2020      23:10:35
و مثلي لا يبايع مثل يزيد
Gaskiyar magana Ashura ba munasaba ba ce ta kuka da alhini kawai ba, a'a munasaba ce ta zaburantar da masu Addini da Aqida, masu Mutunci da Mutuntaka, Mazlumai domin su yunkura su kwaci Addininsu da Aqidarsu da Mutuncinsu da Haqqinsu a wurin Azzalumai Yazidawan zamaninsu. Saboda haka a matsayinka na dan shi'a (ko in ce mai addini) kuma Hussainy baka da wani Addini ko Aqida ko mutunci ko Identity da ya wuce wannan
Lambar Labari: 386
Idan muka sa diqqa da lura dangane da wannan shahararriyar jumlar ta Imam Hussain (A.S) wacce take kunshe da ma'anar ' kwatankwacina baya mubaya'a ga kwatankwacin Yazid.' Me yasa Imam (A.S) bai ce ba, *"انا لا ابايع يزيد"*' Ni ba zan yiwa Yazidu mubaya'a ba.' A nan sai mu ce Imam (A.S) ya bada wata 'Qa'ida Ammah ce', 'General Law' cewa duk wanda ya ke shi irin Imam Hussain (A.S) ne a Addini da Aqida, a Akhlaq, a Mutunci da Mutuntaka, to ba zai yi mubaya'a ba ga irin Yazidu a Addini da Aqida, a Fasadi, a rashin Mutunci da Mutuntaka ba.

Don haka al'amarin Imam Hussain (A.S) Addini ne, Aqida ce, Mutunci ne da Mutuntaka, ba wata waqi'a ce data faru a tarihi kuma ake karantawa a littafi a yi kuka kawai ba. Shi yasa Sayyid Musa Sadar yake cewa,

*'لا تسجنوا الحسين في التاريخ، فلكل عصر حسين مصلح و يزيد مفسد'*

Wato kar ku killace Alhussain a cikin zauren tarihi, kowane zamani akwai Alhussain mai gyara akwai Yazidu mai barna.

Gaskiyar magana Ashura ba munasaba ba ce ta kuka da alhini kawai ba, a'a munasaba ce ta zaburantar da masu Addini da Aqida, masu Mutunci da Mutuntaka, Mazlumai domin su yunkura su kwaci Addininsu da Aqidarsu da Mutuncinsu da Haqqinsu a wurin Azzalumai Yazidawan zamaninsu. Saboda haka a matsayinka na dan shi'a (ko in ce mai addini) kuma Hussainy baka da wani Addini ko Aqida ko mutunci ko Identity da ya wuce wannan.

Lallai thaurar (juyin juya hali) Imam Hussain (A.S) bata taba tsayawa ba balle ta zama tarihi abin tunawa ba, a'a a'a Kullum cikinta muke madamar azzalumai yazidawa suna shakar iskar 'yanci a doron kasa.

*'كل يوم عاشوراء و كل أرض كربلاء'*

*KO WACCE RANA ASHURA CE KUMA KO WACCE KASA KARBALA CE.*

*لا نكون كاالذي يأكل مع الذئب و يبكى مع الراعي*.

Kar mu zama kamar wanda ya ke ci tare da Kura kuma ya ke kuka tare da makiyayi. Muje zaman makokin Imam Hussain (A.S) muna matse idanu muna kuka, in mun fita muyi jinjina ga Yazidu (magajin yazidun da ke mulkarmu).

Domin massala al'amarin Ashura a rayuwarmu, da maida al'amarin fada da zalunci ya zama wani bangare na rayuwarmu (wadda ba zata kammala ba sai da shi), yasa A'imma (A.S) suka sunnanta mana karanta ziyarar Imam Hussain (A.S) (ziyarar Ashura) a kusan kowace muhimmiyar rana da munasabobi wadda a cikin ta muke cewa,
*"اني سلم لمن سالمكم و حرب لمن حاربكم الي يوم القيامة"*
Ni zan zauna lafiya da duk wanda ya nemi zaman lafiya da ku kuma zan yaki duk wanda ya nemi yaki da ku i zuwa ranar tashin alqiyama.
Don haka Khaddin su Sayyid Khamna'i, Khaddin su Sayyid Nasrullah da Khaddin su Sayyid Zakzaky su ne suke massala haqiqanin Ashura Al-mustamirra ila yaumil qiyamati.
Allah ka taimaki mazlumai a duk inda suke a fadin duniya ka murkushe azzalumai, ka kiyashe mu bata cikin shiriya.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: