bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2020      01:51:06
DARASI* *NA DAYA *SANIN* *JAGORA.*
Yazo a cikin addu'a "Ya ubangiji ka sanar da ni kanka domin idan baka sanar da ni kanka ba, ba zan san Manzon ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Manzon ka domin idan baka sanar da ni Manzon ka ba, ba zan san Hujjar ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Hujjar ka domin idan ba ka sanar da ni Hujjar ka ba, zan bace a addini na."
Lambar Labari: 390
A cikin Alqur'ani mai tsarki Allah (swt) ya na cewa "Kadai wadanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayin sa su ne malamai (masanan Allah)

Yazo a cikin addu'a "Ya ubangiji ka sanar da ni kanka domin idan baka sanar da ni kanka ba, ba zan san Manzon ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Manzon ka domin idan baka sanar da ni Manzon ka ba, ba zan san Hujjar ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Hujjar ka domin idan ba ka sanar da ni Hujjar ka ba, zan bace a addini na."

Yazo a cikin hadisi daga Amirul Muminin Ali (A.S) yana cewa: *"Ka san* *ni* *baka* *taimake* *ni* *ba,* *ya fi* *ka taimake* *ni* *baka* *san* *ni* *ba."*

Hakika mafi girman al'amari shi ne sanin Allah sannan sanin Manzo, sannan sanin Hujja da ma'ana na haqiqa wanda yake da ab'ad masu yawa.

Hakika Abdulrahman bn Muljam da dan uwan sa a aiki wato Shimr bn Zil Jaushan su na daga cikin mabiya Amirul Muminin Ali (A.S) kuma mataimaka a gareshi, domin sun halarci yakokin da Amirul Muminin ya jagoranta akan 'yan tawaye sun zare takobi sosai sun yi yaki, sun yi fafutikar ganin Amirul Muminin (A.S) ya yi nasara sun bada jinin su an sare su sun sara, duk domin kare martabar jagora (A.S)
Amma me ya faru daga baya (da yake basu san jagoran ba) sai na farkon ya juyar da takobin sa ya sare abin kaunarsa a da, yayin da na biyun shi kuma ya juyar da takobin sa ya datse wuyan dan abin kaunarsa a da. Ya subhanallah!!! wannan shi ne bata bayan shiriya. Allah (swt) ya tsare mu.

Lallai akwai *DARASI* babba anan cewa har kullum kada taimakon da mu ke jin muna yiwa addini ko jagora ya rude mu, mu yi takatsantsan, mu nemi sanin addinin. Amirul Muminin a farkon hudubar sa ta cikin Nahjul Balaga yana cewa "Auwalul din ma'arifatuhu" ma'ana "Farkon al'amari a addini shi ne sanin addinin" mu nemi sanin Allah da Manzon sa, mu nemi sanin Jagora. Sai mu samu tsabta a tafiyar mu a karshe kuma cikin taimakon Allah mu gama da duniya lafiya ba tare da mun juye mun zama wani abu dabam ba. Allah shi tsare mu bata bayan shiriya.

*DARASI* *NA BIYU:*

*IKHLASI:*

Hakika Amirul Muminin (A.S) shi ne mafi girman tubalan gina addinin nan ya sha wahalhalu daga ciki da wajen addinin ba wani yaqi da Annabi mai tsira da aminci ya halarta kuma aka fafata face yaje da Ali, garuruwa da dama in sun gagara Annabi, Ali ya ke turawa ya je ya share masa hawayen sa ya sha wahala maras misali ya sara an sare shi, ya tsaya kyam har addinin ya tabbata daram.
Amma me ya faru bayan tabbatuwar addinin sai aka ture shi gefe (ba Annabi ne ya ture shi gefe ba fa a'a 'yan bani na iya ne) a ka haramta masa duk wata walwala da nishadi a addinin, daga baya da ragamar addinin ta dawo hannun sa, nan ma suka hana shi sakat suka bishi da yakoki a karshe suka dinga yada propaganda cewa shi ba ma musulmi ba ne, a'a ba shi da wata alaqa ma da Annabin, a'a ya ma cutar da Annabin ne. Kana daga bisani suka hallaka shi.
Kalmar Amirul Muminin (A.S) ta farko bayan dan ta'adda ya sare shi ita ce *"FUZ* *TU WA* *RABBIL* *KA'ABATI"* ma'ana " na rantse da Ubangijin ka'aba na rabauta" *Kai* *jama'a!!!* Wannan yana nuna kololuwar ikhlasin Ali (A.S) da cewa duk abinda yayi a baya yayi ne saboda Allah ba domin addinin ko mabiya addinin su saka masa ba.
Lallai akwai *DARASI* babba anan ga 'yan gwagwarmaya cewa kayi abinka saboda Allah, kar ka damu da matsayin da gwagwarmaya zata baka ko tsangwamar da abokan gwagwarmaya zasu nuna maka, a'a malam kai dai yi abinka *KHALISAN* *LI* *WAJHILLAH,* sai ka zama irin Amirul Muminin (A.S). Allah ya taimake mu da ikhlasi a addinin mu.
A karshe muna tawassuli da jarumta ta Ali da juriyar sa da ikhlasin sa da wadannan kwanaki na shahadarsa Allah ba don mu da ayyukan mu gurbatattu ba, Allah ka gaggauta kwato mana jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) daga hannun wadannan miyagun ka bude kwakwale da zukatan al'ummar mu su fahimci mai kiran su zuwa ga tsira su taho kungiya kungiya zuwa gareshi. Ka gaggauta hallaka mujrimai, miyagu, mugaye, marassa amfani ga duniyar mu ballantana lahirar mu.
*M M KAZAURE*
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: