bayyinaat

Published time: 09 ,February ,2017      09:15:11
Tana karantar da rashin bambanci tsakanin musulmi, rikon addini da gaskiya shi ne daukaka, An ce wannan sura ta sauka ne lokaci da Abdullahi bn Maktum ya zo wajen Usman sai ya daure fuskarsa saboda yana makaho kuma mabukaci
Lambar Labari: 40
Tana karantar da rashin bambanci tsakanin musulmi, rikon addini da gaskiya shi ne daukaka, An ce wannan sura ta sauka ne lokaci da Abdullahi bn Maktum ya zo wajen Usman sai ya daure fuskarsa saboda yana makaho kuma mabukaciبِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
عَبَسَ وَتَوَلَّى 

1. Ya hada fuska kuma ya juya baya.

أَن جَاءَهُ الْأَعْمَى 

2. Saboda makaho ya zo masa.

وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى 

3. To, me ya sanar da kai cewa watakila shi ne zai tsarkaka.

أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَى 

4. Ko ya tuna, sai tunawar ta amfane shi?

أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى 

5. Amma wanda ya wadatu da dukiya.

فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّى 

6. Sa'an nan kai kuma ka bijira zuwa gare shi!

وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى 

7. To, me zai cuce ka idan bai tsarkaka ba?

وَأَمَّا مَن جَاءَكَ يَسْعَى 

8. Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugawa.

وَهُوَ يَخْشَى 

9. Alhali shi yana jin tsoron Allah.

فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّى 

10. Kai kuma ka shagala ga barinsa!

كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ 

11. A'aha! Lalle ne, wannan tunatarwa ce.

فَمَن شَاء ذَكَرَهُ 

12. Saboda wanda ya so ya tuna Shi.

فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ 

13. A cikin littattafai ababan girmamawa.

مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ 

14. Ababan daukakawa, ababan tsarkakewa.

بِأَيْدِي سَفَرَةٍ 

15. A hannayen mala'iku marubuta.

كِرَامٍ بَرَرَةٍ 

16. Masu daraja, masu da'a ga Allah.

قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ 

17. An la'ani mutum (kafiri), mamakin yawan kafircinsa!

مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ 

18. Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ 

19. Daga digon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya kaddara shi.

ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ 

20. Sa'an nan Ya saukake masa hanyarsa.

ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ 

21. Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنشَرَهُ 

22. Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tayar da shi.

كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ 

23. Hakika bai wada aikata abin da (Allah) Ya umurce shi ba.
 
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَى طَعَامِهِ 

24. To, mutum ya duba zuwa ga abincinsa.

أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا 

25. Lalle ne Mu, Mun zubo ruwa, zubowa.

ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا 

26. Sa'an nan, Muka tsattsage kasa tsattsagewa.

فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا 

27. Sa'an nan, Muka tsirar da kwaya ,a cikinta.

وَعِنَبًا وَقَضْبًا 

28. Da inabi da ciyawa.

وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا 

29. Da zaituni da itacen dabino.

وَحَدَائِقَ غُلْبًا 

30. Da lambuna, masu yawan itace.

وَفَاكِهَةً وَأَبًّا 

31. Da 'ya'yan itacen marmari, da makiyaya ta dabbobi.

مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ 

32. Domin jin dadi a gareku, ku da dabbobinku.

فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ 

33. To, idan mai tsawa (busa ta biyu) ta zo.

يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ 

34. Ranar da mutum yake gudu daga dan'uwansa.

وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ 

35. Da uwarsa da ubansa.

وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ 

36. Da matarsa da diyansa.

لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ 

37. Ga kowane mutum daga cikinsu, a ranar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ

38. Wasu fuskoki, a ranar nan, masu haske ne.

ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ

39. Masu dariya ne, masu bushara.

وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ

40. Wasu fuskoki, a ranar nan, akwai kura a kansu.

تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ 

41. Baki zai rufe su.

أُوْلَئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ 

42. Wadannan su ne kafirai fajirai.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: