bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:16:40
Tana karantar da cewa rayarwa da matarwa a hannun Allah suke, su kuma nau’i-nau’i ne. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 5

سورة الأعلى

Surar Mafi Daukaka

Tana karantar da cewa rayarwa da matarwa a hannun Allah suke, su kuma nau’i-nau’i ne

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى

1. Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi daukaka.

الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّى

2. Wanda Ya yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.

وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَى

3. Kuma Wanda Ya kaddara (abin da ya so) sannan Ya shiryar.

وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَى

4. Kuma Wanda Ya fitar da makiyaya.

فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَى

5. Sa'an nan Ya mayar da ita kekasassa, baka.

سَنُقْرِؤُكَ فَلَا تَنسَى

6. Za mu karantar da kai, saboda haka ba za ka manta ba.

إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَى

7. Face abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake boye.

وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَى

8. Kuma za Mu saukake maka zuwa ga mai sauki.

فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَى

9. Saboda baka, ka tunatar, idan tunatarwa za ta yi amfani.

سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَى

10. Wanda yake tsoron (Allah) Zai tuna.

وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى

11. Kuma shakiyyi, zai nisanceta.

الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَى

12. Wanda zai shiga wuta mafi girma.

ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَى

13. Sa'an nan ba zai mutu ba a cikinta, kuma ba zai rayu ba.

قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّى

14. Lalle ne wanda ya tsarkaka ya samu babban rabo.

وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّى

15. Kuma ya ambaci sunan Ubangijinsa, sa'an nan ya yi salla.

بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا

16. Ba haka ba! Kuna dai zabin rayuwar duniya ne.

وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَى

17. Alhalin Lahira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

إِنَّ هَذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَى

18. Hakika wannan yana cikin littattafan farko.

صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَى

19. Littattafan Ibrahim da Musa.

Hafiz Muhammad Sa'id

Haidar Center for Islamic Propagation

+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)

(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: