bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:18:23
Tana karantar da yin hujja da abin da ake iya gani da ido domin a fahimci abin da ake gani da hankali, gwargwadon tunanin abokin magana. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 6
سورة الغاشية

Surar Mai Rufewa

Tana karantar da yin hujja da abin da ake iya gani da ido domin a fahimci abin da ake gani da hankali, gwargwadon tunanin abokin magana. 


بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ 

1. Shin labarin (Kiyama) mai rufe (mutane da tsoronta) ya zo maka?

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ 

2. Wasu fuskoki a ranar nan kaskantattu ne. 

عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ 

3. Masu aikin wahala ne, masu gajiya. 

تَصْلَى نَارًا حَامِيَةً 

4. Za su shiga wata wuta mai zafi. 

تُسْقَى مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ 

5. Ana shayar da su daga wani marmaro mai zafin ruwa. 

لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ 

6. Ba su da wani abinci face dai daga danyi. 

لَا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِن جُوعٍ 

7. Ba ya sanya kiba, kuma ba ya wadatarwa daga yunwa. 

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ 

8. Wasu fuskoki a ranar nan masu ni'ima ne. 

لِسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ 

9. Masu yarda ne game da aikinsu. 

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ 

10. A cikin Aljanna madaukakiya. 

لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً 

11. Ba za su ji yasassar magana ba, a cikinta. 

فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ 

12. A cikinta akwai marmaro mai gudana. 

فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ 

13. A cikinta akwai gadaje madaukaka. 

وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ 

14. Da kofuna ar'aje. 

وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ 

15. Da filoli (matasan kai) a jere.

وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ 

16. Da katifu shimfide. 

أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ 

17. Ashe to ba zasu yi duba ga rakuma ba yadda aka halitta su?

وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ 

18. Da zuwa ga sama yadda aka daukaka ta?

وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ 

19. Da zuwa ga duwatsu yadda aka kafa su?

وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ 

20. Da zuwa ga kasa yadda aka shimfida ta?

فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ 

21. Saboda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. 

لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ 

22. Kai ba mai tankwasawa a kansu ba ne. 

إِلَّا مَن تَوَلَّى وَكَفَرَ 

23. Sai dai duk wanda ya juya baya, kuma ya kafirta. 

فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ 

24. To, Allah zai yi masa azaba, azabar nan da take mafi girma. 

إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ 

25. Lalle ne, zuwa gare Mu komowarsu take. 

ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ 

26. Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisabi.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: