bayyinaat

Published time: 15 ,March ,2017      16:49:41
Imam Hasan (a.s) ya amsa wa sarkin mas'alolin da ya kawo zuwa ga babansa Imam Ali (a.s) domin a amsa masa su, sai Imam Ali (a.s) ya nemi dan sakon ya zabi wani daga 'ya'yansa domin ya amsa masa, sai ya zabi Imam Hasan (a.s).
Lambar Labari: 77
Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da bayanin halayen Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) da rayuwarsa.
 Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.
Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da yake kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.
Imam Hasan (a.s) ya kasance madogara a zamaninsa ga dukkan wani mai neman mafaka domin sanin shiriyar da kakansa annabin Allah (s.a.w) ya zo da ita, ya amsa shubuhohin masu addinai da masu neman kawo rudu domin tseratar da al’umma da sharrin batansu.

Akwai wani abu na karama da ya faru yayin da dan sakkon ya zo, domin ya gaya wa Imam Ali (a.s) cewa shi daga al'ummarsa yake, sai ya nuna masa cewa karya yake yi, shi yana cikin mabiya Mu'awiya ne, sai mutum ya gaskata hakan sannan sai ya ce; Mu'awiya ne ya aiko shi ya tambayi wannan tambayoyin da sarikin Ruma ya aiko masa shi kuwa ba zai iya amsawa ba.
Daga amsoshin da Imam Hasan (a.s) ya bayar sun hada da cewa: 
Tsakanin gaskiya da karya 'yan yatsu hudu ne, domin gaskiya shi ne abin da ka gani, karya kuwa shi ne abin da ka ji. Amma abin da yake tsakanin sama da kasa ita ce addu'ar wanda aka zalunta, da iyakacin abin da gani ya hango. Amma tafiyar wuni daya ita ce abin da yake tsakanin gabas da yamma.  Amma kausu kazahin, shi kazahu sunan shedan ne, shi kausu sunan Allah ne, kuma shi alama ce ta yalwa da aminci ga mutanen duniya daga dulmiya cikin ruwa.   
Amma kuwa Hunsa shi ne wanda ba a sani ba namiji ne ko mace, don haka sai a saurara idan ya yi mafarki to namiji ne, idan kuwa mace ce to zai yi haila kuma nononsa ya fito, idan ba a samu wadannan ba, sai a gaya masa ya mike tsaye ya yi fitsari, idan fitsarin ya samu bango to namiji ne, idan kuwa fitsarinsa ya yi kasa kamar yadda na rakumi yake yin kasa to shi mace ne.
Amma abubuwa goma da wani ya fi wani karfi su ne; mafi karfin abin da Allah ya halitta shi ne dutse, shi kuwa karfe da yake yanka dutse ya fi shi karfi, abin da kuwa ya fi karfe tsanani ita ce wuta da take narka karfe, ruwa kuwa ya fi wuta tsanani, gajimare ya fi ruwa tsanani, iska kuwa da take daukar gajimare ta fi shi karfi, mala'ikan da yake kora ita iskar ya fi ta karfi, shi kuwa wannan mala'ikan mal'ikan mutuwa da yake dauke ransa ya fi shi karfi, shi kuwa mala'ikan mutuwa mutuwar da take dauke ransa ta fi shi karfi, ita kuwa mutuwa abin da ya fi ta karfi shi ne umarnin Allah da yake ije (ture da tunkude ko ingije) mutuwar.
Imam Hasan (a.s) ya shahara da kyautata wa wanda ya munana masa. Ana ruwaitowa wata rana ya samu wata akuya da aka karya mata kafa sai ya ce: Waye ya karya ta? Sai wani bawansa ya ce: Ni ne. Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: Saboda me? Sai ya ce: Domin in sanya maka bakin ciki da damuwa. 
Sai Imam Hasan (a.s) ya yi murmushi ya ce: Ni kuwa sai na faranta maka rai, sai ya 'yanta shi, sannan ya ba shi kyauta mai yawa.
Ya kasance mafi bautar mutane ga Allah a zamaninsa kuma mafi iliminsu kuma mafificinsu, kuma ya fi kowa kama da Annabi (s.a.w), kuma mafi girman Ahlul Baiti a zamanisa kuma mafi hakurin mutane.
Ya kasance daga cikin karamcinsa, daya daga cikin kuyanginsa ta mika masa wani damki na turaren kamshi sai ya ce: ke 'yantacciya ce. Sai ya ce: haka nan Ubangijinmu ya tarbiyyantar da mu yayin da ya ce: "Idan aka gaishe da ku to ku amsa da mafi kyawu daga gareta ko kuma ku yi raddinta" .
Yana daga cikin hakurinsa cewa wani mutumin Sham ya gan shi yana haye da dabba, sai ya rika la'antarsa shi kuma Imam Hasan (a.s) ba ya yi masa raddi, yayin da ya gama sai Imam Hasan (a.s) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai, amma da ka… roke mu da mun ba ka, da kuma ka nemi shiryarwar mu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa, idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai idan kuma kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korare ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka .
Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa.
Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu'awiya domin maslahar musulunci da al'umma gaba daya, ba don wannan sulhun ba to da an kashe duk wani mumini wanda ya rage hada da Imam Hasan da Imam Husain (a.s) da sauran alayen manzon Allah da sahabbai da suka rage masu daraja daga cikinsu.
Hukuma a wurin ahlul-bati (a.s) ba wani abu ne ba sai wasila ce ta samun dammar zartar da hukuncin Allah da tsayar da adalci da yada shiriya, amma idan ta kasance sakamakon nemanta zai kai ga kashe mutane ne kawai don haka ne jagoran ahlul-bait (a.s) Imam Hasan (a.s) ya ga ya dace ya bar wannan lamarin domin maslahar da ta fi dacewa.
Sannan kuma al'ummar musulmi sun samu an cakuda musu ta yadda ba sa iya gane gaskiya da karya, sai ya kasance sun dauka domin mulki ne ake yin yaki, ga mabarnata sun ci galaba kan na gari sakamakon mutane suna son barna da son rai, domin karkatar da dukiyar kasa zuwa ga wasu tsuraru, da neman kin tsayar da adalci a zaman tare, da tattalin arziki, da siyasar al'umma da sauransu.
Gurbacewar al'umma ce ta sanya su ganin Imam Ali (a.s) a wannan zamani kamar wani mutum da ba shi da wayo, don haka ne suka ce Imam Ali mutum mai jarunta sai dai ba shi da wayo. Imam Ali (a.s) ya yi raddi mai kaushi a kan wadannan mutune da cewa: Wallahi Mu'awiya bai fi ni wayo ba, sai dai yaudara ce da fajirci yake yi, kuma ba don kin yaudara ba, da na kasance mafi iya yaudarar mutane. Sai dai dukkan yaudara fajirci ne, dukkan fajirci kafirci ne, dukkan mayaudari yana da tutar wuta da za a san shi da ita ranar kiyama.
Mutane sun kasance suna son san rai ne, don haka sai suka bi jagororin kabilunsu da makamantansu, sai suka dulmuyar da su domin neman abin duniya. Mu'awiya ya kasance ya sayi dukkan jagororin kabilu domin su bi duk abin da yake so, sannan ya sayi dukkan kwamandojin yaki mabiya son rai, da haka ne ya sayi hatta da wasu daga makusantan Imam Hasan (a.s) kamar Ubaidullah dan Abbas saboda kudi da suka kai dirhami miliyan daya.
Muna iya ganin misalign wannan lalacewa ta mutane da ta kai ga Imam Husain (a.s) ya aika Muslmi dan Akili Kufa amma sai dan Ziyad ya yi musu alkawarin dukiya da kudi da zai ba su, sai suka waste suka bar Muslim shi kadai!.
Misalin irin wadannan lamurran suna da yawa matuka a tarihin Imam Hasan (a.s) da Imam Husain (a.s) kuma muna iya ganin yadda hatta da matar Imam Hasan (a.s) ta kashe shi saboda kawai Mu'awiya ya yi mata alkawarin kudi masu yawa, da kuma auren dansa Yazid tsinanne.
Muna ganin Imam Ali (a.s) ya gaji da wannan al'ummar har sai dai ya yi mata addu'ar Allah ya raba shi da ita, ya raba su da shi. Yana mai cewa: Ya ubangiji na gaji da su, sun gaji da ni, ka hutar da ni su, ka hutar da su ni.
Muna ganin bayan mutuwar Imam Ali (a.s) yadda mutane suka zo wurin Imam Hasan (a.s) suka yi masa bai'a a kan shi ne halifan babansa kamar yadda babansa ya yi wasiyya, suka ce; kai ne wasiyyin babanka kuma halifansa, mu masu ji ne daga gareka, ka ba mu umarninka. 
Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: Kun yi karya, wallahi ba ku cika alkawari ga wanda ya fi ni ba, yaya kuwa zaku cika shi gareni!. Yaya kuwa zan samu nutsuwa da ku ban aminta da ku ba? Idan kuwa kun kasance masu gaskiya to alkawarinmu da ku shi ne wurin rundunar garin Mada'in, sai suka tafi can kuwa.
Shin Imam Hasan (a.s) wanda yake shi ma'asumi ne zai yi siyasar yaudara irin ta Mu'awiya ko kuwa irin ta babansa! Sai dai kowa ya sani cewa Imam Hasan (a.s) ba yadda za a yi ya yi siyasar mayaudara fajirai, don haka ne ba zai raba dukiya a tsakanin rundunarsa ba bisa son rai, wannan kuwa yana nufin su sake yaudararsa kamar yadda suka yaudari babansa (a.s).
Wannan lamarin ne ya tilasta shi barin jagoranci domin yanzu jagoranci ya koma wuri ne mai dauda maras tsafta, wuri ne mai kazanta da yanzu kuma ba wani abu ne da za a iya amfani da shi domin hidimar musulmi da musulunci ba.
Amma duk da haka Imam Hasan (a.s) ya yi kokarin ganin ya sanya Mu'awiya sharuddan yin hukunci da musulunci da dokokinsa domin ya bar masa jagorancin al'umma, sai dai mu'awiya bai yi aiki da ko daya daga cikinsu ba. Wadannnan dokokin da sharuddan sun hada da:
Mu'awiya ya yi hukunci da littafin Allah da sunnar manzonsa, da ta halifofi salihai.
Mu'awiya ba zai iya bayar da mulki ga wani ba ko ga dansa, domin zai koma ga Imam Hasan (a.s), sannan bayan Hasan (a.s) sai Imam Husain (a.s).
Mutane dukkansu amintattu ne a Iraki, da Sham, da Hijaz, da Yaman da sauran kasashe, ba shi da hakkin taba wani daga cikinsu.
Shi'ar Imam Ali (a.s) duk inda suke amintattu ne su da dukiyoyinsu, da matansu, da 'ya'yansu.
Kada ya sake ya yi wani makirci ga Hasan da Husain (a.s) ko ga wani daga alayen annabi (s.a.w) a boye ne ko a fili, kuma kada ya tsoratar da wani a ko'ina a bayan kasa.
Sai dai Mu'awiya wanda bai san addini ko tsoron Allah ba, a matsayinsa na jagoran munafunci bai yi amfani da ko daya daga ciki ba, domin ya kashe duk sahabban manzon Allah (s.a.w) da na Imam Ali (a.s) na gari da suka rage, haka nan ya kashe Hasan (a.s) jikan manzon Allah (s.a.w) da duk wani wanda ya samu damar kashewa daga wadanda ba su tsira daga makircinsa ba.
Imam Ali (a.s) ya yi wa Imam Hasan (a.s) tambayoyi na hikima wadanda suka shahara a cikinsu akwai kyawawan halaye kuma duk ya amsa su. Zamu kawo su ne a takaice kamar haka:
Ya amsa katari da cewa shi ne ture mummuna da kyakkyawa. daukaka kuwa ita ce kyautata wa jama'a, da dauke nauyinsu. Mutunci kuwa shi ne kame kai, da kuma gyara dukiya. kaskanci kuwa shi ne sauraron dan kankani, da hana dan kadan. Da sauran tambayoyi da ya amsa su.
Ya kasance yana zama da miskinai ya ci abincinsu, wata rana ya wuce su sai suka yi masa tayi, sai ya zauna ya ci abinci tare da su, sannan kuma sai ya tafi tare da su gidansa suka ci nasa abincin.
Imam Hasan (a.s) ya kasance shi ne wanda manzon Allah ya fi so matuka, ya kasance manzon Allah (s.a.w) yana salla shi kuwa yana yaro ya hau kansa manzon Allah (s.a.w) ya tsawaita sujada saboda kauna da girmamawa gareshi.
Imam Hasan (a.s) ya kasance jarumi ne matuka, kuma ya kasance daga wadanda suka fi kowa jarumta a yakokin da aka yi lokacin halifofi domin daukaka musulunci. Hatta da sulhun da ya yi da Mu'awiya bai so shi ba har sai da ya tabbatar da cewa Mu'awiya ya yi amfani da 'yan leken asirinsa da sauran munafukai domin su yada jita-jitar son sulhu da daina yaki, kuma da yawa daga mabiyansa sun samu ruduwa da wannan lamarin, don haka idan ma ya yi yaki jama'arsa zata kasu gidaje daban-daban ne, kuma da yawa wasu ma zasu ki yakin, wasu kuwa ma an riga an ba su kudi don kashe shi a cikin lokacin yakin.
Don haka maslaha shi ne ya yi sulhu domin jurewa mafi saukin wahala biyu da za a iya fuskanta, sai ya zami mummuna ya bar mafi muni, wato ya zabi yin sulhu duk da ya san cewa Mu'awiya ba ruwan shi da kiyaye sharuddan addini, maimakon ya yi yaki a kashe duk wadanda suka rage daga wadanda suka yi wa addinin musulunci hidima, hada da shi kansa Hasan (a.s) da dukkan sauran alayen manzon Allah (s.a.w).
Bayan dukkan wadannan lamurran ne Imam Hasan (a.s) ya zabi komawa Madina ya assasa makaranta yana yaye dalibai yana aika su garuruwa domin koyar da addini ingantacce da kakansa ya zo da shi ga wurin ubangiji madaukaki domin shiryar da talikai.
Da haka ne ya yaki jahiliyayyar da ake yadawa a Sham ga mutane da sunan addini, da wannan ne kuma zamu gane cewa yakin Imam Ali (a.s) da Mu'awiya yaki ne da ya fara tuntuni tsakanin gaskiyar Banu Hashim da karyar Banu Umayaya la'anannu.
Sai ya kasance ci gaban yaki ne tsakanin shiriya da bata, da gaskiya da karya, da gyara da barna; Abdusshams, da Harbu da Abusufyan, da Mu'awiya, da Yazid sun tsaya a bangaren barna da bata da karya, suka yaki Abdulmudallib, da Abu dalib, da Manzon Allah (s.a.w) da Ali da Hasan da Husain (a.s) wadanda suka tsaya a bangaren gyara da shiriya da gaskiya.
Imam Hasan Mujtaba (a.s), shi ne Hasan dan Ali dan Abu dalib (a.s) kuma babarsa Fadima Zahra 'yar Muhammad (s.a.w) jikan Manzon Allah (s.a.w) mafi girma kuma na biyu a halifofinsa kuma Imami jagora ga mutane bayan babansa (a.s).
An haife shi a Madina mai haske ranar talata a rabin watan Ramadan a shekara ta uku hijira, kuma ya yi shahad da guba da Mu'awiya dan Abu Sufyan ya yi masa kaidinta ta hannun matarsa Ja'ada 'yar ash'as wannan kuwa a ranar alhamis bakwai ga watan safar , shekara ta hamsin hijira, kuma dan'uwansa Imam Husain (a.s) shi ne ya yi masa wanka ya binne shi a Bakiyya a Madina inda kabarinsa yake yanzu wanda abin takaici wahabiyawa suka rushe kubbarsa.
Imam Hasan (a.s) ya rayu a karkashin Inuwar kakansa manzon Allah (s.a.w) kuma a cikin kulawar mahaifiyarsa Fadimatu Azzahra’u (a.s) shekaru bakwai. Kuma ya rayu tare da mahaifinsa (a.s) har ya zuwa rasuwarsa a shekara ta (40 bayan hijira). 
Kuma wannan lokacin wanda ya rayu a cikinsa tare da kakansa da mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya tara masa dukkan abubuwa na tarbiyyar Musulunci mai kaiwa ga gaci. Sai ya zamana ta samar da mutum musulmi Kamili mai tsarkin zuciya.
An ba shi halifanci bayan rasuwar mahaifinsa (a.s) a shekara ta (40 bayan hijra).
Kuma daga cikin muhimman ayyukan da ya yi a lokacin da ya karbi halifanci:
Tura mayakan mahaifinsa (a.s) wadanda ya riga ya tanade su domin yakar Mu’awiya dan Abu Sufyan saboda ya bijire wa umarnin Imam Ali (a.s) na cire shi da ya yi daga gwamnan Sham. Kuma ya kauce daga koyarwar Musulunci da hukunce-hukuncensa a cikin fagagen shugabancinsa a matsayinsa na gwamna a Sham…
Sai dai cewa wasu dalilai sun hana Imam Ali (a.s) kawar da Mu’awiya ta hanyar yin amfani da wadannan mayaka.
Muhimman wadannan dalilai su ne:
1. Ha’incin jagoran mayakan a sakamakon rudin da Mu’awiya ya yi masa na bayar da dukiya da kuma burace buracen samun abin duniya.
2. Rarrabuwar kan mayakan ta hanyar masu haifar da fitina daga cikin mutanen Mu’awiya.
3. Kasantuwar akwai khawarijawa a cikin mayakan, ta yadda suka yi amfani da wannan damar suka shiga rarraba kan mayakan da tarwatsa su.
Bayan rarrabuwar kan mayakan Imam Hasan (a.s) da watsewar su, sai yanayin siyasa a wancan lokacin ya saka Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu’awiya kuma ya koma zaman lafiya… Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu’awiya a bisa wasu sharudda, muhimmai daga cikinsu su ne:
1. Imam Hasan (a.s) zai ba wa Mu’awiya halifanci a bisa sharadin cewa Mu’awiya zai yi aiki da littafin Allah da kuma sunnar manzon Allah (s.a.w) da rayuwar halifofi salihai.
2. Halifanci zai koma hannun Imam Hasan bayan Mu’awiya idan Imam Hasan yana raye. Idan kuma ya rasu to zai bayar da halifanci ga dan'uwansa Imam Husain (a.s). Kuma bai halatta ba Mu’awiya ya yi wasicin halifancin ga wani.
Sai dai cewar Mu’awiya a lokacin da ya gama kame halifancin nan bai cika sharuddan ba sai ya yi ha’inci.
Muhimman abubuwan da suka jawo sulhun su ne:
1. kaskantar Irakawa a gurin mutanen Mu’awiya wadanda suke yakar su a lokacin Imam Hasan (a.s) domin su bar taimakon sa (a.s) a lokacin da yake kiran su zuwa ga mayar da martanin wannan dakarun na yaki.
2. Nisantar manyan mutane masu yawa daga Imam Hasan (a.s) daga cikin wadanda suka yi masa bai’a saboda kwadayin mukami da ganima. Hakan kuwa saboda lazimtar Imam Hasan (a.s) ga wadatuwa da kuma amana wajen bayar da aiki, da daidaitawa wajen rabon dukiyar haraji, domin aiki da adalcin Musulunci.
3. Shigar munafukai daga cikin masu leken asiri na Mu’awiya da ma’aikatansa cikin mutanen Imam Hasan (a.s) domin kawo rarrabuwa da batarwa.
4. kin fitowar da yawa daga cikin wadanda suka yi wa Imam Hasan (a.s) bai’a daga cikin Irakawa a kan yakar Mu’awiya, zuwa jihadi tare da shi (Imam Hasan) saboda yaudara.
5. Yada wasikun da Mu’awiya ya yi, wadanda suka zo masa daga gurin Irakawa, wasikun da suka kunshi biyayya ga Mu’awiya da yin ha'inci ga Imam Hasan (a.s) a tsakanin daidaikun mayakansa, domin raunana rundinar mayakansa da gwaurayata, da kuma cakuda ta.
Imam Hasan (a.s) ya rasu a Madina a shekara ta 50 bayan hijira.
Daga cikin shiryarwarsa:
1. Daga cikin wasiyyarsa (a.s) ga wani daga sahabbansa:
Ka yi aiki domin duniyarka kamar cewa zaka rayu ne har abada. Kuma ka yi aiki domin lahirarka kamar gobe zaka mutu. Kuma idan ka so daukaka ba tare da dangi ba, da kwarjini ba tare da mulki ba, to ka fita daga sabon Allah zuwa da'arsa (s.w.t), kuma idan wata bukata ta sanya ka abokantakar mutum, to ka abokanci wanda idan ka abokance shi zai haskaka ka.
2. Daga cikin wasiyyarsa ga wani daga 'ya'yansa:
Ya kai dana kada ka yi 'yan'uwantaka da wani har sai ka san dabi'unsa. Idan ka samu bayani mai kyau a game da dabi'un nasa kuma ka yarda da abokantakar,… to ka abokance shi a kan zaka yi masa uziri idan ya yi kuskure da kuma taya shi jin zafi da bakin ciki a lokacin da yake cikin tsanani.
3. Daga cikin wa'azozinsa (a.s) ga kowa da kowa:
Bayin Allah ku wa'azantu daga abubuwan da suka faru. Kuma ku dauki darasi daga ayyukan wadanda suka gabata. ku hanu daga ni'imomi, kuma ku amfana da nasihohi. Allah ya isa abin riko kuma mai taimako. kuma Kur’ani ya isa abin kafa hujja kuma abokin husuma. Sannan Aljannah ta isa lada. Kuma wuta ta isa azaba kuma ta isa makoma.


Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
+2348032156884 (telegram, whatsapp, biber, etc)
www.haidarcenter.org
Saturday, July 31, 2010
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: