bayyinaat

Published time: 05 ,April ,2017      16:05:21
Hakika murmushi da sakin fuska suna nuni ne ga kauna da kuma girmamawa, don haka ne suka zamanto hanyar jawo kaunar mutane ga mutum da kuma yada soyayya tsakanin mutane. Sakin fuskarka ga mutane da kuma fuskantarsu da maganganu masu dadi sukan bude zukatan mutane gare ka da kuma rufe kofofin kiyayya gare ka.
Lambar Labari: 80
Duk wanda yake so ya samu abokai kana su kuma su yi alaka da shi kamar yadda ya dace, dole ne ya makwabce su da kyau da kuma kyautata alaka da su. Daga cikin kyautata makwabtaka akwai cewa a duk lokacin da zai gana da mutane ya kasance mai sake musu fuska, mai murmushi yayin ganawa da kuma magana da su da dai sauransu, don kuwa hakan zai jawo kaunarsu gare shi. A daidai lokacin da fuska maras fara'a ta kan dada taimakawa wajen korar mutane daga gare ka, don haka dole ne mu guji turbune fuska yayin ganawa da mutane. 
Hakika murmushi da sakin fuska suna nuni ne ga kauna da kuma girmamawa, don haka ne suka zamanto hanyar jawo kaunar mutane ga mutum da kuma yada soyayya tsakanin mutane. Sakin fuskarka ga mutane da kuma fuskantarsu da maganganu masu dadi sukan bude zukatan mutane gare ka da kuma rufe kofofin kiyayya gare ka. Akwai wasu mutane da suke rayuwa cikin halin damuwa da kuma kumci, to amma a lokacin da ka yi mu'amala mai kyau da su da kuma sake musu fuska, za su sami sauki da kuma jin cewa ka damu da matsalar da suke ciki wacce suke neman mafita daga gare ta… 
Imam Sadik (a.s.) ya yi mana cikakken bayani kan wannan hali, inda yake cewa: 
"Murmushin mumini ga dan'uwansa mumini dabi'a ce mai kyau( ) ". 
Imam Muhammad Bakir (a.s) ma yana cewa: 
"Murmushi dabi'a ce mai kyau, sakin fuska yana jawo kauna da kuma kusanci ga Allah Madaukakin Sarki. Turbune fuska da kuma rashin murmushi kuwa yakan jawo kiyayya da kuma nesantar Ubangiji( ) ". 
Manzon Allah (s.a.w.a.) ma yana shiryar da mu yadda ake mu'amala da mutane don jawo hankalinsu da kuma samun nasara cikin mu'amala da su, inda yake cewa: 
"Lalle ba za ku iya samun kan (soyayyar) mutane da kudinku ba, ku dai ku yi mu'amala da su da sakin fuska da kuma murmushi(3) ". 
Don yada kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane da kuma yaduwar soyayya da farin ciki, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana kiran mutane zuwa ga sakin fuska da kuma kyautata alaka. Yana cewa: 
"Allah Ya yi rahama ga duk wani mai sakin fuska da kuma saukin hali( ) ". 
Sannan kuma daga cikin hanyoyin samun nasarar jawo hankalin mutane da kuma samun abokai da tabbatar kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane shi ne kyakkyawar magana. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mana irin gagarumar rawar da kyakkyawar maganar take takawa wajen kyautata alakokin mutane, inda yake cewa: "Kyakkyawar magana sadaka ce". 
Lalle kyakkyawar magana tana da nata tasiri mai girman gaske wajen samun nasara cikin mu'amala da mutane. Don kuwa a lokacin da abokinka ya ji kyakkyawar maganarka gare shi, zai nuna masa irin soyayyarka gare shi, ko kuma irin yadda kake son kyawun halayensa, ko kuma jinjinawarka ga irin kokarinsa da dai duk sauran kyawawan halayensa. A takaice dai wannan kyakkyawar magana takan bude kofar alakarka da abokinka da kuma jin girmamawa a tsakaninku, sai dai kuma yana da kyau mu kula kada mu wuce gona da iri wajen yabon mutane, don haka na iya sanya musu girman kai. Ko kuma wannan mutum mai kyakkyawan hali na iya canzawa zuwa ga mutum mai aiki don neman yarda da kuma yabon mutane ta hanyar wannan yabo da muke masa. 

Ziyarce-Ziyarce Tsakanin Abokai
Daga cikin halaye da dabi'un da suka zamanto al'ada ga mutum shi ne ziyarar dangi, abokai da kuma makwabta a gidaje ko kuma wajajen ayyukansu…. 
Ziyara takan nuna wa mutumin da ka kai masa ziyarar irin damuwa, soyayya da kuma girmama-warka gare shi. Hakika ziyarar aboki, musamman ma a lokutan bukukuwan farin ciki, ko kuma na bakin ciki, rashin lafiya, bayan dawowa daga tafiya mai tsawo, yana nuni da kasantuwanka cikin dukkan halin da yake ciki da kuma taya shi murna ko jaje kan abin da ya same shi, a bangare guda kuma yana nuni da irin sadaukarwarka gare shi. A duk lokacin da aboki ya fara kai ziyara zuwa ga abokinsa ko kuma ya mayar masa da ziyarar da ya kawo masa yana kara dankon zumuncin da ke tsakani ne…. 
Ziyara kuma takan gyara alakar da ta yi tsami tsakanin abokai…don kuwa tana nuni ne da neman afuwa kan wani abin da ya faru da kuma nuna cewa abin da da yake a cikin zuciya na rashin yarda yanzu fa babu shi… 
A wasu lokuta a kan sami abokai suna ziyartar juna ta hanya cin abinci a guri guda, to hakan ma yana da tasirin gaske don yana nuni ne da yarda da kuma girmamawar da ke tsakanin juna… 
Lalle Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya halicci mutum Yana son Ya ganshi yana da kyakkyawar alaka da sauran mutane, don haka shari'ar Musu-lunci ta kasance mai kwadaitar da musulmi kan kyautata 'yan'uwantaka, abokantaka da kuma ziyarce-ziyarce tsakanin 'yan'uwa da abokai… 
Sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana kiranmu zuwa ga ziyarar 'yan'uwa kana da kuma lada mai yawan gaske daga wajen Ubangiji. An ruwaito shi cikin wani hadisi yana cewa: 
"Babu wanda zai ziyarci dan'uwansa saboda Allah yana mai shaudin saduwa da shi, face Mala'ika ya kiraye shi daga baya cewa; ka sami babban rabo, sannan kuma Aljanna ta rabauta da kai( ) ". 
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa: 
"Hanyar sadarwa tsakanin 'yan'uwa a lokacin da ake gida ita ce ta hanyar ziyara, a yayin tafiya kuwa ta hanyar wasika( ) ". 
Imam Sadik (a.s.) din ya ruwaito cewa, Amirul Muminin (a.s.) yana cewa: "Ziyarar 'yan'uwa ganima ce babba, ko da kuwa ta yi kadan( ) ". 
Daga wadannan ruwayoyi da ma wasunsu, za mu fahimci muhimmancin da ke cikin ziyarce-ziyarce da kuma sadar da zumunta tsakanin 'yan'uwa da abokai. Duk da haka bari mu rufe wannan bayani namu da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) inda yake cewa; Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ziyara tana haifar da soyayya"; sannan kuma don kada ziyara ta rasa irin wannan muhimmanci nata, za mu ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana cewa ba ya kamata a sami lokaci mai tsawo tsakanin ziyara da wata ziyarar, sannan kuma kada ta kasance kullum, don kada a gaji da mutum. Annabi (s.a.w.a.) yana cewa: "Ka ba da lokaci tsakanin ziyara, sai soyayya ta karu". 

Mummunan Makwabci Ba Aboki Ba Ne
Mai yiwuwa ne mutum ma'abucin halayen kwarai ya kasance ya kulla alaka ta abota da mutanen banza ta haka sai ya bata mutumcinsa saboda alakarsa da su. Matasa nawa ne ma'abuta kyawawan halaye suka koma ga aikata munanan ayyuka (suka zama mutanen banza) saboda zama da kuma alaka da munanan abokai. Suka koma mutanen banza masu cutar da mutane, marasa kunya… 
Don haka abokin banza ba aboki ba ne; don kuwa abokinka shi ne wanda yake tare da kai cikin alheri da kuma jan ka zuwa gare shi ta hanyar wannan abota taku. Amma duk wanda zai cutar da kai da kuma jan ka zuwa ga bata, aikata laifuffuka da kuma lalata maka makoma, ko kuma ka koyi munanan dabi'u a wajensa, ba aboki ba ne, don haka ne ma Alkur'ani mai girma ya ambace shi a matsayin makiyi, inda yake cewa: 
"Masoya a yinin nan, sashensu zuwa ga sashe makiya ne, face masu takawa". (Surar Zukhruf, 43: 67) 
Sannan kuma Alkur'ani mai girma yana mana bayanin halin nadama da mutum ya kan shiga bayan ya yi nisa cikin aikata laifi da kuma kauce wa hanya saboda abokantaka da muggan abokai… sannan kuma da yadda wannan mutumin zai yi kwadayin da ma ace bai san wannan aboki nasa ba, da kuma cewa da ma ace nisan da ke tsakaninsa da shi ya kai nisan gabas da yamma. Allah Madaukakin Sarki Yana siffanta irin wannan hali na nadama cikin littafinSa, cewa: 
"Da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum". (Surar Zukhruf, 43: 38) 
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: 
"Misalin abokin kwarai da abokin banza, kamar mai rike da turaren miski ne da mai hura zuga-zugi, don mai rike da miski, imma dai ya ja ka ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka shaki kamshi daga gare shi. Amma mai hura zuga-zugi, imma dai ya kona maka tufafi, ko kuma ka shaki wari daga gare shi( ) ". 
Kididdigan da wasu cibiyoyin kula da muggan laifuffuka suka fitar suna nuni da cewa da yawa daga cikin samaruka da matasan da suke shaye-shayen muggan kwayoyi, sata, kisan kai da dai sauran laifuffuka, sun koyi hakan ne ta hanyar abokantaka da masu irin wadannan muggan halaye, daga karshe rayuwarsu takan kare a cikin gidajen yari da kuma kyama irin ta al'umma. Da a ce ba su sadu da irin wadannan muggan abokai ba, da ba su sami kansu cikin irin wannan bala'i ba, da sun ci gaba da zamansu a matsayin yaran kirki. 
Bincike ya nuna cewa kashi 42 cikin dari na yaran da suka fada cikin tarkon muggan laifuffuka da bata, sun bayyana cewa abokansu su ne suka batar da su da kuma sanya su akan wannan tafarki. 
Sannan kuma kididdigar da aka gudanar kan masu shan muggan kwayoyi tana nuni da cewa kashi 43 cikin dari na wadannan mutane suna shaye-shayen ne saboda abotarsu da wadanda suke shan muggan kwayoyin ne. 
Hakika duk wanda ya girmama mutumcinsa, kana kuma ya kiyaye matsayinsa a cikin al'umma ba zai taba abuta da muggan abokai ba. Hakan kuwa yana kiran matasa maza da mata ne wadanda suke son zaben abokai, da su lura sosai wajen zaben mutanen kirki ma'abuta mutumci. 

Kiyaye Sirri
Kowane mutum yana da sirrin da ya kebanta da shi, don haka dole ne ya kula da shi don kuwa shi wani sashi ne na mutumci da kuma rayuwarsa. Kada ya yada shi tsakanin mutane ya sa kansa cikin hatsari, watakila ma har da iyalansa… 
Mai yiwuwa ne mutum ya yarda da wasu mutane, ta haka sai ya gaya musu sirrorinsa da kuma wasu al'amurra da suka kebanta da shi kawai, wato ya sanya mutumci da kuma rayuwarsa a hannun wasu kenan….to a irin wannan hali ya zama wajibi ga su wadannan mutane da su kiyaye wannan sirrin. 
Kamar yadda masu iya magana suke cewa: magana zarar bunu, ko kuma cewa magana mallakarka ce, amma idan har ta fita daga gare ka, to ka zama mulkinta. 
A wasu lokuta mutum yana bukatuwa da ya yi shawara da wasu abokansa kan al'amurran da suka shafe shi shi kadai, don haka sai ya gaya musu don neman taimakonsu, ko kuma don ya tsoratar da su da ita. To a nan abin da ya hau kansu shi ne kiyaye wannan sirri don kuwa amana ce, saboda ya gaya musu ita ce don yardar da ya yi da su. To amma wasu mutane suna da dabi'ar yawan magana, ta yadda sukan gaya wa dukkan wani mutum da suka sadu da shi maganganun da ya shafe su, to lalle hakan yana da hatsarin gaske, dole ne a kiyaye shi. 
Wasu mutane kuwa suna da dabi'ar rike sirrin da ka gaya musu matukar dai alakarka da su tana nan da kyaunta, to amma a duk lokacin da suka sami sabani da kai, sai su bayyanar da wannan sirri naka. Ko kuma wasu mutane sukan canza daga yanayi mai kyau da aka sansu da shi zuwa mummunan yanayi, don haka sai su yi amfani da sirrinka da suka sani wajen cutar da kai da kuma tilasta maka biyan bukatun da suke so daga gare ka, idan kuwa ba haka ba sai su bayyanar da wannan sirri…. 
Daga cikin mutane kuma akwai wadanda ba sa iya rike sirri, kuma ba sa kiyaye wasa da mutumcin sauran mutane, daga lokacin da suka ji wata magana daga wajen abokinsu, Allah-Allah suke su gaya wa sauran mutane…. 
Da yawa daga cikin mutane sun fada tarkon yada sirrin mutane da kuma bayyanar da shi, inda mutumcinsu ya zube a idon jama'a ko kuma suka fada cikin wahala da wulakanci. Sirrin mutane, a wasu lokuta, yakan kasance ne cikin wani mummunan aiki da mutum ya aikata saboda jahilci da rashin saninsa…Allah Madaukakin Sarki Ya kan rufa wa bayinSa asirinsu, yafuwa da kuma gafarta wa masu neman gafara. Don haka a lokacin da mutum yake bayyanar da sirrinsa yana sa kansa da kuma mutumcinsa cikin hatsari ne, mai yiwuwa ma ya toshe hanyar tuba da kuma nesantar wannan muguwar dabi'a ce. Lalle hakan kuwa haramun ne, sannan kuma ha'inci da cutar da kai ne… 
Akwai hadisai da wasiyoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma Imamai (a.s.) da kuma ma'abuta hikima da suke kiranmu zuwa ga kula da sirrikan-mu. Ga kadan daga cikin irin wadannan wasiyoyi da kuma kalmomin hikima: 
"Sirrinka bawanka ne, idan har ka bayyanar da shi ka zama bawansa( )". 
"Bayyanar da sirri, halaka ce( )". 
"Kada ka gaya wa abokinka sirrrinka, sai dai abin da ko da makiyinka ya san shi ba zai cutar da kai ba, don mai yiwuwa ne wata rana abokinka ya zamanto makiyinka( )". 
Yana da kyau mu koyi darasi daga wadannan wasiyoyi da kuma hikima, don mu kula da harsu-nanmu daga yawan maganganu da kula da bayyanar da sirrorin da suka kebanta da mu. Sannan kuma kamar yadda muke son abokanmu su kiyaye mana sirrorinmu a duk lokutan da muka bayyana musu, haka mu ma ya zama wajibi mu kare da kuma kula da sirrori da kuma kura-kuransu. Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana shiryar da mu zuwa ga wannan kyakkyawar dabi'a, inda yake cewa: 
"Duk wanda ya rufa wa dan'uwansa musulmi sirrinsa a duniya bai bayyanar da shi ba, Allah Zai rufa masa nasa sirrin a ranar lahira". 
"Duk wanda ya rufa wa dan'uwansa musulmi sirrinsa a duniya bai bayyanar da shi ba, Allah Zai rufa masa nasa sirrin a ranar lahira". 
Kamar yadda muka sani ne akwai wasu abubuwan da suke fitowa daga mutum wadanda da a ce mutane za su sansu da sun zamanto masa abin kunya da tozartarwa; don haka ne Allah Madauka-kin Sarki Ya umurce mu da rufe sirrori da kuma kura-kuren mutane. Abin da kawai ya hau kanmu a nan shi ne nasiha da shiryar da su ba tare da mun bayyanar da su ga sauran mutane ba.

MU'ASSASAR AL-BALAGH
Wanda Ya Fassara:
MUHAMMAD AWWAL BAUCHI
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: