bayyinaat

Published time: 13 ,April ,2017      04:59:20
Risalatul Hukuk: Shi ne wannan littafin da yake gaban mai karatu, shi dai wani tari ne na bayanai daga koyarwar Imam Ali dan Husain (a.s) da yake kunshe da hakkokin dan Adam daban-daban.
Lambar Labari: 82
Ali Dan Husain Assajjad (a.s), sunansa da Nasabarsa: Aliyyu dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (a.s). Babarsa; ita ce Shahzinan ‘yar Yazdajir dan Shahribar dan Kisra, an ce sunanta Shahri Banu. Alkunyarsa: Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul-Husaini, Abul Kasim. Lakabobinsa: Zainul Abidin, Sayyidul-abidin, Assajjad, Zussafanat, Imamul Muminin, Almujtahid, Azzahid, Al’amin, Azzakiyyi. Haihuwarsa: 5 Sha’aban 38 H, a wata ruwaya 15 Jimada Akhir. Matansa: An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi, amma sauran duk Kuyangi ne. ‘Ya’yansa: 1-Imam Bakir (a.s) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum. Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi. Littattafansa: Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk. Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: Shekara 35. Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya da Yazidu dan Mu’awiya, da Mu’awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwan, da Walid dan Abdulmalik. Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik. Kabarinsa: Makabartar Bakiyya Madina.
A cikin tsawon lokacin imamancinsa ya ga rashin imani da kekashewar zuciya mai tsanani daga matsantawar da gwamnatin Umayyawa ta yi masa. Sun saka masa tsaro mai takurawa, kuma sun ajiye masa 'yan leken asiri domin kada ya ci gaba da harkar da’awar Musulunci wacce mahaifinsa Imam Husain (a.s) ya ciyar da ita gaba ta hanyar sadaukar da ransa da ya yi a ranar Karbala. Sai dai cewa gaba dayan abubuwan da suka aiwatar, da riga kafin Umayyawa a game da Imam Ali dan Husain (a.s) bai iya hana shi ci gaba da harkar da’awar musuluncin ba. Ya riga ya dauki wasiyyoyi da kira a matsayin wata hanya ta yada Musulunci da yakar Umayyawa. An tattara da yawa daga cikin addu’o'insa a cikin littafi guda daya aka kira shi da suna "Assahifa Assajjadiyya".
Assahifa Assajjadiyya: Shi littafi ne da ya kunshi addu’o'i guda 54 daga addu’o'in Imam Ali dan Husain (a.s), an tattara shi aka wallafa shi a zamanin Imam Ali dan Husain (a.s), kuma an rubuta shi guda biyu. Imam Muhammad al-Bakir ne ya ajiye guda daya wanda sauran imamai suka gaje shi, daya kuwa shi ne wanda Zaidu dan Aliyyu Zainul-abidin ya ajiye wurinsa, ‘ya’yansa suka gaje shi.
Assahifa yana da babban muhimmanci a wurin musulmai, sun kula da shi babbar kulawa, kuma ba zai gushe ba abin kulawa da muhimmanci. Muhimmancinsa yana bayyana a cikin abubuwa masu zuwa:
1. Saboda shi yana kunshe da addu’a ne, addu’a kuwa tana daga cikin mustahabbai mafi muhimmanci na Musulunci.
2. Daukar Littafin a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin harshen larabci da adabobinsa.
3. Daukar sa a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin Akidar Musulunci.
4. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin ilimin kyawawan halaye.
5. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin wasu Ilimomi 
Risalatul Hukuk: Shi ne wannan littafin da yake gaban mai karatu, shi dai wani tari ne na bayanai daga koyarwar Imam Ali dan Husain (a.s) da yake kunshe da hakkokin dan Adam daban-daban. Yana kunshe ne da hakkoki guda hamsin na koyarwar Musulunci da Imam Ali Sajjad dan Husain (a.s) ya yi bayani a kai. Ya hada da hakkin Allah (s.w.t), da na mutum a kansa, da iyali, da jama'a, da na daula.

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id
Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
Saturday, June 04, 2011

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: