bayyinaat

Published time: 26 ,April ,2017      06:31:33
"Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsu".
Lambar Labari: 89
 "Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsu".

Hakkin Gabobin Mutum
Hakkin Rai:"Amma hakkin ranka a kanka shi ne ka sanya ta cikin biyayya ga Allah, sai ka ba wa harshenka hakkinsa, ka ba wa jinka hakkinsa, ka ba wa ganinka hakkinsa, ka ba wa hannunka hakkinsa, ka ba wa kafarka hakkinta, ka ba wa cikinka hakkinsa, sai ka ba farjinka hakkinsa, kuma sannan sai ka nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan.
Hakkin Harshe: "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar maganar alfahasha -da batsa-, da saba masa alheri, da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mummuna mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali a matsayin jagora a kansa, da yin adon mai hankali a cikin hankalinsa da doruwa bisa kyakkyawar dabi’arsa a cikin harshensa, sannan babu dubara babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ji: "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi game da kada ka sanya shi wata hanya zuwa ga zuciyarka sai da wata magana mai kima da zata haifar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko ka samu wata kyakkyawar dabi'a, ka sani kofar magana zuwa ga zuciya tana kai wa ga haifar da ma'anoni kala-kala na abin da take kunsa na alheri ko sharri, kuma babu wani karfi sai da Allah".
Hakkin Gani:"Amma kuma hakkin gani shi ne ka rufe shi daga ganin abin da bai halatta ba, ka bar jefa shi (kana mai kallon ko'ina) sai wurin da yake abin lura ne, kana mai samun wata basira da shi, ko wani amfani na ilimi da shi, domin gani kofa ne na lura".
Hakkin Kafa: "Amma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, kuma kada ka sanya takunka a hanyar da mutanenta ake wulakanta su, su (kafafuwa) masu daukarka ne su dora ka hanyar addini, sauran kokari kuwa ya rage maka, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Hannu: "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka rike shi daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye shi da rike shi daga mafi yawan abin da bai halatta gareshi ba, da shimfida shi zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kansa ba, idan ya kasance ya hankalta, ya daukaka a wannan gida -duniya-, to lada kyakkyawa ya wajaba gareshi daga Allah a gidan gobe -lahira-".
Hakkin Ciki: "Kuma amma hakkin cikinka shi ne kada ka sanya shi salka -jaka- ga haram kadan ne ko mai yawa, kuma ka nufi halal da shi, kada ka fitar da shi daga haddin karfafa zuwa haddin wulakanci da zubar da mutunci, domin koshi mai kaiwa ne ga ma'abocinsa zuwa ga katon tumbi, mai sanya yin nawa da jinkiri, mai yankewa ne daga dukkan nagarta da karimci, kuma cika cikin da yake kai mai shi zuwa ga mayen koshi, mai sanya wulakanta kai da jahilci da zubar da mutunci ne".
Hakkin Farji: "Amma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga abin da bai halatta gareka ba, ka taimaka a kansa da rufe idanuwa, domin shi ne mafi taimakon abu, da kuma kiyaye shi da jin yunwa da kishirwa, da kuma yawaita ambaton mutuwa, da yin gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id
Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: