bayyinaat

Published time: 04 ,May ,2017      15:54:50
Ya zama dole ne ga wanda jagorancin al’umma ya san addini a dukkan kusurwowinsa, kuma ya zama masani da dokoki da cikakkiyar masaniyar tafsirin ayoyin Kur'ani da kewayewa cikakkiya ga sanin sunnar Annabi, da bayanin addini, da amsa tambayoyn mutane a kowani fage, da kuma kyakkyawan jagoranci.
Lambar Labari: 91
Halifan Annabi (s.a.w) wanda yake lamunce ci gaban rayuwar addini kuma mai amsa duk wata bukata ta dan Adam shi mutum ne mai daukaka wacce ta dace da matsayi madaukaki na jagoranci wanda yake da siffofi na musamman da suka hada da: 
1- Tsoron Allah da nisantar duk abin ki, kuma siffa ta isma ta zama masa jiki ta yadda ba zai iya aikata mafi karancin sabo ba.
2- Ilimi wanda ya karba daga Annabi (s.a.w) wanda kuma yake saduwa zuwa ga ilimin Allah, domin ya amsa duk wata bukata ta mutane a kowane janibi da fagen da ya shafi Duniya da lahira.
3- Siffantuwa da kyawawan siffofi da dabi’u kyawawa a mafi daukakar daraja.
4- Iya tafiyar da al’amuran al’umma da kyakkyawan shugabanci bisa asasin koyarwar addini.
Bisa la’akari da wadannan siffofi da muka kawo ga Imami, a fili yake cewa zabar irin wannan mutum ya fi karfin ilimin dan Adam kuma Ubangiji ne kawai saboda ilimi maras iyaka da yake da shi, zai iya zabar halifofin Annabi (s.a.w), don haka mafi muhimmancin siffofin Imami shi ne Allah ne zai zabe shi.
Don haka ne ma sakamakon muhimmancin wadannan siffofin ne ya sanya zamu kawo su a takaice, kuma mu yi bayanin kowanne daga cikinsu.

Ilimin Jagora (a.s)
Ya zama dole ne ga wanda jagorancin al’umma ya san addini a dukkan kusurwowinsa, kuma ya zama masani da dokoki da cikakkiyar masaniyar tafsirin ayoyin Kur'ani da kewayewa cikakkiya ga sanin sunnar Annabi, da bayanin addini, da amsa tambayoyn mutane a kowani fage, da kuma kyakkyawan jagoranci.
Irin wannan mutumin shi ne zai iya zama madoraga kuma makomar mutane kuma irin wannan ilimin ba a iya samunsa sai da wasidar saduwa da ilimin Allah (s.w.t), saboda haka ne ma Shi’a suke imani da cewa ilimin Imami kuma halifan Manzon Allah (s.a.w) dole ne ya zama ya karbe shi ne daga ilimin Allah maras iyaka.
Game da alamomin jagora kuwa, Imam Ali (a.s) yana cewa: Jagora shi ne mafi ilimin mutane, mafi saninsu da halal da haram din Allah, da kuma hakunce-hukunce daban-daban, da umarni da hani, da kuma duk abin da mutane suke bukata .

Kariyar Jagora Daga Sabo
Daga cikin siffofi mafi muhimmanci na Jagora kuma sharadi na asasi akwai isma, kuma ita ana samunta ne daga ilimi da hakikanin abubuwa da kuma irada mai karfi. Saboda Imami yana da wadannan abubuwa guda biyu ya zama yana kare kansa daga aikata sabo, haka nan Imami ma’asumi ne wajan bayanin addinin da kuma aiki da shi, da kuma bayyanar da abin da yake maslaha ko cutuwa ga al’umma. Kuma akwai dalilai na hankali da na karbowa daga Kur'ani da ruwayoyi game da ismar Imami (a.s) wanda mafi muhimmancin dalilai na hankali su ne: 
A- Kariya ga addini ta doru a kan ismar jagora ne; domin jagora yana da nauyin kare addini daga karkata a wuyansa kuma da shiryar da mutane, to zancensa dole ya zama abin karfafa daga ayyukansa don karfafawa ga ayyukan wasu a cikin al’amarin zamantakewar al’umma da kuma tasiri a kan haka. Don haka dole ne ya zama an kare shi a fahimtar addini da aiki domin ya iya shiryar da mutane shiriya ta gari.
B- Bukatar mutane zuwa ga jagora; mutane ba ma’asumai ba ne game da sanin addini da kuma aikata shi, don haka idan jagora shi ma haka yake to yaya za a yi mutane su dogara da shi idan ba shi da kariya daga kuskure. Kuma dole ne mutane su yi shakku game da biyayya garesu da kuma aiwatar da sakonsu da umarninsu idan ba su da isma.
Sannan akwai wasu ayoyi daga Kur'ani da suka karfafa game da wajabcin ismar jagora wacce daya daga cikinsu ta zo a surar bakara, wacce wannan aya ta zo ne bayan bayanin matsayin annabta, kuma Ubangiji ya bayar da wannan matsayi na jagoranci ga Ibrahim (a.s) bayan yana Annabi ne. A nan ne Ibrahim (a.s) ya nema daga Allah da ya bayar da wannan matsayi ga zuriyarsa. Sai Ubangiji ya ce: 
"Alkawarina ba ya samun azzaluamai” Kuma Kur'ani mai girma ya dauki shirka a matsayin zalunci mafi girma kuma duk wani sabawa umarnin Allah yana ganinsa a matsayin sabo ne, to duk wanda ya taba yin sabo a rayuwarsa yana daya daga ckin wadannan azzalumai, kuma bai cancanci matsayin jagoranci ba. Don haka babu makawa Ibrahim (a.s) bai roki jagoranci ga mutanen da tun farko suke sabo ba sannan suka tuba suka koma mutanen da suke aikata aikin alheri sannan sai suka kuma aikata sabo, don haka muna iya cewa mutane sun kasu biyu:

1. Masu sabo tun farkon rayuwarsu sannan sai suka tuba suka koma na gari.
2. Marasa sabo atafau ba su taba yin sabo ba.
Kuma a fili yake cewa ; Ubangiji madaukaki ya toge kashi na farko ne a maganarsa, don haka wadanda suka rage su ne kashi na biyu.
Mai Tafiyar Da Al’amuran Al’umma
Mutum yana rayuwa ne a cikin al’umma kuma al’umma tana da tasiri mai yawa a kan halayensa da dabi’unsa, don haka dole ya zama akwai zamantakewa ta al’umma mai dacewa domin gyara wannan tarbiyya tasa ingantacciya da kuma shiryar da shi zuwa ga Allah, kuma wannan ba zai yiwu ba sai karkashin hukumar Ubangiji. Saboda haka ne dole ne Imami ya zama yana iya tafiyar da al’umma, kuma ya yi amfani daga koyarwar Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) domin kafa hukumar musulunci.
Siffantuwa Da Kamala
Jagora shi ne shugaba a cikin al’umma don haka dole ne ya zama ya nisanci dukkan munanan dabi’u, kuma ya zama ya siffantu da dukkan kamala ta kyawawan dabi’u a mafi kamalar cika, domin ana ganinsa a matsayin mafi kamalar mutum ne. Imam Ridha (a.s) yana cewa: Jagora yana da alamomi da yawa: shi ne mafi ilimin… mafi tsoron Allah, mafi juriya, mafi jarumtaka, mafi kyauta, mafi ibadar mutane .
Sannan a matsayinsa na halifan Manzo kuma mai koyarwa da tarbiyyantar da mutane don haka ya zama dole ya riga kowa siffantuwa da umarnin Allah da kyawawan dabi’u. Imam Ali (a.s) yana cewa: Duk wanda ya tsaya matsayin jagoran mutane, dole ne ya fara da koyar da kansa kafin ya koyar da mutane, kuma ya tarbiyyatar da mutane ta hanyar dabi’unsa kafin tarbiyyatar da su da zancensa .
Allah Ne Mai Kafa Jagora
Jagora shi ne mai maye gurbin Annabi a zartar da umarnin Allah da kuma zabensa a mahangar Shi’a, kuma yana sanar da shi bayan Manzonsa. Don haka babu wani mutum ko wata jama’a da take da hannun wajan nada shi. Wajabcin zabin Imami daga Allah yana da dalilai masu yawa da suka hada da; 
A: Ubangiji shi ne mai hukumci a kan komai ba tare da wani kaidi ba, kuma dole ne kowane abin halitta ya yi biyayya gareshi. A fili yake wannan hukunci da jagoranci Ubangiji yana bayar da shi ga wanda ya so wanda ya dace ne, saboda haka kamar yadda Allah ne yake zabar Annabi haka nan shi ne yake zabar jagora.
B: Kamar yadda muka yi bayanin cewa dole ne Imami ya zama ma’asumi kuma mai ilimi, a fili yake cewa samun mai wannan siffofi mafi daukaka da saninsa, ba ya yiwuwa sai ta hanyar Allah masanin komai, kamar yadda Allah yake fada ga Ibrahim (a.s): "Ni mai sanya ka shugaba ga mutane ne” .
Cikakken Bayani Mai Kyau
Daga karshe yana da kyau mu kawo wani bangare na maganar Imam Ridha (a.s) game da Imami da siffofinsa:
Masu sabani game da al’amarin halifanci da suke rayawa cewa jagoranci al’amari ne na zabe bisa jahilci… shin mutane sun san matsayin shugabanci a tsakanin al’umma ne don ya zama ya dace a sanya hakkin zaben a hannunsu. Matsayin jagoranci yana da daraja, sha’aninsa yana da girma, matsayinsa madaukaki ne, wurinsa mafifici ne, zurfinsa ya fi karfin abin da mutane suke sawwalawa na cewar suna iya gano shi da hankulansu, ko kuma su san shi da ra’ayoyinsu…
jagoranci matasyi ne mai girma na Ubangiji bayan matsayin annabta da khulla wanda yake shi ne matsayi mai daraja na uku a samansu, wanda a mataki na sama na uku ne aka ba wa Ibrahim (a.s) shi, halifancin Allah na Manzon Allah ne kuma matsayi ne na Ali (a.s) kuma gadon Hasan da Husaini. Da gaskiya ne cewa imamanci jagoranci ne na addini kuma shi ne tsarin musulmi kuma gyaran Duniya da kuma izzar muminai… shi ne kamalar salla, da azumi da hajji da jihadi kuma ana kare iyakoki saboda Imami ne.
Jagora yana halatta halal din Allah ne, kuma yana haramta haram din Allah ne, kuma yana bibiyar dokokin Allah, kuma yana kare addinin Allah ne da hikima da wa’azi mai kyau, da dalili, yana mai kira zuwa ga tafarkin Allah. Jagora yana bullowa ne kamar rana, wanda haskensa yake mamaye Duniya, kuma shi yana sasanni ne da hannaye da gannai ba sa iya kaiwa zuwa gareshi. Imami wata ne mai haskakawa kuma fitila mai haske, haske mai walkiya, kuma tauraro mai shiryarwa a duhu mai tsanani a hanyoyi da watannni da duwatsu da kuma tekuna, kuma mai tseratarwa daga dukkan fitinu da jahilci…
Shi ne mai debe kewa, kuma uba mai tausayi, kuma dan’uwa na jiki, kuma uwa mai kyawawan dabi’u mai kyautatawa ga danta karami, kuma madogara ta bayi a yayin manyan musibu.
Imami shi ne wanda yake tsarkakke daga sabo da aibobi. Shi yana da ilimi kebantacce kuma masani mai hakuri… Imami shi kadai yake ba shi da misali, ba mai iya zuwa kusa da matsayinsa, babu wani masani da zai koma masa, kuma ba mai iya maye gurbinsa, haka nan ba shi misali, kuma ba a samun tamkarsa. Waye zai iya gano shi, sam! ba ya yiwuwa?! ya yi kadan! ya yi kadan! A nan ne hankula suka dakushe, tunanunnuka suka bace suka dimauce, a nan ne masu gani maras haske, da babba, da karami, da masu hikima masu dimuwa… da kuma masana magana, suka gajiya kuma suka kasa bayanin daya daga siffofin Imami ko fifikonsa, a nan ne suka yi furuci da gajiyawarsu da kasawarsu!!… 



Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@hotmail.com
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: