bayyinaat

Published time: 06 ,April ,2018      09:47:49
Bayani kan Ashura
Dukkanin Manyan Malamai magabata ba bu wanda ya saba akan cewar an kashe Imam Husaini dan Aliyyu dan Abu Dalib (dan Fadima ‘yar Manzo Allah) da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabin da na Husainin a ranar goma ga watan Muharram. Watan da Hausawa suke kira da watan CIKA-CIKI, kuma suka dauki ranar goma ga watan ranar cika-ciki. Har sukan ce duk wanda bai cika cikin sa ba Ubangiji zai cika masa da wuta Ranar Al-Kiyama.
Lambar Labari: 93

ASHURA
 
Bismillaahir-Rahmaanir-Rahiim. Allaahumma salli alaa Muhammad wa Aali Muhammad.
 
"Wanda idanunsa ya zubar da Hawaye a kan kisan Husaini, ko ya digar da digo daya saboda mu, Ubangiji Madaukakin Sarki zai sanya shi a Aljanna".

Malaman da suka fitar da wannan Hadisin:
1- Fadhaa'ilus-Sahaabah – Ahmad bn Hanbali: 2/675, Hadisi na 1154, ko wani bugun 3/132, Hadisi na 1118.
2- Wasiilatul-aamaal – Al-allaamah Baakathir Al-Hadhramiy, shafi na 60.
3- Rashfatus-Saadiy na Al-Allaamah As-sayyid Abubakar Al-Hadhramiy shafi na 47, wanda aka buga a Al-Kahira.
4- Da wasu litattafan masu yawa na Ahlus-Sunna.


Mecece ranar Ashura?
 
Ranar Ashura rana ce ta bakin ciki ga dukkanin Musulmi na gari, rana ce ta shiga kunci,  rana ce ta bacin rai, rana ce ta takaici. Rana ce ta tausayi da juyayi ga Iyalin fiyayyen halittu Manzon girma Annabi Muhammad (s.a.w), sakamakon irin gallazawar da aka yi musu na tsare su da aka yi a Dajin Allah babu Ruwa babu Abinci, wanda daga karshe aka yi musu kisan gilla.
 
Dukkanin Manyan Malamai magabata ba bu wanda ya saba akan cewar an kashe Imam Husaini dan Aliyyu dan Abu Dalib (dan Fadima ‘yar Manzo Allah) da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabin da na Husainin a ranar goma ga watan Muharram. Watan da Hausawa suke kira da watan CIKA-CIKI, kuma suka dauki ranar goma ga watan ranar cika-ciki. Har sukan ce duk wanda bai cika cikin sa ba Ubangiji zai cika masa da wuta Ranar Al-Kiyama.
 
Bayan dora Yazidu dan Mu'awiya dan Abu Sufyan a  kan Halifancin Musulmai, ya nemi Manyan Sahabban Annabin da su zo su yi masa "Mubaya'a" a kan sun yarda shi ne Shugaban Musulmin Duniya (wato shine zai ci gaba da bada Doka ta Addinin Musulunci ga dukkan Musulmai). Wasu don tsoron Kisa sun je sun yi Mubaya'ar, wasu kuwa ba su je ba, daga cikin wadanda suka ki yin Mubaya'ar akwai Imam Husaini (A.S), akwai Abdullahi dan Umar, akwai Abdullahi dan Abubakar da wasu daga cikin manyan sahabbai a garin Madina.

Lokacin da Yazidu ya matsa sai Imam Husaini (a.s) ya yi masa Mubaya'a, sai Imam Husain (A.S) ya ce masa: "Mutum kama ta (Dan Gidan Annabta) ba zai yiwu ya yi wa Fasiki kamar ka Mubaya'a" ba (wanda babban Malami Ibn Kathir yace: "abu ne sananne cewa; Yazidu ya yi fice wajen shan Giya, kade-kade, wake-wake, wasa da karnuka, wasa da Birai da sauran ayyukan sabo da kowa yasan shi dasu. Ya ci gaba da cewa; babu rana daya da Yazidu ya wayi gari ba a buge da Giya ba. Wanda sanadin mutuwar sa hawa ya yi kan Birinya yana tsalle da ita ta fado da shi ya karya kwankwaso. . . . . Hakanan Mu'awiya ya yi Hajji ya yi kokarin karbar Bai'a daga mutanen Makka da Madina, Abdullahi dan Umar ya ki yace: Baza muyi Mubaya'a ba ga wanda yake wasa da Birrai da Karnuka, kuma yake shan Giya yake bayyana Fasikanci, menene hujjar mu gurin Ubangiji? Ibn Zubair yace: "Ba bu biyayya ga abin Halitta a kan sabawa Mahalicci, bayan ya gama bata mana Addinin mu), wanda daga karshe Imam Husain ya yi hijira ya bar garin Madinah ta Kakansa ya nufi Makkah, yana cikin Dawafi sai ya lura da cewa Yazidu ya turo a kashe Shi, nan take ya fita daga cikin Haramin Allah don gudun kada a keta Hurumin Haramin a zubar da jini a cikin sa. Ya nufi Kufa wato Kasar Iraki shi da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabi (s.a.w) da Sahabban sa, inda Yazidu ya turo rundunar Yaki ta riske su cikin Sahara a kan lallai Imam Husain (A.S) ya mika wuya. A nan ma ya kuma maimaita kalmar sa: "Misli laa yubaya'a Misli Yazid", Mutum kamar ni ba zai yiwa irin Yazidu biyayya (Mubaya'a) ba.
Anan ne suka tsare su kusa da kogin Furat wanda Ubangiji yake cewa: "wa Huwallazii marajal-Bahraini haza azbun FURATUN wa haza milhun ujaj …." Har tsawon kwana ukun suka hana su shan wannan Ruwan Furat din, suka kasance babu Ci babu Sha har Yara suka fara mutuwa saboda Nonon iyayensu ya kafe. A kwana na goma ne Dakarun Yazid (L.T.A) suka farwa wannan tawaga ta Imam Husaini wacce bata wuce mutum 70 ba, wacce take dauke da Maza da Mata, Manya da Kananan Yara. A ciki akwai sayyidah Zainab 'Yar Fadimah (A.S) 'Yar Annabi Muhammad (S.A.W), akwai 'Yayan Imam Hasan (A.S) Dan Fadimah (A.S), akwai 'Yayan Imam Husaini din, Aliyyul-Akbar, Aliyyul-Asgar, haka nan akwai dan Imam Ali Abul-fadl Al-Abbas, da Sukaina wacce Karama ce, bayan kisan wadanda aka kashe, ta kasance tana yawaita Kuka tana kiran "Ina Babana?" sai Yazidu yake tambaya Kukan me take yi aka fada masa, shine ya sa aka kawo ta aka dauko kan Imam Husaini akan farantin Tasa. Yace Yarinya me kike cewa tace " Ina Babana?" Yace "kinga Baban naki" ya daga yankin da aka rufe Kan Imam Husaini da shi tana ganin sa nan take tayi wata kara bata sake ko shurawa ba ranta ya fita. Akwai Jariri Dan Imam Husain yana ta suma saboda tsananin Yunwa da Kishi ya dauke shi yaje yace su ma bashi ruwan da kansu kada su zaci shi ne yake son sha, nan take aka sami wani la'antacce ya harbi wannan Jariri da Kibiya.
 
Bayan sun kashe Imam Husain (A.S), sun yanke kansa sun yi sukuwa da Dawaki a kan Jikin sa mai tsarki, sun kone Hemomin da ragowar Mata suke da Yara, sannan suka bi suka kama ragowa suka sanya musu Sasari suka tisa su a kasa har wajen Yazidu. Wanda a ciki akwai Zainab 'Yar Fadimah (A.S).
 
An ruwaito daga littafin Musnad Ahmad (3/242, 27/97), da Mu’ujamul-kabiir na Dabaraniy (3/106, Hadith: 2813), da Tarikhu Ibn Asakir (14/197)da wasunsu, daga Anas dan Malik yace: "Mala’ikan da yake kula da ruwa ya nemi izini daga wajen Ubangjinsa yana son ya ziyarci Annabi (S.A.W), sai akayi masa izini, a ranar Manzo (S.A.W) yana dakin Ummu Salamah ne: sai Annabi (S.A.W) yace mata: ya Ummu Salamah ki tsaya a bakin kofa, kada ki bar kowa ya shigo mana: tana nan a bakin kofar sai ga Husaini bn Aliy (A.S) ya shigo. Sai ya bude kofar ya shiga, anan Annabi (S.A.W) ya rungume shi yana ta sumbatar sa, sai Mala’ikan ya ce: kana son sa? Ya ce e, sai yace: al’umarka ce za ta kashe shi,  kanaso na nuna maka gurin da za’a kashe shi? Sai Manzo yace na’am: sai ya danko danki daya na kasar gurin da za’a kashe shi ya nuna masa sai ga kasar ja, Ummu Salamah ta karba ta sanya ta cikin tufafin ta. Thabit ya ce: sai muka zamo muna cewa Karbala ce".

Haka nan cikin littafin tarihi na Ibn Asakir (14/190, 192), da wanin sa, daga Dawud, yace: "Ummu Salamah tace: Husaini ya shiga wajen Manzon Allah sai ya razana, Ummu Salamah tace: menene ya same ka ya Rasulallah? Sai yace: Jibrilu ne ya bani labarin cewa wannan Dan nawa za a kashe shi ne, Allah ya yi fushi mai tsanani da wadanda suka kashe shi".
 
 
FARKON  KUKA A KAN KISAN  HUSAINI (A.S) ANNABI MUHAMMAD (S) NE

Farkon wanda ya fara yin kuka da ranar Ashura tun kafin ma tazo shine Manzon Allah (S.A.W). An fitar cikin littafin Mustadrak alas-sahihaini da Tarikhu Ibn Asakir: Ummul-fadhli bintul-haarith ta ce: ……… yayin da na shiga gurin Manzon Allah (S.A.W) sai naga idanuwansa suna ta zubar da hawaye, sai nace: ya Annabin Allah Babana da Babata fansa a gareka me ya faru? Sai yace: Jibrilu (A.S) yazo mini ya bani labarin al’umata za ta kashe Dana wannan, sai nace wannan? Sai yace: "Na'am, kuma ya zo mini da kasa daga kasarsa Ja" (Mustadrak alas-sahiihain na Haakim: 11/135, Haakim yace: wannan Hadisin Ingantacce ne abisa sharadin Buhari da Muslim, amma basu fitar da shi ba).
1- Imam Aliy dan Abu Dalib baban Husainin shi ma ya yi kukan ranar Ashura tun kafin ta zo. An fitar cikin littafin Sawaa’ikul-muhrika: Imam Aliy ya bi ta Karbala a hanyar sa ta zuwa Siffin, sai ya tsaya ya kafa takobin sa a kasar gurin yake cewa: anan ne za’a kashe mazajen su, anan ne jinin su zai zuba, anan ne za’a kona hemomin su. A tare da shi akwai Malikul-ashtar da Ammar bn Yasir, sai Malik  yace: ya Shugabana su wanene? Sai Imam yace: sune dana Husaini. Sai mai littafin Sawa’ik yace: anan Imam Aliy ya yi kuka ya yi kuka har sai da kasar gurin ta jike da hawayen sa. (Sawaa3ikul-muhrikah ta Ibn Hajar Al-haithamiy: 2/566).

2- Sama da Kasa sun yi Kuka saboda kisan Husain (A.S). Al-Hafiz Abu Na'iim ya fada a cikin Dala'ilun-nubuwwah (3/211, ko a wani bugun 2/147): Daga Asbag bn Nabaatah ya ce: "Mun je wajen kabarin Husain tare da Aliyyu sai yace: a nan ne wajen ya da zangonsu, a nan ne za su kafa Hemominsu, a nan ne Jininsu zai kwaranya, Samari daga Alayen Muhammad (S) za a kashesu a wannan Dajin, Sama da Kasa za su yi musu Kuka".
 
An samu wasu kadan daga cikin Malamai suna cewa: ana yin murna tare da Azumi da cika-ciki ne a wannan rana ta goma ga Muharram, don a irin wannan rana ne Allah ya halicci Annabi Adam (A.S), a sannan ne ma Allah ya kubutar da Annabi Musa (A.S) daga Fir’auna, a dai irin wannan lokacin ne Allah ya fitar da Annabi Yusufa (A.S) daga kurkuku ko rijiya, da dai irin wadannan maganganu.
 
Idan ma mun dauka wadannan maganganu a kan kubutar wadannan Annabawa duk sun faru ne tabbas a ranar ta Ashura, to kamar yadda Hadisan baya da suka gabata suka tabbatar mana da cewa: tun kafin ranar Ashura (wato ranar da aka kashe Imam Husaini) ta zo Annabi (S.A.W) ya ke yiwa wannan ranar kuka, yana zubar da hawayen sa mai tsarki, yana takaici da bakin ciki da abin da zai faru. Tambaya ta anan ya kai Dan’uwa masoyin Annabi (S.A.W) shin da za a ce Manzon Allah ya kawo lokacin da aka yi wannan mummunan aiki na kisan gilla ga Iyalin Sa, a zaton ka Annabi (S.A.W) zai yi murna ne ko kuwa bakin ciki? Nasan dole amsar ka ita ce bakin ciki zai yi, don kuwa tun kafin ma abin ya faru yake zubar da hawaye yake bakin ciki, to ina ga ace ma yana duniyar?
 
Ka sani zuwan Annabi Muhammad (S) ya shafe dukkanin wani abu da wani Annabi yazo da shi a cikin tsarin shari'ar Musuluncin da Manzo (S.A.W) ya zo da shi, muna karbar dukkanin wani Hani ko Umarni, ko koyi daga Annabinmu ne Annabi Muahammad (S.A.W). Don haka abisa nassosin da suka gabata sun tabbatar da Annabi yana bakin ciki da wannan rana ne abisa haka dole ne muma mu taya Annabin mu bakin ciki da wannan bala’i da ya afkawa Iyalinsa, ko da kuwa an samu tarihi ya tabbatar da wadancan abubuwa na falala da suka faru a kan wasu Annabawan (A.S).
 

KADAN  DAGA CIKIN  FALALAR  IMAM  HASAN  DA  HUSAINI

Manzon Allah (S) yana cewa akan Su:
1- Sune mafifitan dukkanin al’umar duniya, idan aka cire Manzo, Aliyyu, Fadimah.
2- Sune shugabannin samarin gidan aljanna (domin daman babu tsofaffi a cikinta).
3- Suna daga cikin danginsa da basa rabuwa da Kur’ani har zuwa Alkiyama, al’uma ba zata bata ba idan tayi riko da su.
4- Sune wadanda Kakan su yace akan su: Taurari amana ne ga halittun da suke doron kasa kada su bata. Ahalin gida na kuwa amana ne ga halittun dake  kan doron kasa kada su rarraba (Bata).
5- Haka nan suna daga cikin Ahalul-baitin da hawa jirgin ruwan su kubuta ne, kin hawa kuma halaka ne. (ma’anar Hadisin anan shine Hasan da Husain suna daga cikin jikokin Annabi goma sha biyu da duk wanda ya bisu zai shiga Aljanna, wanda kuma duk bai bisu ba wutar Jahannama makomar sa, Allah ya kiyashe mu).
6- Sune Annabi . yake cewa: Ubangiji ka sani ina son su, don haka kaso su, kuma ina son duk mai son su.
 
Shin kana son Annabi da ‘yayan gidan sa kuwa?! Kana jin za ka ce kana son sune alhalin kana murna da ranar da aka yi wa jikokin Annabin kisan gilla?! Ko kuwa za ka ce kana son sune alhalin kana farin ciki da ranar da Annabi ya ke bakin ciki da ita?! Ko kuwa kana son sune alhalin kana cika cikin ka da abinci a ranar da ‘yayan Annabi suka kasance cikin yunwa da kishirwa?! Ko kuwa kai Annabin ka daban, ba Annabi Muhammad bane?!
 
Ka sani Musulunci ma bai yarda da Mutum ya cika cikin sa da abinci ko abin sha ba dam-dam. Allah Ta’ala yana cewa: "Ku ci ku sha kada kuyi barna hakika (Ubangiji) baya son masu barna” (A’araf:31). Anan wasu Malaman tafsiri sun nuna abin da wannan kalmar "barna” take nufi har da cika ciki dam-dam a koshi.
 
Ka sani cewa Imanin Mutum ba zai taba cika ba, muddin bai so abin da Manzon Allah (S) ya ke so ba. Hakan ne ya sa Malamai suka yi bayani a kan sharadan cikar  "SO” na gaskiya, su ne:
1- Son abin da masoyi ya ke so da yarda da abin da ya yarda da shi.
2- Kin abin da masoyi ya ki da dukkan abin da bai yarda da shi ba.
3- Son masoyan sa da kin duk wanda yake gaba da shi.
4- Jibintar lamarin duk wanda ya jibinci lamarinsa, da gaba da duk mai gaba da shi.
5- Ka tsaya tsaiwar daka wajen taimaka masa, tare da bin abin da ya aikata, wato shi ne tafiya akan abin da ya tafi akai.
 
Malamai suka ce duk wanda ya saba wadannan al’amura to karya yake a cikin soyayyar sa, sai mu gasgata fadin wani mawaki a kansa da yake cewa: "Lau kaana hubbuka saadikan la ada’tahu li’annal-muhibba lil-habiibi mudii’uhu” ma’ana: "Da son ka ya zamo gaskiya to da ka bi abin son naka, domin kuwa dukkanin abin da ake so ana yi masa biyayya ne”. Idan ka duba cikin littafin "Ajwibatul-mufiidah" za ka taras da wadannan sharadan na "so”. 

AZUMIN TASU'A DA ASHURA'

Malamai na gari sun karbo daga jikokin Ma’aiki (S.A.W) cewar; Mustahabbi ne a yi Azumi ranar tara ga watan Muharram (Tasu’a) don dandanar yunwa da kishirwa don kwaikwayon Jikokin Annabi da suka kasance cikin yunwa da kishirwa a wannan lokacin. Sannan a ranar goma ga watan (Ashura) ana kame baki ga barin ci da sha har zuwa bayan la’asar (domin zuwa bayan la'asar din ne wannan kishirwa da yunwa suka kare, suka taras da Liyafa daga Kakanninsu a Aljanna Madaukakiya).

Haka nan a wata ruwayar an so mutum ma ya Azumci gaba dayan watan, domin azumtar watan baki daya yana kiyaye mutum daga dukkanin munanan abubuwa.

Amma yin Azumi ranar Tasu'a da Ashura ta fuskar neman tabarruki HARAM ne

Allah ka samu daga cikin masoya Annabi (S.A.W) da Ahlul-baiti (A.S), masoya na hakika, ka kuma tashe mu tare da su. As-salaamu alal-Husain, Wa- alaa Aliyyib-nil-Husain, Wa-alaa Aulaadil-Husain, Wa-alaa  Ashabil-Husain, As- salaamu Alaikum wa- Rahmatullahi wa- Barakatuh.          Aliyu Abdullahi Yusuf
y.aliyuabdullahi@yahoo.com.
sWhat’a app +2348037493872


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: