Zuhudu (Gudun Duniya)
Da Sunnan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai
             
YA ALAKAR TSAKANIN ZUHUDU (GUDUN DUNIYA) DA KUMA WAYEWAR ZAMANI DA CI GABANSA TAKE!

Haqiqa sifar zuhuda da rayuwa sassauka mara tsada na daga cikin kammalar halaye na gari, kuma wanda ya komawa tushenmu na shari’a zai samu cewa ta bawa wannan sifa muhimmanci sosai kuma ta qarfafa kan yin riqo da ita. A lokacin da zuhudu ke zaburar wa kan rashin xanfara da duniya da qyale-qyalen cikinta, sai dai abin taqaici kwarai da gaske shi ne - wuce iyaka da rashin kai wa ga gaci - sun taka wara mai girma- a tsawao tarihi - kan fahimtar ma’anar zuhudu, haqiqa rashin koma wa zuwa rayuwar Manzo mafi girama (s.a.w) da rayuwar imamai (a.s) ya taka rawa wajen canja kamannin wannan siffa mai tsarki ta zuhudu da rayuwa sassauqa. Imam Kazim (a.s) yana cewa: yana mai yin nuni zuwa ga larurar zabin rayuwa matsakaiciya da kuma yin daidato bisa mahangar rayuwa da addini da kuma yanda ya kamata a rayu: 
"ba ya daga cikin mu, wanda ya bar duniyarsa don addininsa ko kuma ya bar diniyar sa don addininsa”
 Sannan da za mu yi duba zuwa ga addinani da sauran mazhabobi ba zamu sami wani addinan da ya zaburar da mabiyansa kan ci gaba da wayewa da neman sani da neman arziqi da yin sa’ayi da ya yi daidai da hankali kamar addnin musulunci ba. 
Haqiqa wannan lamari ne bayayyananne da yake da samuwa bayyananna a cikin karantarwar addini, don haka ne ma zamu ga musulunci a tsawon zamani yana kwaxaitar da mabiyansa kan ci gaba da wayewar zamani, kuma wannan wata siffa ce bayyananna kuma matashiya ce mai haske a cikin mahangar musulunci. Amma wannan ba ya nufin cewa, a yayin da musulunci ke kwaxaitarwa kan ci gaban zamani da kuma rashin tsayar da jirgin rayuwa da kuma iyakance ta bisa sunna da al’ada da bin tafarkin rayuwar magabata, wannan yana nufin musulunci yana kira zuwa ci gaban zamani irin na yammacin duniya mara kan gado na ko in kula ba!. 
 Sanna akwai wata matashiya da ya kamata a ba ta mihimmanci cewa: haqiqa ci gaban da Musulunci ke kira zuwa gare shi, shi ne ci gaban da ba zai mayar da Xan’adam bawa sha’awa da kwaxaice-kwaxaicen zuciya ba. irin ci gaban da musulunci ke so shi ne wanda zai sa mutun ya ‘yantu daga karkata zuwa ga bautawa sha’awa da soye-soye zuciya.
xxx   Musulunci ya muhimmantar da siffar gudun duniya (zuhudu) da yin rayuwa mara tsada mutuqa, kuma haqiqa karantarwa musulunci a fagen gudun duniya da kuma kin karkata zuwa qyale-qyalenta da kayan alatunta da kuma rashin miqa wuya ga sha’awa da narkewa a cikin karkata zuwa abubuwa na duniya, ta bada mataki na musamman a inda alqur’ani yake magana da manzo mafi girma da faxin sa.
{kada ka miqa idanunka (ka qwallafa rai) kan abin da muka jiyar da su daxi na daga mata da furanni (qyalqalin duniya) da mu jarrabce su da shi, alhali arziqin ubangijin ka shi ya fi alkhairi kuma ya fi wanzuwa}. 
  Daya daga cikin wayayyun masanan Musulunci yana cewa: "Haqiqa furannin duniya ba sa yi bada ‘ya’yan itaciya ga wani, domin duniyar xabi’a na da tsananin sanyi duk lokacin da waxannan furanni suka himmatu da su samar ‘ya’yan itaciya har su nina, sai busashshiyar iska ta kaxa ta faxo da ita daga kan reshe sai ta mayar da ita karmami iska na xaukarta tana wasu da shi yaddda take so”. 
  Na’am, haqiqa a tsawon tarihi ba mu gushe ba muna fuskantar tunane-tunane da ra’ayoyi da bayyanar fassarori mabanbanta bisa kalama Zuhudu da tsoron Allah bisa matakin xaixaiku da kuma gungun jama’a, abin baqin ciki waxannan fassarorin sun yi kai- kawo tsakanin wuce iyaka da rashin kai iyaka, kuma haqiqa wannan siffa ta addini an fahimce ta bisa kuskure kuma anfassara ayoyi da ruwayoyi ba daidai ba, kamar yadda aka yi ko oho da sunnna ma’asumai (a.s) da rayuwarsu a wannan fagen al’amarin da ya kai ga burkata da vata kamanin wannan siffa mai kyau ta zuhudu da sassauqar rayuwa, kai har sai da lamarin ya kai ga fassara wannan kalma ta gudun duniya da ma’anar komawa gefe da kaxaitaka da nisantar mutane da birni da cigaba da wayewa, aka fahimce ta da ma’anar yin kira zuwa yin bauta da addu’a dakaxaitaka da nisanta daga ayyukan rayuwa‼!
 Wanna shi ne farkon abin da ya ke zuwa tunani ka ama’anar kalmar zuhudu, dalilin sa kuma shi ne waxannna fassare- fassaren na kuskure da suka munana wannan siffa maxaukakiya dacce ba’a fahimce ta ba kamar yadda take a haqiqa, daga nan zamu ga Imam Sadiq (a.s) yana cewa: "Gudun duniya ba shi ne tozartar da dukiya ba, kuma baya nufin haramta halal ba, ballanata ma gudun duniya shi ne kada ka fi aminta da abin da ke hannunka fiye da abin da ke h annu ubangiji”  .
 Kuma an karvo daga shugaban muminai Ali  (a.s) yana cewa: "Baki xayan zuhudu yana ciikin kalmomi biyu, {domin kada ku yi bakin baqin cikin bisa abin da ya tsere muku kuma kada ku yi faranicika bisa abin da aka ba ku} . Kenan zuhudu da taqawa suna nufin rashin ratayu wa da abin duniya da adnta da qyale-qalenta da rashin xanfaruwa da abubuwa masu qarewa da abubun da ke duniya masu masu gushewa, da kuma kusantar sarkin na gaskiya tsaki ya tabbata a gare shi kuma ya buwaya, al’amarin da yake nufin sanya kai hutun zuciya da sa sauqaqa wa kai nauyi domin xan Adam ya filfila a sararin samniyar xaukaka mafificiya da tsakaka ta xanAdamtaka.
Idan ka san wannan sai mu yi tamabaya cewa: shin ci gaba da wayewa da ilimi da tarbiyya da anfana daga ni’imomin Allah domin rabautar xan Adam, ya ci karo da gudun duniya kuma suna hana mutum yin zuhudu? 
  Idan mka yi duba zuwa addinai da mazhabobi baki xaya ba za mu samu wani addini da ya bawa ilimi da sani mihimanci kamar addinin musulunci ba, kuma ya kwaxaitar kan newan ci gaba da wayewa da bunqasar hankali. 
 Ashe Manzo mafi gima (s.a.w) bai faxi ba yana mai cewa; " ku nemi ilimi ko da a kasar cana ne”  . Kamar yadda ya ce: "neman ilimi wajibi ne kan dukkanin musulmi”. 
Kuma an rawaito daga aminrul muninina (a.s) cewa; "ilimi rayuwar zuciya ne daga jahilci, kuma haske idanu ne daga duhu”  
Haqiqa wannan bayani ne na sarari a bayyane kan matsayin ilimi da matsayinsa a mahangar muhsulunci da kuma kaskancin duniya da ratayuwa da ita. 
Amma dangane da alaqa tsakanin addini da vi gaba ya kamata mu ce: abin la’akari a tsawon tarihin musulunci shi ne; haqiqa musulnci bai gushe ba kumaba zai gushe ba yana kira zuwa ci gaba da xaukaka da wayewar zamani, sai dai wannan ba yana nifin cewa musulunci yana kira zuwa wayewa da ma’anar da yammacin duniya ke nufi ba (modernization) ko (Modernus) saboda sakamako mummuna da wannan kalamar take nufi a wajen su wanda sakamakon bai yi daidai da koyarwar musulunci ba, ballatana, musulunci yana kira zuwa sabuntawa da ci gaba da wayewa, da ma’anar kar a tsayar jigin nan ko motar rayuwa kan al’adu daxaxxu waxanda ba su da madogara ta hankali ko shari’a da kuma rashin tafiya da zamani, haqiqa musulunci yana ciki zuwa tafiyar da rayuwa bisa ci gaba tare da kiyaye kyawawan halaye na musulunci da kyakkyawar kuyarwar nan ta imani da Allah, wannan wata matashiya ce mai haske a cikin mahangar musulunci.
Na’an akwai in da mahamgodin biyu suka haxu da juna, bisa misali, zamu iya yin nuni zuwa cewa: kwaxaitar wa zuwa ci gaba da mihimmantar da neman sani a mahangar musulunci al’amarin da yake xaya daga cikin abubuwan da tunanin yammacin ya xuro a kan sa da kuma irinsu cigaban zamin yammaci, kare haqqin xan’Adam, sa hankali a komai, kyakkyawan mu’amala da masu savanin ra’ayi, haka ma mabiya addinai mabanbanta, dukkanin waxannan xabi’u kyawawa waxanda suke daga cikin tushen ci gaban yammaci to akwai su a musulunci da bisa kyan yanayi da tsari a cikin koyarwa da mahangar musulunci, kuma yana daga cikin kyawawan xabi’un da yammacin duniya ya koya daga musulunci, lamarin ‘yancin tunani a fagen sanin addini da nisantar saurin yin yaqini a hukunce-Hukunce. 
Sai dai matashiyar da ke da matuqar muhimmanci ita ce: a yayin da musulunci yake kwaxaitarwa kan ci gaba da wayewa kaxai a bin yake so shi ne ya ‘yanta xan’Adam daga son rai da karkata zuwa so juciya kuma kada wannan ya sa ya zama bawan son rai da sha’awe-sha’awenta daga nan zamu ga shugaban Muminai Ali  (a.s) ya na ganin cewa: dun wani ilimi wanda hankali ba ya qarfafarsa to vata ne kuma kaucewa ne, a inda yake cewa: " Duk ilimin hankali baya karfafrsa vate ne” . kuma a lokacin da muka ga cewa musulunci na ganin cewa dukkan mutunin da kwanakinsa biyu (jiya da yau) din sa suka zama daidai ya yi asara, haqiqa yana hakaito wannan fahimtar da wannan hankaltar ta mihimmanci na qarshe wanda musulunci ya bawa ci gaba da wayewa da sabuntaka. 
Sannan haqiqa ruwayoyin da suka zo kan wannan lamari suna da yawa sosai zamu xan tsinci wasu daga ciki:
Imam Sadiq (a.s) yana cewa: "wanda ya san zamninsa ruxani ba ya kawo masa farmaki” .
An karbo daga sarkin Muminai Ali (a.s) yana cewa: ” haqqi ne a kan mai hankali ya jingina ra’ayin sa zuwa ra’ayin masu khankali, kuma haxe iliminsa da na masu hikima” .
An karbo daga gare shi (a.s) "gogayya ba ta qarewa kuma mai hankali na cikin samu kari (ilimi da sani) daga gare ta” .
An karvo daga Imam Kazim (a.s) yana cewa: " ba ya daga cikin mu wanda ya bar duniyar sa don addininsa, da addininsa don duniyarsa” .