ILLOLIN SHAN TABA SIGARI
Shan Taba Sigari wani abu ne da ya ke da hadarin gaske ga lafiyar dan Adam. Har kullum malaman lafiya su na tsawatarwa a kansa, amma duk da haka mutane su na ta'ammuli da ita, har ma Musulmi su na kafa hujja da cewa ai a addinance ba'a haramta ta ba kai tsaye. Na'am ita mahallin sabani ce tsakanin malaman Addini, amma ba mahallin sabani ba ce tsakanin malaman lafiya a kan cewa tana cutarwa, kuma hadari ce ga lafiyar dan Adam wadda har ta kan kai ga rasa Rai.

Marja'in Addini Ayatullahi Sheikh Jafar Subhani ya fada dangane da Annobar Corona cewa;
ان نصائح الأطباء لمكافحة الوباء حجة علينا نحن المراجع
Wato Nasihar Likitoci dangane da yaki da Annoba (Corona) hujja ne a kan mu, mu Maraja'ai.
Abinda zamu fahimta a nan shi ne hatta su kan su Maraja'ai su na sallamawa shawarwarin Likitoci a kan abinda ya zama Fannin su ne. Wato idan Likita ya bada shawara a kan abinda ya sani, wannan shawarar ta zama Hujja ga kowa da kowa.

A bisa wannan sai mu ce bisa dogaro da tsawatarwar da Likitoci su ke yi a kan shan Taba da bayyana hatsarin ta wanda ya hada da: Karancin Numfashi/Sarkewar sa (Shortness of Breath), Ciwon Kirji (Angina Pectoris), Fitsari da Jini ba tare da jin zafi ba (painless bloody urine), wanda ya zama alama ne na Kansar Jakar da ta ke ajje Fitsari (cancer of the bladder), wahala wajen hadiyar abu (difficulty in swallowing) ko canzawar sautin murya (persistent hoarseness) wanda ya kan zama Alama ne na Kansar Baki ko Makogwaro (cancer in the Mouth or Larynx), Bugun Zuciya (Heart Attack), yawan Tari (persistent cough) Ko Kaki da Jini (bloody sputum) da sauran su da yawa. Ya zama tilas a garemu mu nisance ta. Allah ya kare mu.