*WANNE IRIN ABINCI YA KAMATA KA CI.*
*فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللّهُ حَلالاً طَيِّبًا وَاشْكُرُواْ نِعْمَتَ اللّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ*.
A wannan ayar ta cikin Suratul Nahli, Allah (swt) yana umartar bawa da ya ci daga abinda shi Allah din ya azurta shi da shi na halal kuma mai kyau. Lallai musulmi ya sani cewa abincin da zai ci, ba kawai wanda zai gina masa jiki ta fuskacin nau'ikan abinciccikan da suke dauke da sinadaran; Carbohydrates, Proteins, Vitamins da Fats ba, a'a lallai ya lura ta daya gefen da nau'ikan abinciccikan da suke yiwa Ruhi tasiri na kaitsaye, wadanda zasu iya karfafa ko raunana bangaren ma'anawiy (Ruhi) din sa. Don haka lallai ne a cikin abincin ka, ka maida hankali ka sa lura a wadannan bangarora guda biyu.

*Na farko* ka ci abincin da ya dace wanda yake da dadi mai tsabta kuma kake sha'awa sannan ya kunshi wadancan nau'ikan abincin da muka ambata a sama. Wannan shi ne zai gina maka gangan jiki.

*Na biyu* wanda shi ne mafi muhimmanci shi ne wanda zai gina maka ruhi, wanda shi kuma ana bukatar ya zama na *Halal* kuma mai *Tsarki*. Da yawa zaka ga abinci a nazari na malaman lafiya da kuma zahirinsa mai kyau ne, amma a nazarin shari'a da kuma badininsa bai dace musulmi ya ci ba, misali abincin da aka saye shi da dukiyar haramun ko a ka hada shi da abinda ya ke na haram ko na dabbar da ba yanka ta akayi ba to bai halasta a matsayinka na musulmi ka ci ba komai dadinsa, kuma komai abinda ya kunsa na su protein da sauransu. Don haka ya kai musulmi mai sallamawa Allah cikin al'amuransa duk abincin da zaka ci ka tabbatar ya cika wadannan sharuddan;

*NA DAYA: YA ZAMA NA HALAL;*

A musulunci mafi muhimmancin abincin da bawa zai ci shi ne ya zama na halal. Idan aka ce abinci na halal ana nufin abincin da ya kunshi wadannan abubuwan guda hudu;
*(a)* Abinda shari'a ta baka daman ci irinsu nama na dabbobi da tsuntsayen da aka halasta da naman kifi (shi ma a mazhabin Ahlul bait akwai iya wadanda kawai aka halasta, sabanin Sunnah wanda su duk kifi halas ne a wajensu), don haka duk naman da aka ce haramun ne to lallai musulmi ya nisance shi, domin yana bata Ruhi.

*(b)* Halastaccen abincin can kuma ya zama da dukiya ta halas aka nemo shi, don haka abinci koda ya tsallake waccan rariyar ya zama halastacce a Shari'a to ya zama da dukiyar halas a ka nemo shi, kar dukiyar ta zama ta Sata,Gasbu,Riba ko Rashawa ce, ko dukiyar halas da aka cudanyata da haram.
*(c)* Koda abinci ya tsallake wadancan rariyoyin na sama to kuma ya zama ita dabbar yanka na shari'a akayi mata ba mutuwa ta yi ba, hakanan kifi (a mazhabin Ahlul bait shi ma dole ne ya zama an yanka shi, yankansa shi ne ya zama an kamo shi ne da ransa daga baya ya mutu, sabanin Ahlul sunnah su ko da matacce ne aka kamo to su suna ci, wannan kuma yana da hadari don ba'a san me ya kashe shi ba).
*(d)* Sannan abincin ya zama ba zai cutar da jiki ba, duk abinda zai cutar da jikin ka,wajibi ne ka nisance shi, ko da kuwa wasu zasu ci su kwana lafiya amma kai in ka ci zai cutar da lafiyar ka. Imam Sadiq (as) yana cewa:
*كل شىء تكون فيه المضرة على الإنسان فى بدنه فحرام أكله إلا فى حال الضرورة. (تحف العقول: ص 337، بحارالأنوار: ج 65 ص 151 ح 20)*
Wato duk abinda zai cutar da jikin dan Adam haramun ne cinsa, face a yanayi na larura.
Hadisai da dama sun zo suna tsoratarwa a bisa ta'ammuli da daya daga cikin ajujuwan abinci na haramun da muka lissafo guda hudu a sama. Manzo (saw) yana cewa
*" ان الله حرم الجنة أن يدخلها جسد غذى بحرام" (تنبيه الخواطر ج 1 ص 61)*.
A wani hadisin kuma Manzo (saw) yana cewa
*" العبادة مع أكل الحرام كالبناء على الرمل و قيل على الماء" (عدة الداعى: ص 141، بحار الأنوار ج 103 ص 16 ح 73)*
Ma'ana duk ibadar da aka yi ta tare da cin haramun kamar gini ne akan yashi ko aka ce kamar gini ne akan ruwa.
A ma'ana na wani hadisin wanda yazo a cikin littafin Mu'ujamul Ausad, mujalladi na 6 shafi na 311 hadisi mai lamba 6495, Manzo (saw) yana rantsuwa yana cewa ' Na rantse da wanda ran Muhammad yake hannunsa, lallai bawa idan ya jefa loma ta haramun a cikin cikinsa ba za'a karbi aikinsa ba tsawon kwana arba'in, kuma duk bawan da nama ya tsira a jikinsa da dukiyar haramun da Riba to wuta ce tafi dacewa da wannan jikin.

*NA BIYU:*

*YA ZAMA MAI TSARKI KUMA TSABTATACCE:*

Tsarki da Tsabtar Abinci, ba kawai larura ce ta kiwon lafiya ba, a'a suna ma da kyakkyawan tasiri ga Ruhi da Kwakwalwar dan Adam. Kamar yadda Najastacce kuma Kazantaccen Abinci yake mummunan tasiri ga Ruhi da Kwakwalwar dan Adam. Don haka ya zama dole ka kula da tsabta da kuma tsarkin duk abinda zaka saka a bakin ka.

A cikin Alqur'ani Allah mai girma da buwaya ya na hakaito tare da karfafa maganar As'habul Kahfi inda suke cewa;
*"....فابعثوا أحدكم بورقكم هذه إلى المدينة فلينظر أيها ازكى طعاما فلياتكم برزق منه..." (كهف: 19)*

Wato *"ku aika daya daga cikin ku da wannan Kwandalar taku zuwa cikin gari, ya duba ya samo mafi tsarkin Abinci ya zo muku da shi."*

A nan Allah Tabaraka wa Ta'ala yana hakaito mana maganar As'habul Kahfi ne a lokaci guda kuma yana karfafa maganar tasu tare da nuna mana cewa muyi koyi dasu, idan zamu nemi abincin da zamu saka a baka to mu tantance mafi tsarki da tsabta, ba kowanne irin abinci ne zamu ci ba, gudun kada ya gurbata mana tunani da kuma aiki.

As'habul Kahfi tattare da cewa sun farka daga dogon barcin da suka yi cikin matsanancin yunwa amma wannan bai hana su shardantawa dan aikensu ba cewa ba fa kowanne irin abinci zai nemo musu ba, a'a mafi tsarki. A yau mutane sun fi bada kokari wajen rufe abincin su don kariya daga abinda ya shafi Kudaje, Kura da sauran datti da kwayoyin cututtuka dake yawo kan iska, saboda kiwon lafiyar su, wannan yana da muhimmanci sosai domin zai bada kariya daga cututtukan zahiri, amma a lokaci guda kuma ya na da gayan muhimmanci kada mu takaitu ga wannan a'a mu bada muhimmancin gasken gaske wajen tsarkake abinci daga kazantar, Shubuha, Haramun, Riba, Algush da sauran hanyoyin tsarkake abinci daga kazantar da zata sabbaba gurbacewar Ruhi da Kwakwalwar mu, kamar fitar da Zakka, khumusi da sauran sadakoki. Allah (swt) a cikin Alqur'ani yana cewa *"ka karba daga dukiyoyin su sadaqa, ka tsarkake su da ita.."
A cikin Hadisi Manzo (swa) yana cewa;
*" كن كالنحلة إذا أكلت أكلت طيباً، و إذا وضعت وضعت طيباً"*
*(Gurarul Hikam hadisi na 7186)*
Wato *"Ka zama kamar Kudan Zuma idan zata ci tana cin mai tsarki idan zata zubar kuma sai ta zubar da mai tsarki"*
Wato kenan idan mutum ya ci abinci mai tsarki to za'a samu kyakkyawar natija daga gareshi, wato zai fitar da kyakkyawa kenan, ma'ana zai yi kyakkyawan tunani daga nan kuma ya fitar da kyakkyawan aiki, tsabtatacce, kamar yadda Kudan Zuma yake fitar da zuma tsarkakakkiya kuma daddada, sakamakon tsarkakakken abinda take ci. Kowa yana rububin abinda take zubarwa, haka idan ka ci tsabtatacce, tsarkakakke, za'a rinka rububin tunani da aikin da zai rinka fitowa daga gareka. Tunanin ka da aikin ka su zama masu amfanar al'umma da warkar musu da cututtukan dake damun su (na zahiri da na badini) kamar yadda zuma ke warkar da cututtuka.
A wata ruwaya yazo cewa; wani Mutum yazo wajan Manzon Allah (saw) ya tambaye shi yana mai cewa, Ina so a amsa mini addu'a ta, sai Manzo (saw) ya ce da shi *"Ka tsarkake abincin ka kuma kada ka shigar da Haram cikin cikin ka".* (Wasa'ilul shi'a muj 4 babun addu'a babi na 67 hadisi na 4). Ashe kenan cin abinci maras tsarki yana sabbaba rashin karbar addu'ar bawa, ya shiga matsaloli yayi ta rokon Allah amma Allah ya ki yaye masa.


NA UKU.

YA ZAMA DAGA AIKIN HANNUN KA.

Daya daga cikin abinda Musulmi suka kebanta da shi, kuma Addinin su ya kwadaitar da su a kan sa, shi ne rashin yin kasala wajan neman na kan su. A cikin ma'anar wani Hadisi Manzo (saw) ya hana musulmi wasu halaye daga cikin su akwai cewa kar ku yi Kasala (kar ku zama raggwaye ci ma zaune). Hakanan Manzo (saw) ya na cewa duk wanda ya dora bukatun sa a kan mutane, to zai zama mai bakin jini tsakankanin mutane, kuma abin kyama, mutane su ke gudun sa.

Haka nan Addinin mu ya nuna mana cewa kimar kowanne mutum ta na ga kokarin da yake yi wajan neman na kansa. Don haka Abincin da mutum ya samu ta hanyar gumin sa (komai rashin dadin sa) yafi daraja a wajan Allah fiye da wanda a ka jikan mutum a ka tausaya masa a ka bashi. A bisa wannan ne Manzo (saw) ya ke cewa;

"ما أكل العبد طعاماً أحب إلى الله تعالى من كد يده و من بات كالا من عمله بات مغفورا. (تاريخ دمشق ج 10 ح 1484)

Wato Bawa ba zai ci Abinci mafi soyuwa ga Allah ba, kamar wanda hannun sa ya tsuwurwurta, wanda ya kwana da gajiyar aikin hannun sa, ya kwana abin yiwa gafara.

A wata ruwayar ya zo cewa 'wata rana Hawariyyun (Sahabban Annabi Isah) sun bi shi ana tafiya sai suka ce, Ya Ruhin Allah wa ya fi mu? Idan mun so sai ka ciyar da mu, haka idan mun so sai ka shayar da mu, ga shi mun yi imani da kai, mun bi ka, sai Isah (as) ya ce da su, wanda ya fi ku shi ne wanda ya ke aiki da hannun sa ya ke ci daga gumin sa. (Mustadrak Alwasa'il muj. 13 shafi na 23 hadisi na 3).

Tirkashi! Kun ji fa aikin da kayi ka samu da gumin ka ka ci, to ka fi Sahabban Isah wanda a ke saukar wa da kabaki daga Sama. Saboda haka albarka dukkan albarka ta na cikin abinda gumin ka ya nemo maka.

NA HUDU.

YA ZAMA MAI DADI MAI KAMSHI.

Yana daga cikin kamala ta Mutum Musulmi, sifantuwa da kyau da kamshi, a cikin dukkanin al'amuran sa, hatta a abinda zai ci ko ya sha. Manzo Muhammad (saw) da iyalan gidan sa tsarkaka, ba kawai sun karfafa wasiyya ga Musulmi a kan sifantuwa da sifofi na Ilimi da kyawawan dabi'u ba, a'a har ma sun karfafi Musulmi da ya zama mai kyakkyawan shiga da kwalliya ta zahiri. Wannan kuwa ya hada da kamshin jiki da baki domin wannan zai kusanto da mutane zuwa gareshi, kuma ba zai shiga hakkin wasu ba, ya cutar da su. Don haka ne ma suka yi hani bisa cin duk abinda yake da mummunan wari abin kyama da gujewa ga jama'a, kuma bayan an ci a shiga cikin jama'a. Daga Abu Basirin daga Imam Sadiq (As) ya ce;

سئل عن أكل الثوم و البصل و الكراث فقال: "لا بأس باكله نيا و في القدور، و لا بأس بأن يتداوي بالثوم ولكن إذا أكل ذالك أحدكم فلا يخرج إلى المسجد." (الكافي ج ص 375 ح 2)

An tambayi Imam Sadiq (As) game da cin Tafarnuwa da Albasa sai ya ce ba komai da shi a ci a danye ko a romo kuma ba damuwa a iya yin magani da Tafarnuwa sai dai cewa idan aka ci to kar a fita zuwa masallaci.

Daga Amirul Muminin Ali (As) ya ce ;

"من أكل شيئا من المؤذيات بريحها فلا يقربن المسجد"

Wato wanda duk ya ci wani abu daga cikin masu cutarwa (da warin su) to kada ya kusanci Masallaci. A nan an ambaci Masallaci ne amma da nufin shiga cikin jama'a, saboda haka bai takaita ga Masallaci ba kawai. Kamar yadda su ma abinda aka hana a ci a shiga jama'a basu takaita ga wadanda a ka ambata a hadisin ba, a'a da duk ire-iren su, wadanda su ke sa baki ya rinka fitar da wari maras dadi abin kyama ga jama'a. Kuma cutar da jama'a na haifar da gurbatar Ruhi, ta inda mutum bai sani ba.

LOKUTAN CIN ABINCI.

Kamar yadda muka sani ne cewa komai a musulunci an yi bayanin sa a mafi kyawun yadda ya kamata ya kasance, wannan kuwa hatta lokuta mafi dacewa wajan cin Abinci.

A al'adar mafiya yawan Al'ummun Duniya, mutane su na cin Abinci sau uku ne a wuni. To sai dai a musulunce da kuma bincike na lafiya, sun tabbatar da cewa wannan al'adar ta na da nata matsaloli.

Cin Abinci sau uku a wuni yana zama matsala ga jikin dan Adam, domin kuwa (injinan) da ke cikin dan Adam masu markade Abinci domin amfanin sassan jiki, sukan rasa lokacin hutawa, yadda al'amarin ya ke kuwa shi ne, bayan cin Abincin karin kumallo, injinan zasu fara aikin markade, ba zasu kai ga kammalawa ba, sai a wurgo lomomin Abincin Rana, kafin su kammala harwalayau na Dare yazo sai kuma ya hau kan su, kafin wani lokaci gari ya waye an wurgo musu wasu saboda haka sai suyi tazarce. Ba shakka wannan al'amarin zai raunana wadannan (injinan), saboda rashin samun hutu, sannan a lokaci guda zai shafi tunanin mai wannan halayyar saboda alaka ta kai tsaye da ke tsakanin kwakwalwa da kowanne sashe na jikin dan Adam, a karshe mai wannan halayyar (ta cin Abinci sau uku) zai zama mai yawan kasalar jiki da tunani. Wannan dalilin ne yasa jikin dan Adam yafi lafiyar jiki da ta kwakwalwa a lokutan da ya ke Azumi, Kamar yadda hatta binciken lafiya ya tabbatar.

Bisa wannan dalilin ne yasa kasashen da ba na musulmi ba galiban suna bin wannan ka'idar, kuma mafi yawan wadanda suka yi abin a zo a gani a Duniya ta hanyar yin bincike na Ilimi da kirkire kirkire sawa'un musulmi ne ko ba musulmi ba za'a samu cewa sun jibinci wannan halayyar ne, wanda hakan ne ya basu damar yin zuzzurfan tunani.

LOKUTAN CIN ABINCI A MUSULUNCI..

Musulunci ya bayyana lokutan da ya kamata mutum ya ci Abinci a tsawon sa'o'i Ashirin da Hudu na Dare da Yini, Kamar yadda Hadisai na Ma'asumai (A.S) suka nuna.

(1) SAFE, (الغداء): Daya daga cikin lokuta mafi dacewa wajan cin Abinci, shi ne Safiya (Jijjifi), daga Annabi (S.A.W) ya na cewa;
"من أراد البقاء و لا بقاء فليباكر الغداء وليجود الحذاء"
(كتاب من لا يحضره الفقيه، ج 3 ص 555، ح 4902)
Ma'ana; Wanda ya ke son wanzuwa, babu wanzuwa (a duniya) to lallai ne ya rinka gaggauta karin kumallo, kuma ya kyautata takalmi.
Wannan Hadisin ya na bayyana tasirin gaggauta karin kumallo, wajan samun tsawon Rai da dadewa a Raye.

(2) DARE, (العشاء): Lokaci na biyu na cin Abinci shi ne farkon Dare. Imam Sadik (A.S) ya na cewa;
" اصل خراب البدن ترك العشاء"
(الكافي، ج 6 ص 288 ح 2
Ma'ana, tushen raunin jiki, shi ne rashin cin Abincin Dare.
Daya daga cikin Sahabban Imam Sadik (A.S) bisa dalilin matsalolin gurbacewar ciki da rashin narkewar Abinci (constipation) da ya ke fuskanta, ya kai kuka ga Imam (A.S), kuma ya nemi Imam (A.S) da ya bashi shawara, ya ke cewa:
"شكوت إلى أبي عبدالله ما ألقى من الأوجاع و التخم فقال لى: تغد و تعش ولا تأكل بينهما شيئا فإن فيه فساد البدن، أما سمعت الله عز و جل يقول: لهم رزقهم فيها بكرة و عشيا.
(المصدر السابق)
Ma'ana; Na kai kuka na zuwa ga Baban Abdullah na abinda ke damuna na ciwo da cushewar ciki sai ya ce; Ka yi karin kumallo kuma ka ci na Dare kar ka ci komai a tsakanin su domin a cikin sa (cin Abinci a tsakanin su) ya na haifar da raunin jiki, shin ba ka ji Allah mai girma da buwaya ya na cewa; Su na da Arzikin su (Abinci) a cikin ta (Aljanna) Safiya da Yammaci.

(3) LOKACIN JIN YUNWA: Daga cikin lokuta mafi muhimmanci na cin Abinci shi ne lokacin Jin Yunwa. An ruwaito daga Manzo (S.A.W) ya na cewa;
"انا قوم لا نأكل حتى نجوع و إذا أكلنا لا نشبع"
(مكاتيب الرسول (ص) ج 2 ص 436 ح 11)
Ma'ana, mu mutane ne da ba ma cin (Abinci) har sai mun ji Yunwa, kuma idan mun ci (Abinci) ba ma cika ciki.
Don haka Hadafin cin Abinci shi ne biyan bukata ta dabi'ar jiki da samar da karfi da kuzari, don kai wa ga Hadafi na Halitta.
Wannan bai kore lokuta biyu na cin Abinci da muka ambata a sama ba. Na'am ba laifi mutum a tsakanin wadancan lokutan guda biyu, in ya ji Yunwa ya dan yi ciye ciyen abubuwa marassa nauyi irin su, kayan marmari, biskit, kayan shaye shaye da ire iren su, wadanda zasu bashi kuzari, kuma a lokaci guda ba zai bawa injinan cikin sa aiki mai tsanani ba.
Zan ci gaba...