Wahabiyanci/Salafanci 3
Wahabiyawa na dauki da tunanunnuka da yawa da ya sa6awa sauran musulmi cikin abubuwa dabana – daban, ba kamar sauran musulmi ba kamar: 
Musamman cakudewar lazeem da malzoom.
Kamar "wilaya" da su ke ta kokarin maida ita kan ma'ana daya tal bayan tana da ma'anoni daban – daban ta mabambantan fuskoki, duk da cewa wasun su sun dage kanta ne don rushe ma'anar gahdir.
Kalmar kafirci.
Haramcin tawil.
Cakudewa cikin kalmomin da su ke daya wajan furuci (mushtarakatul lafziyya) kamar kalmar "wilaya".
Sun shahara da riki da hadisin a-haad hatta akida, alhalin al'ummar musulmai sun hadu kan cewa bai yiyuwa a yi riko da hadisin a-haad wajan kafa asasin akida, da wannan ne zamu ga sun bada fatawar Allah ya na da jiki, kuma dan saurayi ne marar gemu, sabida sanadin ruwayar ya inganta, da wadannan ruwayoyi ne su ke zubar da jinin mutane musulmi da wanda ba musulmi ba, kai hatta tsakanin ISIS da Jabhatun Nusra (Al'ka'ida ta Syria) da aka samu sa6ani aka dinga zubar da jinanen juna, kan kawai ruwayar da su ka fassara cewa, idan an yi bai'a ga na farko sai wani ya zo domin a yi masa bai'a ku kashe na biyu, wannan ruwaya ta jawo zubar da jini mai yawa tsakanin wadannan jama'a guda biyu ta wahabiyawa sabida ISIS na cewa shuban su al'Bagdadi bai bai'a ga Aimaniz Zawahir ba, wanda Jabhatun nusra (Al'ka'ida ta Syria) ke ganin cewa lallai an yi bai'a ga Usama bin Ladan bayan shi sai Aimaniz Zawahiri don haka a kan me wani (AL Bagdadi) zai zo yanzu kuwa wai a yi mishi bai'a? Sabida haka kawai a kashe na biyu (Al Bagdadi) hadisi daya a-haad ya haddasa yaki da zubar jinane masu yawa tsakanin wadannan 6angarorin wahabiyawa da salafawa, shi yasa hatta sa6anin fahimta kan iya jawo zubar da jini, babu yadda za a yi daya 6angaren yayi tunanin cewa ko shi ne bai fahimta ba, sa6anin fahimta a wajan su babbar matsala ce, zamu ga su na muhimmantar da sanadi, ana zuwa da ita kawai sanadin ta za a kalla ba bukatar sanin sandin ta kamar yadda ya kamata, ba kamar yadda zaka samu cewa Ahlulbait (AS) sun koyawa mabiyan su duba matani ba sanadi ba shiyasa kodaga wa sanadi ya zo misali a ce: "Shaidan ya ce Allah ya ce: "ba sandi zaka kalla ba sai ka dubi matani, kamar a ce: "Shadan ya ce: Allah ya ce a bauta masa shi kadai ba tare da abokin tarayya ba" ba zaka dubi sanadi ba ka ce: wannan ruwaya lalatacciya ce tunda shaidan ne ya kawo ta, saidai ka ce wannnan ruwaya ta yi daidai da kurani don haka mun kar6a, mun wurgar da shaidan.
A wajan wahabiyawa sunna na rushe kur'ani amman kur'ani baya rushe sunna, shi ya sa za mu ga fatawoyi na ban mamaki inda zaka ga an rushe ayoyi sabida ruwaya, wannan ya haifar wa da wahabiyawa babban bala'i.
Ba wahabiye na ganin cewar gaskiya na tare da da shi, don haka idan baka kar6i maganar sa ba kana kan 6ata, shi ne ya san abinda Allah ya ce, shi ne tunanin Manzo (SAW), yana ganin kamar yadda Manzo (SAW) ke tunani haka ya ke tunani, shi ne gaskiya, shi ne sharia, duk abinda ya gane to har wajan Allah haka abin ya ke ba wani kuskure, kuma duk wanda bai bi shi kan wannan ba 6atacce ne, zai iya kafirta sannan duk wani bala'i kan iya hawa kansa.
Rashin tawili wajan siffofin labari (sifatul khabariyya), inda ake cewa ( ), zai fassara maka cewa Allah ne da kansa ya zo, ko a ce () ba ruwan sa a nan kawai shi wajan sa Allah na da hannu, saidai su ce ba wanda ya san inda hannun ya ke.
Sun sa6awa sauran ahalis sunna a manhaj da matsayin su game da shia, duk ahlus sunna na duniya na ganin shia musulmi ne yan uwan su amman banda wahabiyawa.
Su na amfani da siyasa sosai a kasashe domin mamaye siyasar sannan siyasa na amfani da su duk da cewa ba su kadai bane amman sun fi kowa shahara kan haka, dayawa yan siyasa na amfani da su wajan cimma burin su sabida kungiyoyin su na zuwa a zuba musu kudi a siyasance.
Karancin sanin madogarar shia, da matsayin su kan litattafan su, da yawan su basu san cewa litattafai irin su Bihar, tafsirul kummi da wasu litattafan, litattafai ne da shia basa dogara da su.

Ibrahim Al-Mu'azzam