Gwagwarmayar Musulunci
Harkar Muslunci A Najeriya Ta Bukaci A Saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

Harkar muslunci a Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi ba tare da tuhumarsa da wani laifi ba.

A wani taron manema labarai da manyan mambobi na harkar muslunci suka gudanar jiya a Kadna, Farfesa Abdullahi Dan Ladi ya sheda wa manema labarai cewa, suna kira da babbar murya ga gwamnatin Najeriya da ta saki jagoran Harkar Muslunci Sheikh Ibrahim Zakzaky, domin nema masa magani kan matsalar idanunsa a inda ya dace, domin babu asibitin da za ta iya yi masa aikin da ake buka a Najeriya.

Farfesa Abdullahi Dan Ladi ya ce gwamnati ta tabbatar da cewa ba tana tsare da Sheikh Zakzaky bisa wani laifi da ya aikata ba ne, illa saboda tsaron lafiyarsa, ya ce idan haka ne to ya kamata a sake domin a nema masa magani domin samun lafiyar idanunsa da kuma hannunsa, wanda ya samu matsala sakamakon ahrbin da sojoji suka yi masa a gidansa.

Haka nan kuma Farfesa Dan ladi ya yi ishara da cewa yanzu mai dakinsa da suke tare a inda ake tsare da su a Abuja, akwai harsashin bindga guda a cikin kashin bayanta, wanda likitocin Najeriya sun tabbatar da cewa babu kayan aikin da za a iya fitar da harsashin a asibitocin Najeriya.