Dalilan Samuwar Allah


Bahasin Farko
1-Sannin Allah. 2-Tabbatar Da Samuwar Allah. 3-Dalilin Hankali. 4-Dalilin Shari’a (Nakaltowa).
Sanin Allah
Wajibi ne a kan baligi ya san Allah madaukaki, bai halatta ba ya bi wani a kan haka ba koda kuwa babansa ne, misali dole ya yarda Allah daya ne, ta yadda da babansa ko malaminsa zai ce Allah sabanin haka ne, to ba zai bi ba.
Wannan kuwa domin wajabci ne na hankali da ya lizimta gode wa mai ni’ima, ko kuma gujewar azabarsa idan an saba masa.
Kur’ani ya yi kakkausan suka ga masu bin iyayensu[1] a akida ba tare da sanya hankali ba. Don haka ne muna iya cewa; wajibi ne a yi nazari kan sanin jiga-jigan kusoshin addini ta hanyar hankali, sannan sai ya zama shari’a ta karfafi dalilin hankali, bai halatta ba a bi wani a cikinsu.
Kalmar "Allah” suna ne madaukaki na mahalicci da shi ne suna mafi girma. Allah yana da siffofi da ayyuka, wadannan siffofin nasa su ba irin na sauran samammu ba ne, domin shi siffofinsa azali ne wadanda suke tare da shi tun azal, amma sauran halittu siffofinsu suna bujuro musu ne.
Sai dai tun farko yana da kyau mu sani cewa sanin Allah madaukaki yana bukatar ayyana hanyar saninsa ga mai rubutu, domin wani yakan yi bayanin Sanin Ubangiji madaukaki ta hanyar Falsafa, wani kuma ta hanyar Irfani, da makamantansu. Amma mu a nan muna son yin wani gajeren bayani game da Allah madaukaki ta hanyar hankali da shara’a ne.
Da farko dai mu sani cewa Allah ya yi mana baiwar da babu wani mai rayuwar a doron kasa da ya same ta. Ya yi mana falalar da baiwar karfin tunani da kyautar hankali, don haka ne ma ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: "Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya ne”. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: "Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai ba”. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: "Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116.
Wannan ni’imar ta hankali ita ce ta wajabta mana yin bincike domin sanin Allah madaukaki, ta yadda muna iya cewa dokokin hankali suna tilasta mana hakan. Don haka ne abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali.
Kuma babban kuskure ne ga wani mutum ya ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane, ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa, ya san ubangijinsa[2].
Don haka a kanmu akwai nauyin wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba, kuma na farko shi ne ubangiji madaukaki. Wannan wajabcin saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi.
Sau da yawa marubuta sukan kawo sunayen Allah da siffofinsa kamar haka: Allah madaukaki daya ne makadaici, babu wani abu kamarsa, magabaci ne, bai gushe ba kuma ba ya gushewa. Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani, kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu tamka gare Shi, sannan ba a iya riskarsa da wasu mariskai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin jahilcin hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (a.s).
Mafi girman siffar da take fara zuwa a jerin sunayensa ita ce kadaitawa, domin ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, da samuwarsa, da siffofinsa da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan.
Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (s.w.t), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.
Wasu mutanen sun so su kore musulunci daga dukkan wanda yake ziyarar kaburbura, da tawassuli da waliyyan Allah, da da’awar cewa shirka ne. sai dai lamarin ba haka yake ba, domin ziyartar kaburbura da gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada. Wadannan ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa, da taimakon talaka.
Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (s.w.t) ko kuma shirka a bautarSa, haka nan sauran ayyukan ibada. Dukkan wadannan ayyukan ba komai ake nufi da su ba sai rayar da al’amuran Allah da waliyyansa, da sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su "Wannan, duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.
Daya daga cikin mafi girman lamari a bahasin sanin Allah madaukaki shi ne na siffofinsa tsarakaka; da farko dai ana kasa wadannan siffofi zuwa siffofi tabbatattu na kamala da (jamal) kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa.
Wasu sun dauka wadannan siffofin su daban ne, kuma kari ne kan samuwar zatin Allah, ta yadda su ma suna da tasu samuwar ta daban. Sai dai mu muna cewa wadannan siffofi ba kari suke ba a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.
Amma wadannan siffofin sun sassaba a ma’anoni, ba a hakikanin samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar Ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga Ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
Sannan akwai wasu siffofi masu nuna aikin ubangiji kamar[3] halittawa, arzutawa, gabatuwa, da kuma samarwa. Wadannan, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da ayyukansa ga bayinsa.
Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru; da aka fi saninsu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore nakasa[4] daga ubangiji ko duk wata tawaya kamar jiki, sura, fuska, motsi, da rashin motsi, nauyi, da rashin nauyi, da sauransu.
Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) ya yi nuni ga hakikanin siffofin Allah madaukaki yana mai cewa: Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[5], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[6].
Daya daga cikin siffar Allah da aka yi ta ja-inja a kanta ita ce Adalcin Allah, amma mu a takaice a nan zamu ce: Duk wani nau’in zalunci ya koru ga Allah, domin dukkan hanyoyi hudu da za a iya yin zalunci sun koru daga gareshi kamar haka:
1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa zalunci ba ne.
2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma kasa barin aikata shi.
3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma kasa barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya kasance ya yi zalunci ne kawai don sha’awa da wasa.
Dukkan wadannan siffofi sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sannan haka nan Allah ba ya tilasta wa bayi aikin da ba zasu iya yin sa ba, kamar yadda ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Babban nauyin da yake kan baligi shi ne wajabcin ya san Allah madaukaki, bai halatta ba ya bi wani a kan haka ba koda kuwa babansa ne, dole ya yarda Allah daya ne, ta yadda da babansa ko malaminsa zai ce Allah sabanin haka ne, to ba zai bi ba.
Tabbatar Da Samuwar Allah
Farkon abin da aka dora dalilan samuwar mahalicci a kansa shi ne dalilin sanin Allah ta hanyar kallon halittunsa. Da zamu yi la’akari da rana, da wata, da sama, da kasa, da koguna, da sauran halittu, da kuma tsarin da suke kunshe da shi, da mun san cewa akwai wanda ya tsara su a kan hakan.
Da mun kalli tsarin halitta da kuma hikimar da take tattare da su da zamu san cewa babu yadda zata kasance ita ta yi kanta ko kuma wanda yake shi ma yin sa aka yi[7], wanda yake kamarta, shi ya yi ta, don haka ne kenan dole ne ya kasance wannan ya gangaro ne daga samamme, mai kamala, da babu wani mai kama da shi a nau’in samuwarsa.
Domin da ya kasance kamarta ne, da ya bukaci mai samarwa, don haka dole a tuke zuwa ga mai samarwar da ba samar da shi aka yi ba, wanda yake shi ne ainihin samuwa.
Dalilan Hankali
Dalilin Hankali Kan Samuwar Ubangiji
Akwai dalilai na tabbatar da samuwar Allah da dama wadanda a nan zamu kawo wasu daga cikinsu, kamar Dalilin mai tsarawa da mai tsari, da dalilin mai samarwa da samamme da sauransu.
Dalilin Mai Tsari A kan Mai Tsarawa
Wannan dalilin yana cewa ne, duk sa’adda ka ga abu mai tarsi to hakika akwai wanda ya tsara shi, kamar mutum ya ga gida a tsakiyar daji da aka kayata shi, ko wata mota a jeje da aka yi mata wata kira ta musamman, ko kuma ya ga gidan wata tururuwa a sahara da tsarin bangaren ma’aikata da na masu tsaro da kuma sito da wajan uwargijiyarsu, hankali kubutacce a nan ba abinda zai yi hukunci da shi sai wajabcin samuwar mai tsarawa da ya tsara wadannan abubuwan kamar yadda ya so bisa tsari. Don haka muna iya cewa; duk mai tsari yana da mai tsarawa gareshi[8].
A Lura Cewa
Tsararre (mai tsari) ba ya iya ba wa kansa tsari, da yana ba wa kansa tsari da ya zabi wani abu daban ba yadda yake ba, misali da mutum shi yake tsara kansa da bai so ya tsufa ba, ko ya yi rauni ya takwarkwashe, kamar yadda da haka ne cewa yana iya tsara kansa ko tsara wa kansa al’amuransa na halittawa da samarwa da ya aikata abin da ya so ya ga dama, don haka samun sabanin haka yana nuna mai tsarawa daban tsararre (abu mai tsari) daban, amma mai tsarawa shi ne yake tsara tsararre (mai tsari) yadda ya so, don haka tsari yana kasancewa kamar yadda mai tsarawa yake so ne, ba kamar yadda abu mai tsari ya so ba.
Don haka hankali yana tabbatar da cewa kowane tsararre (mai tsari) ko kuma tsarin kansa to akwai mai tsara shi.
Dalilin Samamme A kan Mai Samarwa
Wannan dalilin yana nuna cewa; duk sadda aka sami samamme da samuwarsa ba daga gareshi take ba, to akwai mai samarwa da ya yi shi.
Don haka wadannan duwatsu da koramu da tuddai da shuke-shuke da sauran halittu da muke gani dole ne akwai mai samarwa da ya samar da su.
Idan ka ga sawun rakumi to lallai akwai rakumi[9], domin ba yadda za a yi a same shi sai da dalili, wannan dalilin kuwa shi ne samuwar rakumi. Don haka samuwar mutane tana nuna lallai akwai wanda ya yi su, domin samuwarsu ba ta gaza samuwar sawun rakumi ba a cancanta da kuma kasancewar tana da mai samarwa, musamman idan muka duba kima da girman kyawu, da kamala, da tsari, da suke tattare da dan Adam fiye da na sawun rakumi.
An tambayi wata mata mai saka tana cikin saka cewa; menene dalilin samuwar Allah? Sai ta dakatar da sakar[10] ta ce: Ku duba dalilina. Wato matukar na dakata, to zare da allura da itacen saka duk zasu dakata, domin ba mai motsa su, amma idan na cigaba to sai aiki ya cigaba domin akwai mai motsar da su.
Kamar yadda balaraben kauye ya tabbatar da samuwar Allah ta hanyar cewa kashin rakumi yana nuna mana cewa akwai rakumi.
Ana iya kuma gani a fili cewa dalilin wannan mata ya saba da dalilin da muke magana akai kamar yadda na balaraben kauye ya yi daidai da dalilinmu. Ita wannan mata dalilinta zai iya zama na uku, sai ya zama shi dalili ne na mai motsi a kan cewa akwai mai motsarwa.
Dalilin Mai Motsi A Kan Mai Motsarwa
Ya gabata cewa mun kawo misali da wannan mata kamar yadda kuke iya gani, sannan kuma muna da karin wani misali da yake kama da na mai samarwa da samamme, da kuma dalilin mai tsarwa da mai tsari, da kuma mai motsarwa da mai motsi.
Wani malami sun taba musu da shi da wani mai musun samuwar Allah (s.w.t), sai suka yi alkawarin haduwa a rana ta musamman da lokaci ayyananne, amma sai malamin ya yi lati, har shi zindike ya yi tsammanin ko malamin ya gudu ne ya ji tsoron tattaunawar da zasu yi.
Bayan nan sai ga malamin ya isa, sai mai musun samuwar Allah ya ce da shi: Don me ka yi lati.
Sai malamin ya ce: Kun san gidana yana waccan gabar kogi ne, na zo zan hau jirgina sai wata iska ta taso ta kakkarya mini jirgin ruwana ta daidaita shi. Ina tsaye na rasa yadda zan yi sai ga wani abin mamaki! Katakwayen nan suna haduwa har suka hada jirgi ya dawo kamar yadda yake, sai na hawo shi na zo domin mu tattauna. Sai mai musun samuwar Allah ya fara yin isgili da dariya ga malamin yana cewa da shi: Da na dauka kai mai ilimi ne, na so in tattauna da kai, amma yanzu karancin hankalinka ya bayyana gareni, a yanzu akwai mai hankalin da zai yarda da maganarka cewa wai kwale-kwale ya gyara kansa?!
Sai malamin ya ce ai kai ne kafi kowa wauta, domin babu hauka irin naka, idan kwale-kwale ba zai iya yin kansa ba, to yaya wannan duniya maras iyaka a fadi zata samar da kanta ba tare da wani mai halittawa, mai samarwa, mai motsarwa ba.
Abin lura
Allah madaukaki ba samamme ba ne da ma’anar wanda aka samar, shi samamme ne da ma’anar mai samuwa kuma mai samarwa da ba shi da wanda ya samar da shi, kamar yadda Allah ba tsararre ba ne domin shi ba mai tsari ba ne, shi mai tsarawa ne, domin duk abin da yake mai tsari to dole ne ya zama yana da gabobi ko yanke-yanke da suka hada shi suka bayar da tsari, don haka Allah madaukaki ya kubuta daga yanke-yanke. Kamar yadda Allah ba ya motsi, amma shi mai motsarwa ne, domin duk mai motsi yana samun canje-canje ne, kuma Allah ya kubuta daga samun canje-canje.
Dalilin Tukewar Salsala
Idan muka ce akwai wani mutum mai suna "D” da yake da mahaifi wanda yake shi ne "C”, shi kuma yana da uba sunansa "B”, wanda shi kuma "B” yana da baba mai suna "A”, shin ba zai yiwu a samu uba na asali da tushe da wannan salsala ta tuke zuwa gareshi ba da zai zama shi ne uba na farko da babu wani uba sama da shi ba, shin zai yiwu a hankalce a ce tafiya ta tafi ta yadda babu uba da suka faro daga gareshi tun farko. Sannan kuma tunda kowane uba ba shi ya samar da kansa ba, ashe hankali ba zai yi hukunci da cewa dole ne a samu wanda ya samar da uba na farko a wannan salsalar ba. (A yi tunani)
Wani misalin shi ne; Idan da za a samu ziro (sifiri) daya ko biyu, ko uku har zuwa dubu, ko miliyoyi shin muna ganin zasu iya ba mu adadi idan ba a samu wata lamba da zata haifar da adadin ba, kamar karshensu mu sanya lamba daya ko biyu.
Haka nan ma yake ga halittu da samar da su aka yi, wadanda samuwar ba daga garesu take ba, dole ne su samu wani wanda shi ne ya samar da su tun asali domin su sami samuwa, in ba haka ba, kamar yadda tarayyar sifirori ba zasu iya ba mu wani adadi ba, haka ma tarayyar halittu matukar babu asali da suka samu samuwa daga gareshi babu wata samuwa da zata kasance garesu. Don haka tunda mun ga samammu to dole ne akwai samamme da yake shi samuwa zatinsa ce, ba wanda ya ba shi ita, wanda shi ne ya samar da sauran halittu.
Dokokin lissafi da Mantik suna iya yin amfani a yayin da muka yi amfani da su a cikin abin da yake bayani game da samuwa a irin wannan fage, don haka a yi tunani kan wannan dalili.
Dalilin Kewayo (Gewayo)
Idan muka ce "A” baban "B” ne, shi kuma "B” baban "C” ne, amma kuma "C” wanda yake jika a wannan misalin shi ne ya haifi "A” kakansa, shin hankali zai taba yarda da hakan.
Wannan ne ya sanya ake cewa; ba yadda za a yi kewayo ya yiwu a al’amarin halitta, don haka ba zai yiwu ba wanda aka samar ya samar da wanda ya samar da shi, domin wannan yana kai wa ga kewayo cikin al’amarin samar da halitta ne, al’amarin da yake mustahili a cikin hankali.
Wannan dalili yana tabbatar mana da cewa, wannan samuwar da muke gani ba daga wanda aka samar take ba, wajibi ne ta kasance daga wanda shi mai samarwa ne, ba a samar da shi, domin matukar wani daga cikin su ne ya samar da shi to za a samu kewayo, wanda yake al’amari ne mustahili kamar yadda muka gani.
Dalilin Kididdiga
Shin akwai inda muka taba ganin samamme da ya zamanto ba mai samar da shi, shin akwai wanda ya taba ganin bisa haka nan kawai wani abu ya samu ba daga wani da ya samar da shi ba, da wani zai ce maka wuri ya yi kazanta amma ba wani abu da ya yi sanadin hakan ko kuma wasu masu bata wajan, ko kuma ya zama wani yana da cutar malariya amma ba tare da wani dalili ba shin hankula gaba daya zasu iya yarda da hakan.
Da wani zai ce ya taba ganin wata mota a daji, ko wani gida a cikin sahara, ko kuma mu ga wata takarda da rubutu a kai amma sai wani ya zo ya ce mana: motar nan da gidan nan da rubutun nan su suka samar da kawukansu, da menene hankalinmu zai yi hukunci da shi? Don haka ne wannan dalili namu na kididdiga yake cewa; tunda ba a taba samun wani abu a cikin samuwa da ba shi da dalili ba, to wannan ka’ida ta mamaye dukkan wani wanda samuwarsa daga wani take, don haka duk ababan halitta suna da mai samar da su da ya yi su wanda shi kuma shi ne karshe da ba wanda ya samar da shi, domin in ba a samu tukewa zuwa gareshi a matsayinsa na wanda ba ya bukatar mai samarwa ba domin shi ya samar da kansa, to zamu samu rashin tukewar salsala, wannan kuwa dalili ya gabata a kansa a binciken dalilin tukewar salsala
Dalilin Mai Tasirantuwa A kan Mai Tasirantarwa
Duk wani fararre da wanda ya farar da shi, wannan kuwa yana afkuwa ne sakamakon wajabcin alaka tsakanin mai samarwa da wanda aka samar, ko kuma mai tasirantarwa da mai tasirantuwa, amma mun samu wasu daga masana kamar su Dabid Hume da suka yi musun irin wannan mai tasirantarwa da mai tasirantuwa, suka tafi a kan cewa al’amarin yana faruwa ne bisa haduwa da dacewa ba a bisa wajabcin alakarsu ba ne.
Raddin da zan yi wa Dabid Hume shi ne; Koda mun yarda da cewa alaka tsakanin mai tasirantarwa da mai tasirantuwa tana kasancewa a bisa dacewa da haduwa ne ta yadda ba sa rabuwa har abada, to matukar har abada haka ne ta yadda ba sa sabawa a tsakaninsu, to wannan ba zai cutar da wannan dalili ba.
Don haka koda alakar wuta da kuna ta kasance bisa dacewa ne ta haduwa tsakanin samuwar wuta da kuna, matukar har abada haka ne wannan ba zai iya cutar da dalilinmu ba. Don haka sai ya zama bisa dacewa ta har abada ne da ba ta sabawa samuwar Allah (s.w.t) ta haifar da samuwar wadannan halittu gaba daya. A cikin musulmi akwai ash’arawa da Nicolas Malebranche daga masu tunani kuma malamin Falsafa a yammacin duniya da suke da tunani makamancin wannan na musun tasiri tsakanin mai tasirantarwa da mai tasirantuwa.
Ash’arawa daga cikin musulmi kuma da Nicolas Malebranche daga malaman yamma sun tafi a kan cewa; duk sa’adda aka samu alaka ta samuwa tsakanin abu biyu kamar wuta da zafi to wannan alakar ba ta hanyar tasirantarwa da tasirantuwa ba ne, domin sun yi musun alakar tasiri tsakanin ababan halitta, kamar ruwa da kashe kishirwa, ko wuta da zafi, suna ganin wuta ba ta zafi kamar yadda magani ba shi da waraka, suna masu imani da cewa abin da yake faruwa shi ne; duk sadda wuta ta samu sai Allah ya haifar da zafi tare da ita, haka ma duk sadda aka samu magani sai Allah ya sanya masa warkarwa, ba tare da wata rawa da wuta ko magani zasu taka ba, wannan kuma al’amari ne da rashin ingancinsa yake a fili.
Dalilin Godiya
Yawancin littattafai suna kawo wannan a matsayin dalilin da yakan tunkuda mu domin mu yi tunani game da samuwar Allah madaukaki, amma ni zan yi amfani da shi a matsayin kafa dalilin samuwar Allah kai tsaye;
Muna iya cewa; muna ganin ni’imomin halitta da suka babaye mu, ni’imar rana, da ni’imar dare da ba mu san iyakacin su ba, ni’imar iska, da ruwa, da lafiya, da tunani, da zafi, da sanyi, da shiriya, ta hankali da ta wahayi, da sauran ni’imomi da ba zasu kirgu ba.
A yanzu wadannan ni’imomi ba zasu sanya mu tabbacin cewa akwai wanda yake kwararo su zuwa garemu ba, ashe idan ba mu yarda da cewa akwai mai kwararo wadannan ni’imomi ba kare da idan ya ga kasusuwa sun fado daga sama, da ya tabbatar da cewa ba yadda za a yi kasusuwa su jefo kansu yakan waiwaya domin ganin waye ya jeho su domin ya gode masa, ba zai fi mu hankali ba kenan.
Kuma shin kare da ake ba shi kasusuwa amma ya kwana yana gadi domin gode ni’imomin wadannan kasusuwa da ake ba shi yana lashewa ya dangana da su, ba zai fi mu tunani da hankali ba a matsayinmu na mutane idan ba mu gode ba.
Dalilin Hattara
Wannan dalilin ana amfani da shi kamar yadda ake amfani da na samansa, amma na yi amfani da shi kai tsaye a matsayin dalili maimakon abin da zai sanya mu mu shiga bincike da neman dalili kamar yadda na yi amfani da na samansa ta hakan, ta hanyar cewa;
Da yawa muna ganin halaka da tabewa da mummunar makoma tana samun masu kin Allah da saba masa tun a nan duniya, kuma muna ganin darasin da yake samun rayuwarsu da makomarsu mummuna, ashe kenan wannan yana iya sanya mu, mu san cewa da akwai mahallici mai daukar fansa da ukuba ga masu kinsa da keta huruminsa, wannan dalili duk da an dauke shi daga daukar darasin abin da yake wakana amma zai iya zama mai karfafawa kamar yadda mai biyo masa yake.
Idan ya kasance muna ganin darasi kamar mu ga gawar bayin Allah da suka yi shahada a tafarkinsa ta yi shekaru dubu amma har yanzu jini yana zuba, kuma mu ga makiyansa cikin minti daya tana zubar da tsutsa, shin wannan ba ya iya zama mana tabbacin akwai Allah da ya dauki nauyin yin hakan, domin jiki ba shi da bambanci da jiki idan haka ne.
Don haka idan muna ganin mai bayar da labarin cewa akwai ‘yan fashi a hanya yana sanya mu kin bin wannan hanyar, shin ba zai zama wauta ba muna ganin irin wadannan darussa sannan sai mu rufe idonmu mu ki yarda da samuwar mahalicci mai iko da ya dauki nauyin wadannan ayyukan.
Hada da cewa muna ganin mutanen da suka fi mu hankali da tunani na daga annabawa (a.s) da wasiyyansu (a.s) duk ba wanda ya saba a cikinsu a kan maganar cewa akwai mahalicci.
Dalilin Gamsarwa
A nan muna son cewa ne a yi imani da mahalicci da aiki da hakan koda an kaddara da cewar babu shi ya fi zama abin hankalta a kan rashin yarda da hakan, domin idan an koma masa; idan an kaddara babu shi to da mu da wadanda ba su yi imani da shi ba mun zama daya, kuma wahalar da muka sha wajan bautarsa ba zata cutar da mu ba, amma idan akwai shi fa! kenan mun tsira su kuma sun halaka, kuma Imam Sadik (a.s) ya kawo wannan dalili ga Addisani.
William James daya daga cikin jigan-jigan Pragmatism da ire-irensa suna ganin wannan dalili a matsayin abin da zai taimaka mana wajan tabbatar da cewa lallai addini wani abu ne da a hankalce yana da kyau a bi shi, amma a sani kallon Willian da kallonmu game da wannan dalili ya saba, domin su suna ganin wannan zai sa a ga mai addini akalla ba yana hauka ba ne, wato riko da addini da ya yi abu ne da hankali zai iya karbarsa, amma mu muna ganin cewa addini wani abu ne da ya zama tilas a yi riko da shi domin mahallici a wajanmu samamme ne, dalilin a wajenmu domin karin gamsar da wanda bai yi imani da Allah ba ne, da kuma karfafawa ga dalilanmu a kan waninmu, ba kamar yadda su wadancan ‘Yan maslahar hankaltuwar riko da addini suka tafi a kai ba ne.
Dalilin Shari’a
Dalilin Shari’a Na Tabbatar Da Samuwar Allah
Wannan dalilin yana zuwa bayan an tabbatar da samuwar Allah ta hanyar hankali ne, ayoyin kur’ani masu yawa sun zo game da tabbatar da samuwar Allah madaukaki, kamar yadda ruwayoyi masu yawa suka zo daga hadisan Manzon Allah da Ahlul Bait (a.s) game da hakan.
Samuwar Allah a cikin kur’ani mai girma wani abu ne wanda kur’ani ya dauke shi a matsayin bayyananne da hankli kubutacce ingantacce ba ya musun sa, shi ya sa a wurare da dama ya yi nuni da hakan, a wasu wurare kuma yakan zo da sigar tamabya ne, kamar fadinsa madaukaki: "Shin akwai kokwanton samuwar Allah”[11]? Da sauran ayoyi masu yawa da suka zo game da bayanin tauhidi, don haka ya fi karfafawa kan tauhidin kadaita shi da ibada, ko ya yi nuni yana mai karfafa a kan kadaita shi cikin tafiyar da al’amuran bayi, ko kadaita shi ta hanyar kore masa abokin tarayya. Abin da surar Fatiha ta kunsa babban misali game da hakan, don haka sai mai karatu ya koma zuwa ga tafsirinta.
Daga cikin dalilai da kur’ani ya kafa a kan samuwar Allah akwai aya da ta kunshi dalilin samamme a kan mai samarwa, da dalilin mai tsari a kan mai tsarawa da fadinsa madaukaki:
"Hakika a cikin halittar sammai da kasa, da sabawar dare da rana, da jirage da suke gudana a kogi (dauke) da abin da yake amfanar mutane, da abin da Allah ya saukar daga sama na daga ruwa sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikinta daga dukkan dabbobi, da juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa, hakika akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali”[12].

Hafiz Muhammad Sa’id
www.haidarcenter.com
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@yahoo.com – hfazah@hotmail.com

13 Rabi’ul awwal 1427
23 Parbardin 1385
12 Afrilu 2006
[1] Bakara: 170.
[2] – Wato abubuwan da suke wajibi ne kowane mutum ya san su.
[3] – Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alaka tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.
[4] – Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.
[5] – Wato siffofn kari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dadu ga zatin Allah kuma zatin yana bukatarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu, da kuma Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah, da idonsa, da fuskarsa, da suke da tawili da ma’anar da laraba suka sani alokacin saukra da littafin kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da karfi ko iko ko alkawarin Allah, kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a kur’ani mai girma.
[6] – Alhalin Allah yana ko’ina bai kebanta da wani wuri ba.
[7] Hakkul yakin: 1.
[8] Aka’idul hakka: 36.
[9] A: Risalatul Muslim fi biladil garb, 39. B: Aka’idul hakka: 1/184.
[10] Abin da ya gabata, A: 40. B: 42.
[11]
[12] – Bakara: 164.