Hujjoji Kan Halaccin Yin Mauludin Annabi
Hujjojin Yin Mauludi Kashi Na Daya 

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai, Tsira da Amincin Allah su Tabbata, ga Manzo da Alayensa, Tsarkaka Managarta.

A Wannan Bahasi Mai Take (Hujjojin Yin Mauludi) na ke so in kawo kadan
daga cikin dalilan yin Mauludi, amma kafin nan zan so in fara da kawo dalilan da wadanda ba sa yin Mauludin suke kafawa, na rashin inganci ko ma haramcin yin Mauludin a gurinsu.
1-Da farko dai su wadanda ba sa yin Maududi dinsuna kafa hujjar haramcin yin Maulud ne saboda dogaro da Hadisin da Manzo (s.a.w) yake cewa: ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - » ﻣَﻦْ ﺃَﺣْﺪَﺙَ ﻓِﻰ  ﺃَﻣْﺮِﻧَﺎ ﻫَﺬَﺍ ﻣَﺎ ﻟَﻴْﺲَ ﻓِﻴﻪِ ﻓَﻬُﻮَ ﺭَﺩٌّ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ . ﺝ ,7, ﺹ 36, .
Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya fari wani abu a cikin Al-Amarinmu wanda baya ciki Addini to an mayar masa. Sahihul Bukhari, jiz’I na 7, shafi na36.
Kuma Mauludi Musamman da irin wannan launi da muke iya gani a yanzu daga baya ne aka ƙirqira, don haka an mayarwa masu yin Mauludi Abunsu. 
2-Suna ganin Mauludi Bidi’a ce, alhali a Hadisi da Manzo (s.a.w) na cewa:ﻭﻗﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ : " ﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ ﻭﻛﻞ  ﺿﻼﻟﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ . ﻣﻮﻃﺄ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺎﻟﻚ . ﺝ .1,ﺹ 355, .
Fadin manzo (s.a.w) Dukkan wata bidi’a-Abinda aka qirqiro- 6ata ce kuma dukkan wata 6ata tana cikin wuta. Muwatta na Imam Malik, juz’I na 1, shafi na 355.
Kuma mauludi qirqirarren abu ne, don haka makomarsa wuta. 3-Masu cewa son Annbi (s.a.w) ne ta sa suke yin Mauludi, shin sun fi Sahabbai Irinsu Abubakar, da
Umar, da Usman, da Aliyu, son Annabi (s.a.w) ne? gashi su ba su yi Mauludi ba, don haka inda Mauludi Addini ne da su magabata su zasu fara yi.
4-Yadda za a gane Mauludi baya cikin Addini shi ne: meye Farillai ko Mustahabban Mauludi?
5- Ana chakuduwa maza da mata a gun mauludi, alhali yin hakan haram ne.
6-Masu yin biki da murna a ranar Mauludi suna murana ne da rasuwar manzo (s.a.w) saboda a ranar da aka haife shi a ranar ya yi wafati.
7-keɓe wani Wata da wani Rana don yin Mauludin Annabi (s.a.w) Taƙaita son da ake masa ne, don Yakamata ne kullun mutum yana son Annabi (s.a.w).
8-Anfi Qasar Saudiyya ce son Annabi (s.a.w) meyasa su basu yin Mauludi?
9-Magata-Salafus Salihin- Irinsu Shaikhul Islam Ibni Taimiyya Waɗanda sun fi mu sanin Addini amma suma ba su yi ba. 
10-kwaikwayon Nasara ne da suke murna da haihuwan Annabi Isa (a.s). Idan Allah ya Yarda zamu yi Bahasi akan Waɗannan Abubuwa 10 Ɗaya Bayan Ɗaya, sai a Biyomu. 
A ci gaba da Wannan Bahasi Mai take(Hujjojin yin Mauludi) na ke so in bijiro da Dalilan da Masu qin yin Mauludin 'Daya bayan 'Daya Wanda suka Dogara da su, sai in bada Amsoshinsu dai dai bakin Gwargwado: 
1-Da farko suna kafa Hujjar Haramcin yin Maulud ne bisa Dogaro da Hadisin da Manzo (s.a.w) ke cewa:  ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - » ﻣَﻦْ ﺃَﺣْﺪَﺙَ ﻓِﻰ ﺃَﻣْﺮِﻧَﺎ ﻫَﺬَﺍ ﻣَﺎ ﻟَﻴْﺲَ ﻓِﻴﻪِ ﻓَﻬُﻮَ ﺭَﺩٌّ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ . ﺝ ,7, ﺹ 36, .
Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya fari wani abu a cikin Al-Amarinmu wanda baya ciki –Addin-to an mayar masa.  Sahihul Bukhari, jiz’I na 7, shafi na36. Kuma Mauludi musamman da irin wannan launi da muke gani a yanzu daga baya ne aka qirqira, don haka an mayarwa masu yin Mauludi abunsu. 
Amsa:  Muna buqata zuwa ga Bayanin Ma'anar Wannan Hadisin a Wurin Masana Hadisi, kafin mu gina Hukunci a kai, Ga bayanin kamar Haka: 
ﻭﻗﺎﻝ: ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺘﺢ : ﻭَﻫَﺬَﺍ ﺍﻟْﺤَﺪِﻳﺚُ ﻣَﻌْﺪُﻭﺩٌ ﻣِﻦْ ﺃُﺻُﻮﻝِ ﺍﻟْﺈِﺳْﻠَﺎﻡِ، ﻭَﻗَﺎﻋِﺪَﺓٌ ﻣِﻦْ ﻗَﻮَﺍﻋِﺪِﻩِ، ﻓَﺈِﻥَّ ﻣَﻌْﻨَﺎﻩُ : ﻣَﻦْ ﺍﺧْﺘَﺮَﻉَ ﻣِﻦْ ﺍﻟﺪِّﻳﻦِ ﻣَﺎ ﻟَﺎ ﻳَﺸْﻬَﺪُ ﻟَﻪُ ﺃَﺻْﻞٌ ﻣِﻦْ ﺃُﺻُﻮﻟِﻪِ ﻓَﻠَﺎ ﻳُﻠْﺘَﻔَﺖُ ﺇﻟَﻴْﻪِ.
Fassara: Ibni Hajar a cikin Fatahul Bari ya ce: Wannan Hadisin ana Qirga shi daga cikin Asullan (Tushen) Addinin Musulumci, kuma Qa'ida daga cikin Qa'idojinsa, kuma Ma'anarsa shi ne: "Duk Wanda Ya Qirqiri Wani Abu a Addini Wanda ba'a sami  Asali daga cikin Addini ya Shaide shi ba to ba'a kula da shi.
Kenan Idan Asali ko Tushen Addini ya Shaidi Abu to za'a kula da shi a Addini.
To Meye Maulud ke Qumshe da shi? Zamu Saurari Amsa daga Bakin Shaikhul Islam:
قال ابن تيمية :   *وكذلك ما يحدثه بعض الناس إما مضاهاة للنصارى في ميلاد عيسى عليه السلام وإما محبة للنبي صلى الله عليه وسلم وتعظيما له والله قد يثيبهم على هذه المحبة والاجتهاد لا على البدع* 
أحمد بن عبد الحليم بن تيمية الحراني أبو العباس )728(، اقتضاء الصراط المستقيم مخالفة أصحاب الجحيم ، ج 1 ص 294 ,دار النشر, مطبعة السنة المحمدية - القاهرة - 1369 ، الطبعة الثانية ، تحقيق محمد حامد الفقي.
Fassara:
Ibni Taimiyya ya ce: Haka Abin da Wasu Mutane suke Qirqira ko dai sabo da Kwaikwayon Nasara ne akan Haihuwan Annabi Isa (a.s) ko dai Soyayya ne ga Annabi (s.a.w) da kuma Girmama shi, kuma Allah zai iya basu ladan Wannan Soyayyan da Qoqarin da Suka yi, ba saboda Bidi'ar da suka yi ba. Iqtidaa'u Siratil Mustaqim Mukhalsfatu Ashabul Jahim, Vol 1 P 294........
Na Tabbata inda za'a Tambayi dukkan masu yin Maulud cewa: don me kuke yin Maulud zasu ce: 
1-"Don Soyayyarsu ne ga Ma'aiki (s.a.w).
2-Don Girmama Ma'aiki ya sa suke Mauludi.
Wanda Shekh Ibni Taimiyya ya ce: zasu iya samun lada akan haka.
Tambaya anan shi ne Ashe Asal ko tushen Addini ba su Shaidi SON ANNABI ko GIRMAMA SHI ba?
Idan Amsar shi ne: E, sun Shaida to Abinda ake buqata ya Tabbata, idan Amsar ita ce: a'a.  Idan kuna biye da mu Bayan Mun kawo Bayanin Ma'anar Hadisin da Ibni Jajar ya yi Wanda ke nuna cewa: Ana nufin ne Wanda ya Qirqiro Wani Abin da babu Asul wani Ginshiqin Addini da ya ya bada Shaida a kansa to Wannan Abin ba'a kula da shi a Addini.  Sai kuma Muka kawo Zancen Ibni Taimiyya akan batun bada Masu yin Mauludi lada akan Soyayyarsu ga Manzo da Girmama shi, Sai a qarshe muka yi Al-kawarin Tabbatar da cewa Addinin Musulunci ya Gina Mutane bisa: 
1- Soyayyan Manzon Allah.
2- Da Girmama shi.
 Ga Kadan daga Wuraren, Allah yana cewa:  

﴿...ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺷَﻌَﺎﺋِﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻧَّﻬَﺎ ﻣِﻦ ﺗَﻘْﻮَﻯ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏِ﴾

(...Wanda ya Girmama Alamu na Allah na daga cikin Taqawar Zuciya)
Bana tsammanin da akwai mai Shakkan kasantuwar Manzon Allah Babba Alama na Allah.  A Wani Wuri kuma Allah ya sake cewa:
إِنَّآ أَرْسَلْنَــكَ شَهِدًا وَمُبَشَّرًا … ﻟِﺘُﺆْﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺗُﻌَﺰِّﺭُﻭﻩُ ﻭَﺗُﻮَﻗِّﺮُﻭﻩُ ﻭَﺗُﺴَﺒِّﺤُﻮﻩُ ﺑُﻜْﺮَﺓً ﻭَﺃَﺻِﻴﻠًﺎ(٩)
Lallai Mun Turoka a Matsayin Mai Shaida Mai Bushara (8) Don Ku yi Imani da Allah da Manzonsa, kuma Ku Taimake shi, kuma Ku Girmama shi, kuma Ku Tsarkake shi Safiya da Maraice (9).
Akan Soyayyar Manzon Allah kuma Allah yana cewa:
﴿ﻗُﻞْ ﺇِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﺁَﺑَﺎﺅُﻛُﻢْ ﻭَﺃَﺑْﻨَﺎﺅُﻛُﻢْ ﻭَﺇِﺧْﻮَﺍﻧُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﺯْﻭَﺍﺟُﻜُﻢْ ﻭَﻋَﺸِﻴﺮَﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻣْﻮَﺍﻝٌ ﺍﻗْﺘَﺮَﻓْﺘُﻤُﻮﻫَﺎ ﻭَﺗِﺠَﺎﺭَﺓٌ ﺗَﺨْﺸَﻮْﻥَ ﻛَﺴَﺎﺩَﻫَﺎ ﻭَﻣَﺴَﺎﻛِﻦُ ﺗَﺮْﺿَﻮْﻧَﻬَﺎ ﺃَﺣَﺐَّ ﺇِﻟَﻴْﻜُﻢْ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺟِﻬَﺎﺩٍ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻠِﻪِ ﻓَﺘَﺮَﺑَّﺼُﻮﺍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺄْﺗِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑِﺄَﻣْﺮِﻩِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳَﻬْﺪِﻱ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻔَﺎﺳِﻘِﻴﻦَ ‏( 24 ﴾
(Ka ce: idan ya kasance: Iyayenku, da 'Ya'yanku, da 'Yan Uwanku, da Matanku, da Danginku, da Dukiyoyin da kuka Tara, da Kasuwancin da kuke tsoron Hasaransa, da Wuraren Zaman da kuka yarda da su, kun fi Sonsu akan Allah, da Manzonsa da Jahadi a Tafarkinsa, to Ku zauna Har sai Allah ya zo da Al'amarinsa, kuma Allah bai Shiryar da Mutane Fasiqai.
Kenan Dolenka kafi Son Allah da Manzonsa da Jahadi Sama da Iyayenka da 'Ya'yanka da 'Yan Uwanka da Matanka da Danginka da Dukiyarka da Tijaranka da Gidajenka, in ba haka ba kana cikin Fasiqi!  Don haka Musulumci yana kiran Mutane ne akan Girmama Manzo da Soyayyarsa, kuma su ne Abubuwan da Ibni Taimiyya ya ce Masu Maulidi za'a iya basu lada akan aikatasu.
2-Suna ganin Mauludi Bidi’a ce, kuma Ga shi ya zo a Hadisi Manzo (s.a.w) yana cewa:

ﻭﻗﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ : " ﻛﻞ ﺑﺪﻋﺔ ﺿﻼﻟﺔ ﻭﻛﻞ ﺿﻼﻟﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ .
ﻣﻮﻃﺄ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺎﻟﻚ . ﺝ .1,ﺹ 355, .

Faɗin Manzo (s.a.w) Dukkan wata Bidi'a Ɓata ce kuma dukkan wata Ɓata tana cikin wuta. Muwaɗɗa na Imam Malik, juz’I na 1, shafi na 355. 
Kuma Mauludi Bidi'a ce, don haka Makomarta wuta.
Amsa:  Da Farko zamu so Mu yi Ta'arifin Bidi'a a Yare da Shari'a, a yare idan aka ce Bidi'a ana nufin: 
ﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻐﺔ : ﺗﻄﻠﻖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﻲﺀ ﺍﻟﻤﺨﺘﺮﻉ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﺮ ﻣﺜﺎﻝ ﺳﺎﺑﻖ ﻓﻤﻦ ﺃﺗﻰ ﺑﺄﻣﺮﻟﻢ ﻳُﺴﺒﻖ ﺇﻟﻴﻪ ﻓﻬﻮ ﻣﺒﺘﺪﻉ.
Bidi'a a Yare: ana Ɗora ta ne akan Abin da aka Qirqira ba akan Abin da ya Gabata ba, Wanda ya yi Wani Al-amari Wanda ba Wanda ya Riga shi za'a kira shi Wanda ya Qirqira
Amma Bidi'a a Shari'a ita ce:
ﻭﻓﻲ ﺍﻻﺻﻄﻼﺡ : ‏« ﻣﺎ ﺃﺣﺪﺙ ﻣﻤﺎ ﻻ ﺃﺻﻞ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻳﺪل عليه .

A Shari'a ita ce: "Abinda aka Fare shi daga cikin Abubuwan da bai da Asali a Shari'a Wanda zai yi nuni a kan shi". 

Mun ji Yadda Ma'anar Bidi'a take a Yare da Shari'a, kuma Zamu yi Amfani ne da Ma'anar Bidi'a a Shari'a ba a Yare ba, Saboda Shari'a ce aka Kallafa Mana binta ba Yare ba.
To Abin Tambaya a nan shi ne: Shin Soyayyar Manzo (s.a.w) ne bai da Asali a Addini ko Girmama shi? 
Idan Har Soyayyan Manzo (s.a.w) da Girmama shi suna da Asali a Addini, kuma in dai Har Shari'a ta yi nuni da su, to baza a kira Mauludi da Bidi'a ba, Sabda Muna Yin Maulidi ne Don: Soyayya da Girmama Manzon Allah (s.a.w) da Muke yi.
3-Masu cewa son Annbi (s.a.w) ne ya sa suke yin Mauludi, shin sun fi Sahabbai Irinsu Abubakar, da Umar, da Usman, da Aliyu, son Annabi (s.a.w) ne? gashi su ba su yi Mauludi ba, don haka inda Mauludi Addini ne da su magabata su zasu fara yi.
Amsa:   Idan Muka yi La'akari da Abinda ke ƙumshe a cikin Maulud na Soyayyar Manzo da Girmama shi zamu iya cewa Sahabbai Sun yi irin Nasu Maudin, Wanda ta yiwu ya Saɓa da irin namu Mauludin Sakamakon Saɓanin Mutane da lokaci, Misali akan haka Shi ne: kowa ya San  Sahabbai sun koyi karatun Al-ƙur'ani Amma tayiwu Hanyar da suka koya ya Saɓa da namu Hanyar koyon karatun Al-ƙur'ani a yau, a da ana Rubuta Al-ƙur'ani ne a Jikin Ganyen bishiya da Fata da Ice, Amma Mu a Yanzu namu Al-ƙur'anin an Rubuta shi ne a Takarda, Sannan a jikin Al-ƙur'anin da ke Hannun Sahabbai ba Ɗigo ba Wasali, Amma a namu Al-ƙur'anin a kwai Ɗigo da Wasali, Sannan Tayiwu ma ta Hanyar Kaset muke koyon karatun Al-ƙur'ani Amma su a Zamaninsu ba Radiyo ba Kaset balle su ko yi karatun Al-ƙur'ani ta Hanyarsa, Amma idan aka ta shi Bayani za'a ce da kai da su duk kun koyi karatun Al-ƙur'ani dukda kun Saɓa a Usulubin koyon.
Misali na Biyu shi ne: a Zamanin Manzon Allah Sahabbai Sun yi Neman Aure Amma Tayiwu yanayin Neman ya Saɓa da namu Neman Sakamakon Canjin Zamani da Al-ada.
Sannan kowa ya San a Zamanin Sahabbai sun yi Sujada ne a kan Qasa da Dutsi da Ganye, Amma yanzu zaka ga Mutane suna Sujada ne akan:
Kafet, Tabarma, Siminti, Kwalta da sauransu, ba tare da Mutum yana jin ya Saba ma Annabi da Sahabbai ba, su masu Tuhumarmu akan yin Maulud so sukeyi su ce: Idan Annabi da Sahabbai ba su yi Abu ba ya Haramta mu yi, Muma sai mu Tambayesu cewa: Me ya Sa Ba ku Sujada akan Abin da Annabi da Sahabbai suka yi a kai? A she kuma kun Aikata Haram kuma Baku da Sallah?
Sannan da Zaka yi Tambayi cewa: Shin Annabi (s.a.w) ya kasance yana lizimtan Al-ƙur'ani a Watan Azumi kamar yadda mu ke yi? Za ka ji Har da Wadanda basu yin Mauludi sun ce: E, Tayiwu ma har su kafa Hujja da Hadisin ya nuna cewa: Mala'ika Jibril ya kasance yana Sauka suna Karatu tare da Manzon Allah kullun, Amma inda zaka yi Tambaya cewa: Shin yadda Yanzu Muke yi haka suka yi? Wato An sami Mai Jan Baqi da Mai Fassarawa da Masu Sauraro a Zamanin Manzo (s.a.w)? Amsar itce a'a, to Meyasa? Tayiwu saboda wasu dalilai na Daban, Wanda baza su Wuce cewa: Muna Ganin yin Tafsirin Al-qur'ani ga Mutane a cikin Watan Ramadan a Yanzu shi ya fi, to Amma shin mun fi Manzon Allah da Jibril sanin Abin da ya fi dacewa ne? Mun barwa Masu Tambayar mu cewa: Shin Mun fi Sabbai Son Manzon Allah ne Meyasa basu yi Maulud ba? su Amsa Wannan Tambayar cewa: shin kun fi Manzon Allah da Jibril sanin Abin da ya fi dacewa ne kuke Tafsirin Al-qur'ani a Watan Ramadan Al-hali Manzon Allah da Jibril su Taqara su ke yi a Watan ba Tafsir ba? Mun barsu su bada Amsar Wannan Tambayar tunda suma suna Tafsir a Watan Ramadan Saɓanin Abin da Manzo da Jibril suke yi.
A biyo mu don ci gaba. 

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi.

Tahir Umar Sulaiman