bayyinaat

Kurani
Tafsiri
Shi: lamiri ne na namiji tare da cewa Alllah (SW) ba namiji bane kuma ba mace ba, a yaren larabci a kan yi amfani da lamirin namiji don kiran sunan sa maɗaukakin sarki, harma mala'iku da sauran su don girmamawa.
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna kan saukar waxannan surori biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa, an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haxa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah)
Kamar yadda ya zo daga wajan yan uwan mu ahalussunna game da saukar surorin nan biyu wato suratul falaƙ da suratun naas cewa: an yi wa Manzo (SAW) sihiri aka haɗa da gashin sa da ƙulli 11 aka binne a wata rijiya, sai ya ji kamar an ƙulle masa kan sa (wal'iyazu billah)
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1) Da sunan Allah mai rahama (mai faɗin da take ko ina) mai jin ƙai(rahama ce keɓantacciya wadda bata haɗe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
Ina neman tsarin Ubangiji daga shaiɗan jefaffe (daga rahamar ubangiji, aljannar ni'ima ta tunani da ta rayuwa bakiɗaya duk an fitar da shi, tare da saukar fushin ubangiji a kan sa).
Tana karantar da tabbatar Tashin Kiyama, kuma duka abin da ake aikatawa idan ba na tattalin Kiyamar ba ne, to, ya zama wahalar da kai, maras amfani, da bata lokaci. Fatanmu Allah ya sa mu samu damar ci gaba da wannan fassara.
2