bayyinaat

Sīrāh
Imamai Sha Biyu
Shahadar jikan Manzon Allah (s.a.w.w) Imam Hassan Mujtaba {a.s}
Muna taya Shi'ar Nigeria da sauran Shi'ar duniya, juyayin shahadar jikan Manzon Allah (s.a.w.w) Imam Hassan Mujtaba {a.s}
Shahadar Sayyida Ruƙayyah {A.S}
Ranar biyar ga watan safar, shine ranar da ƴar Imam Hussain {A.S}, Sayyida Ruƙayyah tayi shahada a garin dimashq na Sham (wato siriya a yau).
Yazo a cikin addu'a "Ya ubangiji ka sanar da ni kanka domin idan baka sanar da ni kanka ba, ba zan san Manzon ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Manzon ka domin idan baka sanar da ni Manzon ka ba, ba zan san Hujjar ka ba. Ya ubangiji ka sanar da ni Hujjar ka domin idan ba ka sanar da ni Hujjar ka ba, zan bace a addini na."
Imam Zainul Abidieen (a.s)
Abin lura wajan Amsar sallar mutum shine wilayar mu da kuma bara'a ga maƙiyan mu.
Gaskiyar magana Ashura ba munasaba ba ce ta kuka da alhini kawai ba, a'a munasaba ce ta zaburantar da masu Addini da Aqida, masu Mutunci da Mutuntaka, Mazlumai domin su yunkura su kwaci Addininsu da Aqidarsu da Mutuncinsu da Haqqinsu a wurin Azzalumai Yazidawan zamaninsu. Saboda haka a matsayinka na dan shi'a (ko in ce mai addini) kuma Hussainy baka da wani Addini ko Aqida ko mutunci ko Identity da ya wuce wannan
Abin la'akari shi ne: gaba dayan A'imma (A.S) hadafinsu daya ne, wannan hadafin kuwa shi ne: Sãmar da Hukumar Allah a doron kasa, a nesa ko a kusa, sai dai hanyoyin kaiwa ga hadafin ne suke caccanzawa daga lokaci zuwa lokaci daga wani yanayin zuwa wani