bayyinaat

Akida
Imamanci
Kamata ya yi a ce sun kalli hadisin kallo na ilimi ‘yantacce daga duk wani tunani da ya gabata, domin su da kansu su iya tabbatar da kuskuren wannan fassara da suka yi wa hadisin ta abin da zai zo nan gaba, idan har Annabi Muhammadu (s.a.w) ya kasance ya na kallon abin zai zo nan gaba ne to don me zai fayyace adadin halifofi goma sha biyu, tare da cewa lokacin zai ta tafiya ya ma wuce iya zamanin halifofin?
Akwai dalili na akida kan wannan fahimta a cikin daruruwan hadisan da suka zo daga Manzon Allah (s.a.w) wadanda suke yin nuni kan tantance wanene hakikanin Mahdi (a.s) da kuma kasancewarsa daga Ahlulbaiti (a.s)
Isma ita ma daya ce daga cikin mafi mahimmancin siffar wanda zai kasance khalifan Annabi, domin kariya ga addinin musulunci, haka kuma cikar ma’ana a kan wajib cin abin da yake larura na addini.
Shin wanda yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi shi, ko kuwa wanda baya shiryarwa face dai shi a ke shiryarwa? To minen a gare ku yaya kuke yin hukuncI
Duk da irin wannan matsayi da daukaka da take da shi bai sa ta gafala da ayyukan ibada da neman kusanci zuwa ga Allah ba, Wannan ya sa ta zama abar koyi ga dukkan Musulmi.