Ijtihadi da Takalidi

Ijtihadi da Takalidi

Hukunc-hukunce su ne: Dokokin da Suka Gangaro daga Mai Shar'antawa don Tsara Rayuwan Dan Adam. Kuma Wadannan Hukunce Hukuncen su ne Suke Iyakance Aikin da ya Hau kan Mutum Wanda zai yi da Wanda zai Bari, kuma sun kasu ne kashi Biyar: 1-Wajibi. 2-Haram. 3-Mustahabi. 4-Makaruhi. 5-Mubahi.
Duniyar Abokai: Kyakkyawar Makwabtaka

Duniyar Abokai: Kyakkyawar Makwabtaka

Hakika murmushi da sakin fuska suna nuni ne ga kauna da kuma girmamawa, don haka ne suka zamanto hanyar jawo kaunar mutane ga mutum da kuma yada soyayya tsakanin mutane. Sakin fuskarka ga mutane da kuma fuskantarsu da maganganu masu dadi sukan bude zukatan mutane gare ka da kuma rufe kofofin kiyayya gare ka.
Tsarkin Sirrin Mutum

Tsarkin Sirrin Mutum

Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga haram to (har yanzu dai) ku yi a hankali kada ya rude ku, domin lallai sha'awowin halittu suna sassabawa, sau da yawa wani wanda yake nisantar dukiyar haram komai yawanta, (amma) kuma (da zai samu dama, da) ya dora kansa (ya hau) kan wata mummunar mata mai muni (duk muninta) sai ya aikata haram (na zina) tare da ita.
Abota Da Abokai

Abota Da Abokai

Alaka da sauran mutane fanni ne daga cikin muhimman fannonin rayuwa ta zamantakewa, da yawa daga cikin mutane ba sa kyautata fannin alaka da sauran mutaneā€¦don haka ne suke fuskantar rashin nasara wajen samun abokai da kuma lalata alakarsu da sauran mutane. Hakan kuwa saboda ba su san yadda za su jawo hankalin mutane (abokai) zuwa gare su ba ne da kuma yadda za su yi mu'amala da su ba. Hakika ilmummukan sanin dan'Adam, na yau da kullum da kuma uwa-uba shiryarwa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma tsarkakan Imamai (a.s.) duk sun koyar da mu hanyoyin samun abokai da kuma yadda za mu yi mu'amala da su.
1 2 3 4 5 6 7 8