bayyinaat

Published time: 08 ,April ,2018      16:03:19
Mun kudiri aniyar zabo Kissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan kissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.
Lambar Labari: 101
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Kur’an: Al-Kalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Kissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan kissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. MAFI GIRMAN HAKURI; SHINE KADA MUYI SABO:
An taba yin wani bawan Allah mai matukar yawaita bauta a al'ummar da ta gabata lokaci mai tsawo. Wanda bai taba ruduwa da rudun duniya ba. Hakan sai ya sa Ran babban shaidan (Iblis) ya baci matuka. Sai babban shaidan (Iblis) yayi kuwwa mai karfi, sai tattara dakarunsa, duk suka taru a kewaye dashi. Sai ya tambaye su kamar haka: Waye a cikinku zai iya batar da wancan A'bid (mai yawan bauta) din? sai daya daga cikinsu yace, zan iya. Iblis yace, ta yaya? sai yace, ta hanyar mata wato Mace. Iblis yace, hakan ba zai yi tasiri gare shi ba, saboda ya kasance kwata-kwata bashi da alaka dasu kuma bai San su ba. sai wani shaidanin ya tashi yace, ni zan batar dashi da Giya, shaye-shaye da sauransu. Iblis yace, kaima ba za ka iya yaudararshi ba ta wannan hanyar. 

Sai shaidan na uku ya tashi yayi ikrarin batar dashi ta hanyar fakewa (pretending) da kuma bayyana a matsayin mumini mai yawan bautar Allah. Sai Iblis yace, lallai kai za kayi nasara akanshi. Sai shaidanin nan ya shiga gurin mai bautar nan a matsayin mutumin kirki, yaje kusa da gurin da mutumin yake yin ibada, shima ya tashi sallah. Mai ibadar nan bayan wasu 'yan lokuta yayi sallah da yawa, sai ya tsaya domin ya huta, amma shaidanin nan ko gezau (wato ba sassauci). Ganin haka sai mai ibadar nan, ya fara jin kaskanci ganin ga sabon zuwa, Amma ya kere masa sa'a. cikin tawali'u sai ya tambayi shaidanin cewa, kai kuwa ya akayi ka samu kuzari da tsayuwa wajen bautar Allah haka, babu ko gajiya? Amma la'anannen bai ko kula shi ba, kawai ya ci gaba da yin sallah. Ya dai takura shi da tambaya makamancin haka, cewa meye ya kaishi ga wannan babban matsayi? 

Sai shaidanin nan yace, Kai bawan Allah! na kasance nayi SABO (wato ya sabawa Allah), amma sai na tuba, kuma kodayaushe ina sanya Sabon nan a raina yana damu na, wannan ne ya bani karfin yin ibada ba tare da gajiya ba. Sai mai ibadar nan ya tambaye shi cewa, wanne sabo ne, nima in samu in aikatashi. Sai shaidan yace masa kaje gari kaza... ka shiga gidan wata mata mai zaman kanta, sai ka bata Dirhami biyu. sai mai ibadar nan yace ai ko Dirhami biyun bani da, sai shaidan ya dauko daga gurin da yake zaune, ya mika mashi, sai mai ibadar nan ya kudiri azama, ya nufi waccan gari, cikin kayanShi na kamala. 

Da ya isa garin, sai ya tambayi gidan matar nan mai zaman kanta. koda mutane suka ga mutun cikin kamala yana tambayar wancan gida, sai suka dauka cewa, zai je ya shiryar da matar ne. sai suka nuna mashi. Da shigarshi gidan sai ya jefa mata dirhamin nan biyu, yace ki tashi mu shiga daki, sai ta tashi suka tafi dakin ta, tace dashi, ya kai wannan bawan Allah, kazo min a wani irin yanayin da babu wanda ya taba zo min a irin shi (wato yanayi na kamala). Dan haka dan Allah zan so ka gaya min, me yasa ka zabi kazo gurina? sai ya gaya mata duk abin da ya faru. Sai tace dashi, Ya kai bawan Allah, ka sani Kin aikata zunubi yafi sauki akan tuba bayan an aikata shi. Ka sani ba zai yiwu ba mutun yayi zunubi yana sane (intentionally) sai daga baya ya tuba, sannan kuma kace zai sami babban matsayi a gurin Allah kamar yadda kake sawwarawa.

Dan haka lallai kowaye wanda ya turo ka dinnan, to shaidan ne yayi badda kama (in disguise) ya zo maka domin ya batar da kai. ka koma inda ka fito ba zaka iske shi ba a can. Sai mai ibadar nan ya koma gida. Wannan Mata kuma sai Allah Ya karbi ranta a wannan daren. Kashegari da safe kuma sai mutanen garin suka ga rubutu a kofar gidan nata an rubuta cewa: dukkan mutanen garin su je Jana’izar wannan Mata, saboda tana cikin wadanda zasu shiga aljanna. sai mutane suka yi mamaki, dan haka sai basu yi hakan ba, suka bar ta har tsawon kwana uku. Sai Allah Ya yiwa Annabin wannan zamanin wahayin dukkan abin da ya faru, mai ruwayar yace, Annabi Musa Alaihissalam ne.
Allah Yace dashi kaje ka sallaci Mata wance saboda na gafarta Mata. na tanadar Mata aljanna saboda cetar bawa Na da tayi daga Saba min.

2. KYAKKYAWAN KARSHE NA GA MASU TSORON ALLAH:
An taba yin wani Mumini a zamanin da, da ya kasance yana yawaita fadar: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki; kuma Kyakkyawan karshe na ga masu tsoron Allah." to ashe wannan furuci yana kona Ran Iblis (babban shaidan). Dan haka sai ya turo daya daga cikin yaranshi a sifar mutun domin yazo ya canzawa muminin nan tunaninshi akan wancan furuci da yake yi. 

Koda karamin shaidanin yazo, da yaji Muminin nan ya kuma fadar maganar hikimar da ya saba, sai shaidanin yace dashi "kai malam kyakkyawan karshe yana ga masu kudi da dukiya." sai muminin nan yace a'a ba haka bane, lallai kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah. Shaidanin nan yayi iya yinshi domin ya canza muminin nan, amma ya kasa, sai yace to, mu nemi wani mutumin a hanya ya raba mana gardama, kuma da sharadin cewa, duk Wanda akayi galaba akanshi to za a yanke hannunshi daya. Mumini ya yarda, sai ga wani mutumi yazo wucewa, suka tambaye shi, sai yace musu, "kyakkyawan karshe na ga masu kudi da dukiya'. Shikenan sai aka yanke hannun Mumini guda daya. Sai shaidan yace dashi ka gani ko? na gaya maka ai! sai Muminin nan yace ai lallai Shi har yanzu bai yarda ba. Sai shaidan ya kuma cewa, to mu tambayi wani mutun din da zai sake bullowa, shima wannan karon za a cire hannun duk Wanda akayi galaba akanshi, Mumini ya yarda. Sai ga wani mutun ya bullo, aka tambayeshi, shima ya ba da amsa kamar na farko, sai aka cire daya hannun Muminin. Shaidan ya kuma ce masa, ka gani gashinan ka rasa hannu biyu, na gaya maka, abin da kake cewa ba haka bane. Muminin nan ya kuma cewa, ina! ai lallai kam, kyakkyawan karshe na ga masu tsoron Allah. sai shaidan yace, to a kuma tambayar mutun na uku, amma a wannan karon, Kai za a cirewa duk wanda akayi galaba akanshi. Mumini ya yarda. sai Allah Ya turo Mala'ika a sifar mutun ya biyo hanyar, sai suka fara haduwa dashi, suka tambaye Shi. sai ya dauki hannun Muminin nan daya ya dora shi a gurin da yake, Sannan ya shafi gurin, sai hannu ya koma yadda yake, ya dauki dayan ma yayi masa kamar na farko. Sannan sai ya fille kan shaidanin nan, yace "LALLAI KYAKKYAWAN KARSHE NA GA MASU TSORON ALLAH"...Murmushi....murmushi...!
*****
3. TAMBAYOYI HUDU:
Wani mutun yazo gurin Imam Ali (Alaihis-salam) yace: Ba na tambaye ka abubuwa hudu ba, ka bani amsar su?!
1. Menene wajibi? kuma meye yafi zama wajibi?
2. Menene Kusa (kusanci)? kuma meye mafi Kusa?
3. Menene abin al'ajabi (mamaki)? kuma meye mafi al'ajabi?
4. Mecece wahala? kuma meye tsananin wahala?

Sai Imam Ali (Alaihis-salam) yace:
1. Wajibi shine yi wa Allah Ta'ala Biyayya (Da'a); Amma mafi zama wajibi shine, barin Sabo.
2. Kusa itace Ranar Alkiyama; Amma mafi kusanci itace Mutuwa.
3. Abin Al'ajabi kuwa itace Duniya; Amma mafi zama abin al'ajabi shine Son Duniya.
4. Wahala kuwa shine Kabari; Saidai mafi wahala shine Zuwa babu guziri.

Allah Ta'ala Yayi mana kyakkyawan Karshe.
*****

4. LAILA DA MAJNUN:
An taba yin wani mutumi wai Majnun, ma'ana Wanda Hankalinshi ya gushe. 
Tambaya!!! garin yaya ya Sami wannan suna? Da farko dai wannan mutumi, kawai ya ji sunan Laila ya bugi kunnenshi, sai kawai ya rika sawwarata (imagining) a zuciyarshi, har ya kamu da sonta. Wadda Soyayyar tata har ta kai wani yanayi da ba zai iya hakura ba, ba tare da ya nemi abin son nan tashi ba.

Dan haka sai ya kuduri aniyar fita neman abin sonshi. Ya fita yaje wannan gari, yaje waccan gari, amma babu labarin Laila, haka yayi ta shan wahala da ketara garuruwa domin haduwa da abin sonshi. A karshe dai ya hadu da wani wanda ya taba jin labarin Laila, sai yake ce mashi tana kasa kaza da kaza... dai yayi masa kwatancen kasar da nisa daga yadda yake. Haka dai Majnun ya kara daura damarar tafiya. -kamar yadda kowa ya sani cewa ance Garin masoyi baya nisa, kuma so yana gusar da duk wata wahala daga Ido ko Rai na masoyi- Dan haka sai Majnun yaci gaba. 

To!!! Yau dai Allah Yayi ga Majnun a gari kuma a kofar gidan da Laila take!!!

To bamu San me zai faru ba!!! Masu biye damu ku sani fa mun tsallake wasu wahalhalu da hatsarurruka da bala'o'in da Majnun ya gamu dasu a hanya domin zuwa gurin abin Sonshi. To amma koda Majnun ya kwankwasa kofar Laila, sai Laila ta tambaya, Wanene? sai Majnun yace mata "Nine Majnun"
sai Laila tace dashi "Je ka ba zan bude maka ba." Sai Majnun ya ja da baya ya koma, sai ya sami karkashin wata bishiya ya zauna, zuwa wani dan lokaci wutar so ta kuma ruruwa a zuciyarshi, sai ya tashi ya koma bakin kofar Laila, ya kuma kwankwasawa, tazo bakin kofa tace Wanene? a wannan karo, sai yace da ita "KE CE!!!" -Allahu Akbar, kunji fa masu saurare, wato duk son da yake yi mata a baya, tunda ya iya shaida kanshi da yace mata "Nine Majnun' a kwankwasawar farko, to hakan yana nufin ba Majnun din bane, saboda mahaukaci na Hakika baya iya shaida kanshi, amma da ya koma gefe bayan taki bude masa, a yayin da Mahaukacin So din ya taso mashi, sai ya gaza bambancewa tsakanin Kanshi da abin Sonshi- kar in cika ku da surutu, da yace mata KECE ai sai ta bude mashi Kofa.

Da bude kofa, sai ga Laila ta bayyana ga Majnun. sai ga Laila ta bayyana Tsohuwa, Ajuza, Rarrauna. Sai take cewa Majnun: "TO KA GANNI DAI YADDA NAKE, TSOHUWA, RARRAUNA, NA GAJI. DAN HAKA DA ZAKA MAYAR DA SONKA GA WANDA BAYA TSUFA, BAYA GAJIYA, WANDA YA MALLAKEKA, YA MALLAKENI? TO DA KA DANDANI ZAKIN SO."
*****

5. ALKALI:
An taba samin wani alkali A'dilin gaske, da yazo mutuwa, sai ya yiwa matar shi wasicci da cewa, idan ya mutu, bayan anyi mashi wanka, to kada a rufeshi, yana so a dora shi akan gadon katako, zuwa wasu 'yan kwanaki, aga me zai faru ga jikinshi, ya ci gaba da cewa, shidai ya san bai yi wasu munanan ayyuka ba (kuma dama an shaide shi cewa Adili ne). Da ya mutu sai matar nan tayi kamar yadda ya umarceta, bayan dan kankanen lokaci, sai ta ga tsutsotsi suna cin kwakwalwarshi. Sai tayi mamaki matuka. 

Kashegarin ranar, sai tayi mafarkin mijin nata, yana ce mata, kin yi mamakin abin da ya faru ga jikina ko?! tace kwarai ma kuwa? sai ya ce mata, hakan ya faru ne, sakamakon wata rana da kaninki suka yi fada da wani, da aka kawo karar gabana, sai a zuciyata, na raya cewa Allah yasa kanin matar nan nawa ya zama shine mai gaskiya. Kuma a al'amarin sai ya kasance shine mai gaskiya din. To shine dalilin faruwar haka ga jikina. To masu karatu kun ji fa, KAWAI SAKAMAKON YAJI A RANSHI CEWA, INAMA ACE MAKUSANCIN SHI YA KASANCE MAI GASKIYA!!!
*****

6. GASKIYA DOKIN KARFE:
Anyi wani sarki a zamanin da, wanda alkalinshi yana da wani Dan'uwa mumini mai gaskiya, da matarshi itama mumina kwarai. Sai wata rana sarkin ya nemi a samo mashi wani mutun amintacce, yana so zai tura shi wani gari domin wani aiki na musamman, sai ya bukaci Alkalin nan da ya samo mashi, sai alkalin nan yace yana ganin ba wanda ya dace a tura sai wannan Dan'uwan nashi. Dan haka sai ya kira shi, ya sanar dashi abin da sarki ya bukata, amma sai Dan'uwan nan nashi yaki amincewa, yace gaskiya ba zai iya barin matarshi ita kadai ba. 

Sai alkalin ya dage, yana ce mashi, sarki yana matukar so yaga kaine kaje wannan aiken, da ya dage dai akan yaje, sai Dan'uwan yace, to tunda ka takura sai nine zan yi wannan tafiya, to ya zama wajibi ka kula min da Matata, da kula da duk ayyukan da take bukata, har dawowata. Da alkali ya amince da haka, sai yayi shiri ya tafi aiken sarki, yayi sallama da matarshi, duk da cewa itama ba tayi farin ciki da wannan tafiya ba. 

Daga nan sai alkali ya rika zuwa gurin matar yana yi mata aike-aiken da ta bukata, kamar yadda Dan'uwanshi ya bukata, ana haka sai ya kamu da sonta, har ta kai ga ya neme ta da lalata, amma taki amincewa. Amma sai alkalin nan mai cike da son zuciya, yayi mata barazana da cewa, ko ta yarda da bukatarshi, ko kuma yaje yayi rantsuwa a gurin sarki yace tayi zina. 

Ita kuma duk da haka taki, tace yayi duk abin da zai iya yi, amma ita dai ba za ta taba sabawa Allah ba, kuma ba za ta ci amanar mijinta ba. Ganin haka sai alkalin nan yaji tsoro idan Dan'uwanshi ya dawo ya sami labarin abin da yayi niyyar yiwa matarshi. Dan haka sai ya tafi wajen sarki ya gaya mashi cewa matar Dan'uwanshi tayi zina, kuma ya bincika, ya tabbatar da hakan.

Shikenan sai sarki yace, to ai sai aje a jefe ta. Sai alkali ya tafi gurinta ya sanar mata cewa, naje na gayawa sarki, kuma yace a jefe ki, dan haka idan baki bani hadin kai ba, to zan yi kokari in ga cewa an jefe ki din ki bar duniya. Sai matar nan ta sake cewa, kayi duk abin da kaga za kayi, ni dai bazan taba amsawa mummunar bukatarka ba. Shikenan sai alkali ya hada mutane aka tafi jeji akayi dan rami aka zaunar da ita a ciki, sannan aka yi mata ruwan duwatsu a ka, har sai da yaga cewa ta mutu, sannan suka dawo gida. 
Can da tsakar dare, ashe da sauran numfashinta, sai ta farfado, ta girgije duwatsun kanta, ta fito waje, cikin tsananin azaba da wahala ta isa kofar wani gurin bautar wani malamin (fada) yahudu, ta fadi a nan sai bacci a wannan gurin, sai da safe malamin yahudun nan ya bude kofarshi sai yaga mata cikin rauni ta galabaita a kwance. Ya tambayeta abin da ya faru, da jin abin da ya faru, sai tausayinta ya kama shi, sai ya dauke ta zuwa cikin gurin bautar nan.

Malamin ya kasance mai kudi ne babba, sai ya dau nauyin maganin ta, ba dadewa sai duk raunukan jikinta suka warke tas. Dama yana da wani da karami, sai ya danka mata shi, tayi mashi tarbiya. Sannan kuma yana da wani bawa. Shi kuma bawan nan sai ya kamu da son ta, kuma ya bukaci shayar da sha'awarshi da ita, da barazanar cewa idan bata amsa bukatarshi ba, zai kashe ta. Tace mashi zai iya yin duk abin da yaso, amma ita ba zata taba aikata sabo ba. Sai bawan nan ya kashe yaron nan, sannan yaje ya gayawa malamin yahudun nan cewa, halaccin da ka yiwa matar nan ga abin da ta saka maka dashi (wato kashe Dan ka). 

Malamin ya kirawo ta ya tambayeta dangane da kisan danshi, ta gaya mashi gaskiyar abin da ya faru dangane da bawan nan, amma duk da haka, malamin bai yarda da ita ba, yace ba  za ta ci gaba da zama a gurinshi ba, sai ya dauko kudi Dirham ishirin ya bata, yace ta kama hanya ta bar mashi guri.
Haka matar nan ta bar gurinshi ta dauki hanya, ta shafe dare tana tafiya, har ta isa wani kauye kashegari da safe. 

A can ta iske wani mutumi a rataye bai karasa mutuwa ba, ta tambayi mutumin nan da yake a bakin mutuwa dalilin haka, yace mata kudi ake binshi har kimanin Dirhami ishirin, su kuma a al'adar garin idan bashin da ake bin mutun ya kai haka, to ana zuwa a rataye mutun ne har sai ya biya ko an biya mashi, ko ya mutu haka, da jin haka, sai ta bashi wannan kudin nata Dirhami ishirin, tace ya biya, sai aka kwanceshi aka sake shi, sai mutumin yace: lallai wannan Mata mai karimci kin ceci raina daga mutuwa. Dan haka na zabi in kasance tare dake a matsayin mai hidima a gareki. 

Suna tafiya sai suka isa bakin teku inda suka ga jiragen ruwa. Sai mutumin ya cewa matar jira a nan ina zuwa, zan je inyi wa masu jirgi aiki, domin in samo mana abin da zamu ci abinci, sai ya je gurin masu jirgi, ya tambaye su, wacce irin hajja ce (kaya) dasu a cikin jiragen su? Suka ce mashi a daya jirgin kayan yari da awarwaro ne masu kima, shi kuma dayan shine wanda suke hawa wajen tafiye-tafiyen su, sai yace musu zasu kai nawa kimar kayayyakinku, sai suka ce, gaskiya baza mu iya sanin kimarsu ba duka saboda darajarsu. 
Sai mutumin yace musu, ina da abun da yafi kayan nan naku kima, suka ce menene haka? Yace musu wata kyakkyawar baiwa ce yarinya mai kyawun da baku taba ganin irinshi ba. Sai suka bukaci ya sayar musu da ita, sai yace amma da farko sai daya ku ya je ya ganta, amma ta yanayin da baza ta fahimci cewa ita aka je gani ba, sannan sai azo a biya ni kudina. Sannan kuma idan na tafi sai kuje ku dauki abarku, sai suka yarda da haka, sai dayansu yaje ya gano ta, ya dawo ya gayawa 'yan uwanshi cewa, ai kuwa tayi kuma bai taba ganin mace mai kyawu irin ta ba. Sai wannan maci amanar mutun ya siyar musu da ita akan kudi Dirhami dubu goma (10,000) ya karbi kudin ya gudu abinshi. 

Da ya bace, sai suka je gurinta suka ce, ke yarinya baiwa, tashi ki shiga jirgi mu tafi, tace dan me? Suka ce, mun siye ki daga ubangijinki, sai tace ai ba shine mamallakina ba, ni ba baiwa bace. Suka ce, kada ki kawo mana wani wargi, kawai kizo mu tafi, in ba haka ba zamu dauke ki ta karfi. Dan haka sai ta bisu zuwa bakin ruwa. koda akaje hawan jirgi, sai duk suka rika kishi akan ta, kowa yana tunanin yadda zata zama mallakinshi, sakamakon haka, sai suka ki yarda da juna, sai suka yanke shawarar dora ta a jirgin kayan alatun nan ita kadai, su kuma dukkan su suka hau daya jirgin.

A yayin da jiragen suka isa tsakiyar ruwa, sai Allah Ya aiko da iska mai karfi, ta kifar da jirgin da suke ciki, duk suka nutse. Shi kuma jirgin da matar take ciki, sai iska ta kaishi wani tsibiri, da ita da kayan a ciki. A can taga wani gida mai kyawu, ga wata korama kusa dashi, da bishiyoyi masu kayan marmari masu kyawu a kewayenshi. Tace a ranta a nan zata zauna ta karasa rayuwarta, tana bautawa Allah tana ci daga wadannan 'ya'yan itatuwa ta sha daga ruwan koramar nan mai kyawu har karshen rayuwarta. 

Sai Allah Ya yiwa daya daga cikin Annabawa na wancan lokacin wahayi, cewa yaje ga sarkin nan (mai wancan alkalin na farko), ya sanar dashi cewa, a tsibiri kaza... akwai wata yarinya Mumina. ya debi duk mutanenshi suje su same ta, suyi ikrarin laifukansu da suka yi a baya, sannan su nemi yafiyarta, idan ta yafe musu, sannan Ni kuma zan gafarta musu. Idan ba haka ba, to Zan saukar musu da azaba mai radadi. Da samun wannan umarni daga Annabin Allah, sai sarkin nan ya hada jama’a suka tafi tsibirin nan, suka iske matar nan a can. 

Sai sarkin ya fara matsawa kusa da ita, cikin girmamawa, yace, wannan Alkalin ya gabatar min da matar Dan uwanshi, yace tayi zina, ni kuma ba tare da kwakkwaran bincike ba, kuma ba tare da kirawo sahihan shaidu ba, nasa aje a jefe ta, dan haka ina tsoro cewa nayi hukunci ba bisa adalci ba, ki roka min Allah Ya gafarta min. Sai tace zauna nan, Allah zai gafarta maka. Sai kuma mijinta ya matso gabanta (ita kuma ta shaida shi) sai yace, ina da Mata Mumina. sai sarki ya aika ni domin wani aiki a wani gari, duk da yake bamu so tafiyar ba, sai na barwa Dan'uwana alkali amanar ta, to da na dawo sai Dan uwan nawa ya gaya min cewa ta yi zina, an jefe ta, to shine nake jin tsoron ko ina da laifi a wannan alamari, dan haka ina neman ki nema min gafara a gurin Allah, tace kaima Allah Ya gafarta maka, zauna nan, ta zaunar dashi kusa da sarki. Sannan sai alkali shima yazo ya gafatar da laifin da yayi kuma ya nemi tayi mashi adu’a akan laifinshi, shima tace ya zauna anan Allah zai gafarta mashi. 

Sai kuma wannan fada (malamin yahudu) din shima yazo ya fadi nashi alamarin, shima tace dashi ya zauna a nan, Allah Zai gafatar maka. Daga shi kuma sai bawanshi, shima yazo ya gabatar da mummunan aikin da zaluncin da yayi, ya nemi tayi mashi adu’a ko ya sami rabauta, tace shima ya zauna a nan, Allah Yai maka gafara. Sai mutun na karshe wannan mutumin da ta ceta sakamakon bashi, da aka daureshi, shima yazo ya gafatar da mummunan aikinshi, kuma ya nemi tayi mishi adu’a dangane da rashin godiyar da ya nuna.

Daga nan sai Muminar matar nan ta dubi mijinta tace dashi, nice matarka, kuma duk abin da kaji dinnan, to nice duk hakan ya faru akai na. Kuma yanzu ni bani da sha'awar ko bukatar miji ina so ka dauki wannan jirgin dake cike da kayan yari, kaje dashi domin bukatuwarka, ni kuma ka barni a nan in karasa rayuwata wajen bautar Allah kawai. Ka ga dai yadda na wahala a hannun mutane. Ya yarda da haka, ya dauki kayan nan tare da sarki da sauran mutanen gari suka dawo cikin gari abinsu.
*****

To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo karshen Sashe na biyu  a wannan darasi namu na Akhlak, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na uku’, da wannan ni Hassan Adamu nake cewa ku huta lafiya. Limawa86@yahoo.com.


Littattafan da aka ciro wadannan Kissoshi sune:

1- Yek sad Maudhu’ 500 dastan (Sayyid Ali Akbar Sadakat)
2- Hayatu Al-Kulub (Allama Majlisi)
3- 100 moral stories (Akramullah Syed)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: