bayyinaat

Taska
Littafi
Shi'anci da Duniyar Gobe
Littafi ne mai muhimmanci matukar gaske da yake nuna mana karshen duniya da yadda zai kasance a mahangar addinai da suka gabata da suka hada da; Zardanci, Budanci, Hindanci, Yahudanci, Kiristanci. Sai kuma Musulunci; da ya hada da mazhabobinsa manya guda biyu na sunnanci da shi'anci da yadda kowanne yake ganin yadda karshen duniya zai kasance.
Gaskiya Kamar yadda Take
Wannan littafi ne mai muhimmanci matuka da ya dubi sifofin shi'a mabiya Ahlul-baiti (a.s) da halayensu da wurarensu da rayuwarsu domin sanin su waye 'yan shi'a. Makiya shi'a sun dade suna lika musu sharrori tsawon zamani, sai wannan malami mai daraja ya rubuta siffofin shi'a da akidunsu a dunkule kuma a saukake tare da gajercewa matukar gaske. Wannan lamari ya zama yankan hujja ga wanda yake son sanin 'yan shi'a daga harshensu.
Akidojin Imamiyya
Wannan littafi ne na Muhammad Ridha Muzaffar da ya kunshi aqidojin shi'a imamiyya kan Tauhidi, Annabci, Imamanci, Adalci, Alkiyama, domin ya kasance mai saukin riko a hannu, kuma mai saukin dubawa ga masu farawa don sanin yadda shi'a suke ganin mas'alolin aqida sabanin yadda makiyansu suka jingina musu. Akwai muhimmanci matuka ga kowane mai farawa da ya duba shi kafin daukar manyan litattafai.
Buhari da Muslim
Littafin Buhari da Muslim a Ma'auni yana bahasi ne kan ruwayoyi da suka shafi annabin rahama (s.a.w) da yadda aka cusa su a ruwayoyin musulmi alhalin sun saba wa koyarwar addini mai inganci da ta zo a cikin littafin Allah madaukaki da ya tsarkake annabinsa mai daraja da daukaka. An bi kowane fasali da ya yi maganar wani abu wanda ya saba wa Kur'ani game da siffofin annabin daraja da kamala domin tsarkake shi daga duk wata dauda da aka jingina masa amincin Allah ya tabbata gare shi.
Yadda ake Salla
Wannan littafi ne mai muhimmanci matukar gaske kan lamarin yadda ake yin salla da yake koyar da alwala da salla cikin hotuna don saukaka wa yara da manya sanin yadda ake yin su bisa koyarwar mazhabin Ahlul-baiti masu daraja da daukaka (a.s). Bibiyar littafin da koyarwarsa lamari ne mai muhimmanci matukar gaske ga wanda ya duba shi domin sanin yadda yara da manya zasu kiyaye dokokin mafi girman ibada a wurin ubangijinsu.
Rayuwar Ma'aurata
Littafi ne mai muhimmanci matukar gaske wurin zana mana yadda ya kamata rayuwarmu ta aure ta kasance. Ya fara da bincike kan halittar namiji da mace, sai kuma bahasin rayuwar mata a al'ummu, da kuma bincike kan auren mace sama da daya a al'ummu da addinai, sannan ya gangaro zuwa rayuwar samartaka da zabar abokan rayuwar aure. Sai shafin rayuwarmu mai muhimmanci da ya hada rayuwar zaman aure, siffofin ma'aurata, hukunce-hukunce, da sauransu. Daga karshe ya rufe da bahasosin sabanin ma'aurata da rabuwarsu.
1