bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      00:24:06
Mun kudiri aniyar zabo Kissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan kissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.
Lambar Labari: 102
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. 
Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Kur’an: Al-Kalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Kissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan kissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. KOWA ANA YI MASA JARABAWA A FAGENSHI NE!!:
An taba yin wani malamin Akhlak (koyar da kyawawan dabi'u) babban gaske, domin yana da dalibai sama da dubu da suke sauraren darussanshi na akhlak kuma suna anfanuwa. Amma saidai Kash!!! shi kuma sai aka jarabashi da shaidaniyar Mata, domin matar nan tashi, ta kasance mai tsananin Tsiwa da Bala'i, kuma kullum abin sai gabayake yi, shi yasa ma wannan malamin kullum idan dalibanshi sunzo gaishe shi kafin a fara karatu, sai ya rika kokarin saurin fitowa daga gidan saboda kada su fahimci halin da yake ciki, to amma yau da gobe taki wasa, sai da daliban suka lura da abin da yake kokarin boye musu. Sai wata rana wani daga cikin daliban yake cewa malamin, 
"Allah Ya gafarta malam, ya kake azabtuwa haka ai ina ga da ka sawwake mata, ai sai ka huta"!! Sai malamin yake ce mashi: "Hakane amma idan nayi haka, wato idan na sake ta, to cikin biyu za ayi daya: ko taje ta auri wani shima ya dandana wannan azabar da nake sha, ko kuma taki auruwa ta shiga cikin wani hali na matsi da takura, NI KUMA DUKAN BIYUN NE BANA SO, shi yasa a gurina yafi in cigaba da jure halinta, dan kada cutarwarta isa ga wani koda kuwa ga kanta ne."
*****

2. SAHIHIN TUBA:
wata rana Imam Musa Al-kazim Alaihissalam zai wuce ta kofar gidan wani mai kudi shagalalle mai suna Bishr Hafiy a garin Baghdad. sai Imam yaji kide-kide da hayaniyar alamun raye-raye a gidan wannan mutumin, daidai lokacin da Imam ya iso saitin kofar gidan, sai ga wata mai khidimar gidan ta fito domin zubar da shara, sai Imam ya tambaye ta kamar haka: "ya ke baiwar Allah shin mai gidan nan 'yantacce ne, ko kuwa Bawa ne?." sai tace: "'yantacce ne". sai Imam yace: "lallai kin fadi gaskiya, Dan da Bawa ne, to da yaji tsoron Ubangijinshi." shikenan sai ta koma gida abinta, da ta shiga sai ta iske Bishr a gaban shimfidar liyafa (abinci iri-iri) ga giya nan kala-kala, sai ya tambaye ta dalilin dadewarta, sai ta gaya mashi ga Wanda ya tsayar da ita kuma ga abin da ya gaya mata. jin wannan magana ta ma'asumi, sai tayi mashi tasiri, sai daga bakin shimfidar nan, kafarshi ko takalmi babu wato HAFIYAN, sai ya fito waje a dimauce, yabi inda Imam (AS) ya nufa, har ya tarar dashi, yana mai yin KUKA, NADAMA da NEMAN UZIRI, akan sabon da yake yi, a karshe dai ya karbi tuba a hannun Imam (AS). to tun daga lokacin, sai ya shagaltu da yiwa Allah biyayya, ya zama Zahidi kuma A'rifi, har karshen rayuwarshi, dan har sai da kasance cikin manya-manyan A'rifai na Karni na Uku. Allah Ya gafarta mana kuma Yasa mu dace da Tuba ingantacce.
*****


3. SAKAMAKON CEWA 'ALHAMDULILLAH'...:
 Abul Hasan Sara Sakati yana daga cikin A'rifan Karni na uku, ya kasance kuma Dan kasuwa, wato yana da shago a Wata kasuwar garin Bagadada, sai Wata rana da dare wuta (gobara) ta kama a wannan kasuwar da shagonshi yake, sai ya fito cikin hanzari ya nufi kasuwar, sai ya hadu da wani a hanya, sai mutumin yake gaya mashi, shagonka bai kone ba. jin haka sai yace 'Alhamdulillah', yana fadar haka kuma sai ya farga cewa, shagunan mutane fa sun kone, amma Shi yace alhamdlillah saboda ban da nashi! ai tun daga wannan lokaci ya fara ISTIGFARI akan fadar Alhamdulillah sai da yayi shekaru Talatin (30) yana yin Istigfari akan wannan abu da yayi.
*****




4. YA MAI SUTURCE AIBUKA!
An taba yin fari (karancin ruwa) a wani gari a Iraki a zamanin da can. wadda mutanen yankin suka yi ta rokon ruwa amma sai ba a sami ijaba (amsawa) ba, sunyi addu'o'in rokon ruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma ba a dace ba, suka fito da yara da dabbobi suna kuka, amma duk ba a dace ba. Akwai wani malami bawan Allah kwarai, har da shi a addu'o'in amma, ba labari. Sai malamin nan ya koma dakinshi yana ta kuka yana yabon Allah da harshen bayin Allah ma'asumai. Ana haka bayan sallah, ya dan kwanta sai yayi mafarki da wani bawan Allah mai tsarki, ya gaya mashi cewa: suje kauye kaza.. akwai wani makiyayi a can mai suna kaza.., su same shi, suce ance ya roka musu ruwan sama. Sai ya tashi, sai yaga ai mafarki ne, sai ya koma baccinshi, sai ya kuma ganin hakan a mafarkin, sai ya kuma tashi dai, sai ya kuma gani cewa mafarkine sai ya kuma komawa baccinshi, har dai sau uku, a karshe dai ya tashi ya sanar da wasu manyan mutanen garin, sai suka zabi wasu kadan daga cikinsu, suka nufi waccan kauye da aka yiwa malamin nan ishara dashi. da suka isa kauye, suka sami mutumin nan, ya fito da dabbobinshi zai tafi kiwo, suka tsayar dashi suka ce yayi musu addu’ar samin ruwa, yace: shi a wa?! suka dai takura shi, sai yace to, ni dai na san ba kowa bane ni, amma tunda kun takura, bari nayi muku, sai ya daga hannunshi yayi musu addu’a ga Allah Subhanahu wa Ta'ala, sauke hannunshi ke da wuya, sai hadari ya fara haduwa, sai ga ruwa, har mutanen nan suka jike, kafin su Sami mafaka.
To anyi haka, sai kuma mutanen nan suka dame shi da cewa, dan Allah ya gaya musu, me yake yi haka, har ya taka wannan matsayi babba? yace kai mutanen nan kun ganni dai kiwo zan tafi kuka tare ni ko?! to ni dai daga kiwon nan ba abin da nake yi, sai wajuba da suka hau kaina nake kokarin saukewa, dan hatta ko nafila bana samun yi, saboda shagaltuwa da kiwona.
suka dai takura shi, suka ce sudai basu gamsu ba, kodai ya boye musu wani abu.
A karshe dai yace, to, shi dai abinda zai iya gaya musu kenan, sai kuma wani abu daya da zai iya tunawa dashi, wadda yana ganin ba wani abu bane babba. Abin kuwa shine: Matarshi ta farko wadda ta rasu, lokacin da ya aure ta, koda aka kawo ta, tun daga daren farko sai tayi ta mashi kuka ta kunshe a kusurwar daki tana ta kuka, nayi ta rarrashinta, ina cewa 'ba gani ba ai na isheki dauke kewa, inma kina ganin har yanzu baki shirya rabuwa da gidanku ba, to ki koma ki zauna tare da iyayen ki, ni sai na rika zuwa gurinki', nayi-nayi dai in rarrasheta amma taki daina kukan, a karshe dai tace: duk abin da kake fadi ba sune matsala taba, matsala shine: "Nazo gidan ka ne da ciki Wata uku, kuma ka san idan iyayena suka ji kasha ni za su yi kamar yadda ka sani a al'adarmu". hakan yasa na boye maka, kuma yanzu ban san yadda zanyi ba. Sai nace Mata indai wannan ne tayi shiru, nayi Mata alkawari muddin tana raye babu Wanda zai sani, kawai ta tubarwa Allah, ni kuma zan ci gaba da zama da ita a mata ta, da kulawa, har ta haihu, kuma zan riki dan kamar nawa, kuma bana so ta gayawa koda yaron/yarinyar da zata haifa cewa ni ba ubanshi/ta bane.
Haka muka yi, kai saboda kada mutanen garin su fahimci wani abu misali su ga ta haihu da wuri, sai na sa ta hada mana kayanmu mu bar garin, sai na gayawa makusantana cewa zamu je wani gari ci' rani, dan haka a yafe mu, sai sun ganmu. haka muka bar garin nan, muka tafi can wani garin da ba a San mu ba, ta haihu a can, har yaro yayi wayo. bayan 'yan shekaru muka dawo. ba dadewa da dawowar mu, Allah Ya yiwa yaron rasuwa.
To kunji abin da nasan nayi, kuma nima ina rokon ku, iya ku dinnan, da ku bar wannan abu a ranku, kar ku gayawa kowa, har sai bayan na koma ga ubangiji na. Allah Ya dada suturce mana aibukanmu, Ameen.
*****

5. AIKIN ALKHAIRI BAYA GUSHEWA HAKA...:
An taba yin wani mutumi mai arziki da ya rika yiwa mabukata hidima da dukiyarshi, bayan Allah Yayi mashi  rasuwa, sai matar sa ta ci gaba da yiwa mabukata hidima da dukiyar da ya bari. to mutumin ya bar Da karami, bayan da yaro yayi girma, ya fara fita sai ya zamana duk inda yaron nan yaje a garin nasu sai mutane suyi ta sa mashi albarka, suna yiwa mahaifinshi addu'ar alkhairi da Rahma. Sai wata rana yaron nan bayan ya zama saurayi, yake tambayar mahaifiyarshi, wai meye dalilin da yasa duk inda naje sai mutane suyi ta yi min addu'a tare da mahaifina?, Sai mahaifiyar tashi tace mashi: Mahaifinka ya kasance mumini mai tsoron Allah, kuma Allah Yayi mashi arziki, amma sai ya rika yin hidima wa mabukata da dukiyar tashi, ni kuma da ya rasu, sai na ci gaba da hakan, har na karar da dukiyar. Sai yaron yace ya abin sona (mahaifiyata)! marigayi mahaifina ya samu lada dangane da wancan aiki mai kyau da yayi da dukiyarshi, amma ke baki da ikon yin abin da kika yi da ita, dan haka ke saidai ki sami fushin Allah da abin da kika yi. sai mahaifiyar ta tambayeshi , me kake nufi da haka Dana? Sai Dan yace, mahaifina ya bayar da dukiyarshi ne, amma ke dukiyar wani kika bayar (wato nufinshi dukiyarshi 'Dan'). Sai mahaifiyar tace gaskiya ne Dana!. amma nayi tunanin cewa ne baza ka damu ba da hakan, wato na dauka zaka amince da abin da nayi ne, wato na dauka zaka halatta min dukiyarka ne. Sai Dan yace nayi hakan yanzu, wato na halatta miki abin da kika yi da dukiyar tawa, to yanzu akwai saura ne? in yaso sai inyi jari da su ko Allah zai sa musu albarka sai kiga muma munyi arzikin! sai tace ina da 'Dinar dari', sai Dan yace, in Allah Yayi musu albarka sai kiga sun yawaita. sai ya karba ya fita domin nema da wadannan kudi a matsayin jari. A kan hanyarshi ta fita zuwa nema, sai ya iske wata gawa ta wani mutun da yaga alamu a fuskar shi, alama ta mumini. Sai yayi tunanin amfani da kudin nan nashi na jari, domin shirya gawar nan da yi mata sutura har zuwa sallah da bisnewa, haka kuwa yayi, wadda a karshe, yaga saura Dirham ishirin suka yi saura a hannunshi, sai yace Allah Ya yiwa wadannan albarka. Sai ya kara gaba abinshi. Yana ci gaba sai ya hadu da wani mutun, mutumin ya tambaye shi, Ina zuwa, yaro yace zanje neman halal da albarkar Allah. Sai ya tambaye shi nawa ne yake dasu a matsayin jari? yaro yace masa Dirham ishirin, sai mutumin yace, Me 'yan wadannan kudin zasu yi maka a matsayin jari?, sai yaron yace, Idan Allah Yayi musu albarka, sai kaga sun yawaita. sai mutumin yace haka ne yaro ka fadi gaskiya. To amma ina so kayi duk abin da zance maka, amma da sharadi daya, sharadin kuwa shine, duk abin da ka samu, to zamu raba shi daidai. Yaro ya yarda da haka. Sai mutumin ya gaya mashi, akan wannan hanyar da zaka bi zaka iske wani gida a gabanka, mai gidan zai gayyace ka bakunta zuwa gidanshi, to ka amsa gayyatarshi, kuma a yayin da mai hidimar gidan zai kawo muku abinci, zaizo tare da wata mage baka a hannunshi, to ka tambayeshi ya siyar maka da ita, zai ki da farko amma ka takura, a karshe zai yarda ya siyar maka da ita akan Dirhami ishirin (wato duka kudinnan naka), to lallai ka biya hakan, ka karbi magen. daga nan sai ka yanka magen ka kona ta, sai ka cire kwakwalwarta ka kulle, idan ka kulle tokar kwakwalwar magen nan a cikin kyalle ko wani abin, sai ka ci gaba zuwa wani birni. Za ka samu sarkin garin ya makance. Ka gayawa mutanenshi cewa zaka yi mashi magani. Kada ka tsorata da ganin gawawwakin wadanda sarkin yasa aka kashe sakamakon gazawa wajen yi mashi magani. Zaka iya sanya duk farashin da kake bukata  akan maganin da zaka yi mashi. A ranar farko sai kayi amfani da Mishi (tsinken sa kwalli), sai ka dangwali wannan tokar kwakwalwar magen, sai ka sa a idon sarkin kamar kwalli, zai fara jin sauki, kuma zai bukaci da yawa, to kada ka bashi, kawai ka kuma sanya mashi da mishin nan kamar na farko, a kashegari, a rana ta uku ma kayi haka, zai warke duka. Shikenan Yaro ya tafi ya fara isa gidan farko, ya sayi mage (kyanwa), yayi duk abin da aka gaya mashi, ya nufi wancan birni, ya iske sarki, ya fara magani kamar yadda aka umarce shi. Tun a rana ta farko da ya sanyawa sarki magani, sarki ya fara jin sauki, zuwa rana ta uku, sarki ya warke tas, ganin shi ya dawo kamar baiyi makaranta ba.
Sarki ya rungume yaro yace, kayi min babban taimako, yanzu saura nine zan saka maka. Ka dawo min da masarautata gareni. Sakamakon haka na baka 'yata a matsayin mata, na aura maka ita. Sai yaron yace, Mahaifiyata tana raye kuma bazan iya rabuwa da ita ba. Sarki ya aura masa ita, kuma yace, zaka iya zama har iya rayuwarka a wannan masarauta, kuma in kana so zaka iya komawa wajen mahaifiyarka, tare da matar ka (wato Gimbiya). sai yaro ya zauna har tsawon shekara daya tare da sarki cikin girmamawa da karimci, sannan ya fari shirye-shiryen tafiya. Sarki ya bashi: dukiya, kaya, rakuma, shanu da tumaki masu yawa. Yaro ya hada duka kaya tare da matarshi ya dau hanya, sai ya biya ta gurin mutumin da ya gaya mashi yadda ya warkar da sarki. Ya sami mutumin a gurin kuwa, da ganin yaron kuwa mutumin yace, kai yaro ya baka cika alkawari ba? sai yaro yace, da farko ina rokon ka da ka shafe min abubuwan da nayi amfani dasu a yayin da na zauna a can gurin sarkin tsawon shekara. Sannan kuma duk wani abu da na samo ga su nan tare dani, sai ka dauki rabinsu. Yaro ya raba dukkan dukiya biyu, yace mutumin ya zaba, sai mutumin yace, yaro baka yi adalci ba. Yaro yace kamar yaya fa? Sai mutumin yace wannan matar ma ai tana cikin abubuwan da ka samo. yaro yace hakane kana da gaskiya. Dan haka, ka dauki dukkan dukiyar, sai ka bar min Matar. sai mutumin yace, a'a! itama rabinta nake bukata. Sai yaro ya bukaci Zarto, ya dora a kan ta zai raba ya bashi, sai mutumin yace: Yanzu ka cika alkawari da kuma maganarka. Wannan matar da dukkan dukiyar nan ka rike sun zama naka, ka tafi da kayanka, bana bukatar komai daga ciki. Ni dama Mala'ika ne, Allah Ya aiko ni, in baka Lada daga cikin ladan aikin alkhairin da kayi ga Gawar nan da ka iske a hanya lokacin da ka fito daga garinku.
*****


6. MACE MAI KAMAR MAZA:
Ummu salim matar Abu Dalha ansari, ta kasance daga cikin mata madaukaka na Bani hashim. lokacin da Abu dalha ya nemi aurenta, sai tace dashi: ta wata fuskar kai mutun ne da ka cancanci a aura, amma saidai kash! kai ba musulmi bane, ni kuma musulma ce, dan haka idan zaka musulunta, na yarje maka da musuluntar ka ta zama a matsayin sadakina. Bayan musuluntar Abu dalha, ya kasance daga cikin manyan sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa alihi wa sallam). A yakin Uhud ya kasance cikin wadanda suka tsaya dan kare Ma'aikin Allah (S.A.W.A.), idan aka yo harbi yana tura kirjinshi gaban Ma'aikin Allah (S.A.W.A.), yana cewa: kafin harbi ya isa ga Manzan Allah (S.A.W.A.), to ya fara fasa kirjina tukun. Abu dalha ya kasance yana da wani Da (yaro) da yake matukar son shi kwarai. Sai wata rana yaron ya kamu da rashin lafiya. Ummu salim wacce tana daga cikin madaukakan matan musulmi, da ta lura cewa kamar cutar yaronsu ta ajali ce, sai kawai ta kirkiri wani sako, ta baiwa mijinta (Abu dalha) ya kaiwa Ma'aikin Allah (sallallahu alaihi wa alihi). bayan fitarshi zuwa wajen aiken, sai Allah Ya yiwa yaron cikawa (mutuwa). sai Ummu salim ta lullibe shi da mayafi, ta dauke shi ta kai shi can karshen kusurwar daki ta ajiyeshi. Sannan tayi sauri ta dora abinci, ya dahu ta sauke, sai kuma ta shiga wanka, ta fito tayi ado, ta yadda zata ja hankalin mijinta. Da abu dalha ya dawo daga gurin Ma'aikin Allah (S.A.W.A.), sai ya tambayi halin (jikin) yaro, sai tace mashi yana can a kwance. sai ya bukaci abinci, tayi sauri ta kawo suka zauna suka ci tare, bayan cin abinci kuma TA GABATAR MASA DA KANTA GARESHI, bayan ya nutsu sai Ummu salim tace: a 'yan wasu lukuta akwai amana a hannu na, amma yau na mayarwa da mai ita (amana), da fatan ba zaka damu da hakan ba? sai Abu dalha yace: meye na damuwa dan kin sauke nauyin da ya hau kanki! sai Ummu salim tace: Dama abin da nake so in sanar da kai shine, Dan (yaron) ka, amanar Allah ce a hannunka, to yau mai abu Ya karbi amanarShi.

Sai Abu dalha cikin dakiya da nutsuwa, yace: Nine ya kamata in sami wannan dakiya (Istikama) fiye da ke mahaifiyar wannan yaro, dan haka babu bata lokaci sai ya tashi yaje yayi wanka, sannan yazo yayi sallah Raka'a biyu, sai ya tafi gurin Ma'aikin Allah (S.A.W.A.), ya bashi labarin mutuwar Danshi, sannan ya gaya mashi irin aikin da Ummu salim tayi (wato halayen da ta nuna na juriya da dakiya da kwantar da hankalin mijinta). Sai Manzan Allah (sallallahu alaihi wa Alihi) yace: Allah Ya sada ku da albarkar wannan rana, sannan kuma yace: Godiya ta tabbata ga Allah da nima ya azurta al'ummata da Mata irin Sa'biratu Bani Isra'ila (wata mata ce mumina a al'ummar bani isra'ila).
*****

To alhamdulillahi dan uwa mai karatu a nan ne muka kawo karshen Sashe na farko  a wannan darasi namu na Akhlak, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na biyu’, da wannan ni Hassan Adamu nake cewa ku huta lafiya. Limawa86@yahoo.com.

Littattafan da aka ciro wadannan Kissoshi sune:

1- Yek sad Maudhu’ 500 dastan (Sayyid Ali Akbar Sadakat)
2- Hayatu Al-Kulub (Allama Majlisi)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: