bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      00:31:03
Ina neman tsarin Ubangiji daga shaiɗan jefaffe (daga rahamar ubangiji, aljannar ni'ima ta tunani da ta rayuwa bakiɗaya duk an fitar da shi, tare da saukar fushin ubangiji a kan sa).
Lambar Labari: 103
A yau ne Allah ya nufe mu da fara kawo muku abinda muka daɗe mu na fatan samun damar farawa wanda shine asasin dukkan komai, wato fassarar ayoyin wannan mabuwayin littafin da Allah (SW) ya saukarwa Manzon sa Annabin Rahama Muhammad (SAW), bisa asasin fassarar da ta fito daga gidan annabta ta hanyar Manyan magabatan Malamai da marawaita ta cikin wannan mazhabin na gidan annabta mai tsarki.

Duk da cewa abinda za mu kawo tarjamar ayoyi ne ba tafsirin su ba kamar yadda muka ambata, sabida idan tafsiri za mu aiwatar da dukkanin ma'anar sa ya na buƙatar lokaci da dogon bahasin da kan iya ɗaukar shekaru masu yawa, domin cikin tarjamar al'ƙurani akwai ulum daban – daban, kuma kowane ilimi dole a bashi haƙƙin sa, misali cikin sa akwai bahasin irfani, falsafa, kalam, fiƙihu, aƙida, tarihi, tattalin arziƙi, siyasa zamantakeawar al'umma, tarbiyyar yara, zamantakeawar iyali, haƙƙoƙin mutane, haƙƙoƙin hukuma, rayuwar al'umma da sauran bahasosin da baza su ƙirgu ba. Duba da wannan ne ya sa mu ka ga lokaci ba zai bada dama mu yi fassara ba saidai tarjama a taƙaice, mu na fatan Allah ya bamu ikon yin tarjama a nan gaba idan mu na raye ko kuma ya gadar mana da waɗanda za su iya ɗorawa kan inda mu ka gaza.

A nan ne mu ka ga kawai bari mu ɗan yi amfani da wannan ɗan lokacin da Allah ya bamu domin kawo tarjamar ayoyin wannan littafi mai girma a taƙaice.

Za mu fara da bbabar sura ma daraja ta farko cikin jerin surorin al'ƙurani mai girma wato suratul fatiha, wacce ake kiran ta da babar al'ƙurani wacce kullum mutane ke karantawa kullum dare da rana safe da yamma, sannan mu gangaro zuwa ga gajerun surorin da ke ƙarshen sa muna yo sama (farawa daga ƙasa zuwa sama) sabida su ne surorin da aka fi yawan karanata musamman cikin ibadu, muna son yaran mu da matan mu kai har ma da mu baki ɗaya mu san ainihin abinda mu ke faɗa yayin karanta waɗannan surori yayin ibadu da sauran ayuuka, har zuwa lokacin da za mu samar da tafsirin wannan littafi bayan kammala tarjamar sa in Allah ya raya mu.

أعوذبالله من الشيطان الرجيم

Ina neman tsarin Ubangiji daga shaiɗan jefaffe (daga rahamar ubangiji, aljannar ni'ima ta tunani da ta rayuwa bakiɗaya duk an fitar da shi, tare da saukar fushin ubangiji a kan sa).

Fassara (ƙarin Bayani)

Duk sanda muka ambaci shaiɗan da yawan mutane na kallon iblis ne kawai, su na manta cewa yana da wakilai da yawa, a ko ina akwai su akwai na mutane, al'janu, mala'iku, duniyar arwah, duniyar asma'a (kamar mai neman Allah (SW) daga dhalaal, ko fushin sa da sauran su), kuma dukkanin su shaiɗan ne, sabida haka shaiɗan mataki – mataki ne, hatta a mutumin shi da kansa, domin shaiɗan ɗin mutum na iya zame masa kansa da kansa, dukiyar sa, iyalin sa, ɗan sa domin duk su kan iya hana mutum fahimta ko taimakon gaskiya da bautar Allah ko bin sa, a duniyar yau shaiɗan kan iya zamewa mutum wayar sa ko computer sa, ya danganta da yadda ya iya sarrafa kayan aikin sa domin bin Allah yadda ya kamata, kamar yadda duk waɗancen abubuwan kan iya zamewa mutum shiryar sa, shaiɗan kan iya zowa mutum ta hagu ko dama, idan ta haƙu ne kamar ya sanya shi aikata manya laifuka irin su sata, shan giya, zina da sauran su, ta dama kuma shine kamar: mutum ne zai yi aikin alheri, amman matuƙar ba amfanin sa a ciki ba zai yi ba, Allah ya kare mu!!

*_Ibrahim Muhammad Sa'id_*

*whatsApp, Telegram, Viber, etc*

_+2348068985568_

Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

Ibraheemsaeedkano@yahoo.com

*HAIDAR CENTER*


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: