bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      00:40:22
A muslunci, kalmar aure an fi alaqanta ta da kalmar 'Nikah' wato saduwa tsakanin mace da namiji, amma a shari’a Kalmar aure tana nufin yarjejeniya (ta saduwa) tsakanin namiji da mace wanda hakan ke halatta saduwa tsakaninsu a wajen Allah (S.W.T) da kuma al’umma gaba xaya.
Lambar Labari: 105
A muslunci, kalmar aure an fi alaqanta ta da kalmar 'Nikah' wato saduwa tsakanin mace da namiji, amma a shari’a Kalmar aure tana nufin yarjejeniya (ta saduwa) tsakanin namiji da mace wanda hakan ke halatta saduwa tsakaninsu a wajen Allah (S.W.T) da kuma al’umma gaba xaya. Xaya hanyar da ta yi saura wacce ke halatta saduwa tsakanin mace da namiji, ita ce hanyar siyo baiwa mace, amma maganar mallakar baiwa ba ita ce maganar da muka bawa qarfi a cikin wannan littafin ba.
Aure na da rukunai da hukunce-hukunce kamar haka:-rukunan aure sun haxa da yarjejeniya da kuma rashin samuwar xaya daga cikin abubuwan da kan vata auren. Amma hukunce-hukuncensa sun haxa da dokoki da sharuxxa ko yarjejeniyar dake tattare da auren. Da sannu taqaitaccen bayani zai biyo baya dangane da wasu daga cikin dokokin aure kamar: Saki, Idda, rantsuwar qin takar mace, rantsuwar qin ubantakar xa ko`ya (korewa ko musanta zama uban xa ko ‘ya), rantsuwar saki da gado.

1. RUKUNAN AURE
Aure yana da wasu rukunai, a wajen Shi’a guda biyu ne, a wajen Malikawa da Hannafawa guda uku ne, a wajen Hambalawa da Shafi’awa kuma guda hudu ne. Duk mazhabobin nan sun haxu a kan rukunai biyu na farko wato 'siga' (wato kalmar xaura aure) da kuma ma Ma'aurata.

A. Siga (Kalmar Xaura Aure)
Aure yana halatta ta hanyar yarjejeniya wato bayyanawa 'nema' da kuma 'karva' yarda. Mace kan furta neman qulla aure da namiji 'na aurar maka da kaina' shi kuma ya bayyana amincewarsa ta ya karve ta a matsayin matarsa. 'na aura ko na karvi auren..', Daga nan ta zama matarsa.
Mazhabobin nan sun sava a kan irin furucin  da  ya zama wajibi mace ta yi a wajen  qulla  aure,   Shafi’i  da  Hambuli  sun  tafi  a kan   cewar idan mace ta ce:  'na  aure  ka' 'wato 'ankahtu ka ko zauwajtuka' ya  wadatar.  maliki   ya  tafi  kan cewa: Idan tantance sadakin da za a ba matar  to za ta iya  cewa  'Na mallaka maka kai na'.  Shi’a kuwa sun qi yarda da kalmar 'mallaka' amma sun qara da 'Na miqa kaina don jin daxinka'.  Mazhabar Hanafiyya kuwa ta abayar da ‘yancin yin kowane furuci ko da kuwa bai tafi kai tsaye ba.
Amma gaba xayan mazahabobin sun tafi a kan cewa namiji na da damar yin amfani da duk kalmomin da ya ga dama, waxanda suke nuna amincewarsa.
Mazahabar Hanbaliya, Malikiya da Shi’a sun tafi a kan cewa jimlar da za a yi amfani da ita, lalle ne ta zama tana qunshe da ma'anar qulla aure kuma tana nuna cewa yanzu aka qulla auren, wato da (sigar fararwa ko insha'i a larabci) kuma me xorewa, wato (perfect tense). 
Hanafi ya tafi a kan yin amfani da jimla me nuna auren ya faru a yanzu, matuqar tana nufin abin da zai zo nan gaba, kar dai jumlar ta zama irin wacce ke nuni a kan yin alkawarin aure . A wajen shafi'iyya kuwa, sun tafi a kan cewar za a iya yin amfani da sigar ko jumlar da ke nuni a kan  yanzu matuqar ba za a yiwa jimalar fassarar da nuna alqawarin yin aure ba, ta hanya qarawa da kalmar 'yanzu' a cikin sigar.  
Dukkanin mazhabobin sun tafi a kan cewa dole kalmar Nema da Karva ayi su a lokaci ko zama xaya. kuma ba dole ne sai furta Nema ya gabaci Karva ba in banda a wajen Hambaliyya.  Kuma waxanda suka san Larabci dole su furta da Larabci, ga waxanda ba su san Larabci ba, za su iya amfani da yarensu, amma sharadin shi ne ya yi daidai da ma’anarsa a Larabci. kurma kuwa sai ya yi nuni ko ishara.

B. Ma’aurata (Miji Da Mata)
Namiji da Mace dole su kuvuta daga dukkanin abubuwan da shari’a ta gindaya waxanda ke haramta auratayya a tsakaninsu. Kuma dole a tantance wanene mijin? kuma wacece matar? misali, idan waliyyin mace ya ce: 'na aura maka xayan `ya`yana mata biyu, ko na ba ka xayan `ya`yana mata biyu ka aura'. Sai namijin ya amince to auren bai yi ba.
kuma mace ba za ta auri namijin da ba tsaranta ba 'kufu'i'. Amma wannan maganar Shi’a sun xora ta a kan cewa namijin dole ya zama musulmi.  Amma Mazhabar sunna sun qara da cewa ba wai kawai dole ne ya zama musulmi ba, a a, dole ne su daidaitu har a sauran vangagarorin rayuwa, kamar `yanci da matsayi a cikin al'umma dss. Amma sun tafi a kan cewa namiji zai iya auran wacce take qasansa ta fannonin rayuwa.
Daidaituwa tana nufin daidaituwar matsayin ma’aurata wanda a haka ne ke sa su dace da juna, duk mazahabobin nan huxu sun tafi a kan haka sai xan banabancin da ba a rasawa. A wajen hannafi daidaituwa ta haxa da musulunci da asali (salsala) sana’a `yanci nagarta da arziqi, shafi’awa sun lissafo asali, addini, sana’a, hakama Hambalawa suka ce sai xan banbancin da ba arasa ba wanda shi ma na lafazi ne, malikawa sun lissafa nagarta da `yanci a matsayin abubuwan da ke hana ingancin aure. 

Kashi na biyu na nan tafe in Allah ya yadda.

*_Ibrahim Muhammad Sa'id_*
*whatsApp, Telegram, Viber, etc*
_+2348068985568_
Ibraheemsaeedkano@gmail.com, 
Ibraheemsaeedkano@yahoo.com

 
*HAIDAR CEN TER*

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: