bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      00:42:27
Duk da irin wannan matsayi da daukaka da take da shi bai sa ta gafala da ayyukan ibada da neman kusanci zuwa ga Allah ba, Wannan ya sa ta zama abar koyi ga dukkan Musulmi.
Lambar Labari: 106

 Kamar yanda muka sani Sayyida Fatima 'ya ce ga Fiyayyen Halitta Manzon Rahma (s.a.w). sannan mata ga shugaban mu'uminai, Imam Ali (a.s) kuma ita ce shugabar matan Duniya, uwa ga Samarin Aljanna Imam Hasan da Imam Husai (a.s) Kamar yanda hakan ya zo a cikin Hadisai ingantattu tsakanin makarantun Shi'a da Sunna. 

Duk da irin wannan matsayi da daukaka da take da shi bai sa ta gafala da ayyukan ibada da neman kusanci zuwa ga Allah ba, Wannan ya sa ta zama abar koyi ga dukkan Musulmi.

SAYYIDA  FATIMA A MATSAYIN 'YA:
Ta kasance mai biyayya ga mahaifanta kuma mai ji daga gare su mai sauraren su a duk umarni da hani,kuma mai kare mutuncin su. Ya zo cewa lokacin da mushirikan makka suka durawa Manzo (s.a.w) mahaifar Rakuma a baya yayin da yake Sallah ita ce ta zo ta dauke masa daga bayan sa mai tsarki. kuma ta kasance duk lokacin da kafirai suka cutar da shi takan tsayu wajan kare shi.
daga nan zamu fahimci kuma mu koyi girmama iyaye da kare mutuncinsu daga Rayuwar Sayyida Fatima (a.s).

   SAYYIDA FATIMA A MATSAYIN MATA:
Ta kasance mata ga Amirul-mu'uminina Ali (a.s). Rayuwar Auren su cike take da darussa da koyar wa ga Mu'uminai, ta kasance mai Hakuri da juriya a tsawon dukkan Rayuwar su ta yanda ba ta taba nema ko tambayar wani abu wanda mijin ta ba shi da shi, kuma tana karbar dukkan shawarar da ya zo mata da ita. 

  KARE MARTABAR MIJI
Sayyida ta kasance mai matukar muhimmantar da al'amarin mijin ta da kuma tsayuwa wajan neman hakkin sa, haka kuma bata dora masa nauyin abin da ba zai iya yi ba. Harma tana ce wa: "mafi muhimman cin jihadin mace ahi ne kula wa da mijin ta"don haka ta tsayu wajan taga ta kare martabar mijin ta. Har ma Imam Ali (a.s) yana cewa: "na rantse da Allah Fatima ba ta taba nuna min fushi ko dora min Abin da ba zan iya ba ko tilasta ni haka ni ma ban taba yi mata laifi ba kuma ba ta taba saba umar ni na ba, ko yaushe tana ya ye min damuwa."

 SAYYIDA FATIMA A MATSAYIN UWA:
Ta kasance Uwa mai jin kai da tausayi ga 'ya'yan ta sannan kuma mai matukara kula da tarbiyar su da tsftar su, takan ware lokaci a kullum wajan koya wa 'ya'yan ta Karatu musamman karatun kur'ani mai tsarki, wanda hakan ya sa har sai da diyan ta Hasan da Husain (a.s) suka haddace kur'ani, kai har ma da mai musu hidma ita ma ta tarbiyan tu ta kuma karantu a Hanun sayyida Fatima (a.s).  Sannan tana muhimamntar da tsaftar yaran ta ta yanda harma lokacin da take rashin lafiyar da ba ta tashi ba ba ta bar yiwa yaranta wanka ba. Sannan tana mbasu lokaci domin hutawa kuma tana wasa da 'ya'yan ta tana jansu a jika sosai da yanda ya zama sun shaku da ita matuka.


 SAYYIDA  DA MAKWABTA
Kula da halin da makwabta ke ciki da kuma kokarin war-ware musu matsalolinsu na da ga cikin muhimman abubu wan da Sayyida ta ba su muhimmanci a rayuwar ta;
 Ta kasance tana kulawa da hakkin makwabta matuka, ta yadda har ma ya shahara cewa tana fifita bukatun makwanta a kan nata. Ta kasance idan tana ibada cikin dare takan yawan mai-mai yiwa makwabta Adu'a tana mantawa da nata bukatun.

Dan ta Imam Hasan (a.s) yake tambayar ta cewa:"lokacin da ina yaro a wasu darare na juma'a idan na daga kai na na kan ga Babata a wajan ibadar ta tana Salla sannan acikin Ruku'u da sujjada
tana kiran suna yen mumina  tana musu Adu'a Amma ba ta roka wa kan ta komai,sai na tambaye ta:"Umma mai yasa ko yau she wasu kike wa Adu'a amma baki yiwa kanki?" Sai ta ba shi amsa da cewa:"ya dana ai ana fara gabatar da makwabta ne kafin Gida, su ake fara yiwa Adu'a sannan kai na". Da wannan zamu dauki darasi kuma mu koyi sadaukar wa da kula da hakkin makwab ta.

 TSAYUWAR TA WAJN KARE GASKIYA:

    Sayyida Fatima ta kasance mai tsayuwa ce wajen kare gaskiya da kuma fada da Zalunci a dukkan rayuwar ta tun lokacin rayuwar mahaifin ta (Manzon rahma) har zuwa lokacin da yabar duniya. haka kuma ta tsayuwa wajen kare wilaya lokacin  da 
 al'ummar musulmi suka juyawa wasiyar da manzon Allah(Saw) ya yi baya (na kasance war Imam Ali a matsayin Halifan sa a bayan sa ). Sai ya zama Sayyida Fatima ba ta tsaya ta zuba Ido ta bar Al'umma cikin bata ba; bayan sakifa (taron da wasu Sahabbai sukai suka Zabi Abubakar a matsayin Halifa ) ta rike hannuwan Imam Hasana da Imam Husaini tana zuwa gidajen Ansar da Muhajirun(Sahabban Annabi yan Asalin makka da madina) tana tunatar da su wasiyyar da manzo (S) ya yi masu da kuma bai'ar da suka yiwa Imam Ali (a.s)da kuma zantu kan Manzo (s.a.w) aka matsayin Imam Ali da Falalr sa da fifikon sa a kan sauran Sahabbai, kuma ta kasance tana yawan tuna musu alkawarin da suka yi na bin Ali (a.s)a bayan sa.
   
GUDUN DUNIYAR TA
Ta kasance mai tsan-tsaini da gudun duniya har haka ya sa komai ta mallaka tana iya ba da shi ga mabukaci ko da kuwa wannan abun ba ta da sama dashi. Ranar da za ta tare a dakin mijin ta sai mabukaci ya zo ya yi mata sallama ya kuma nemi taimako a wajan ta, sai ta dawo ta bawa wannan mabukacin rigar angwanci da ita daya ce a wajan ta. Ta kuma sa rigar da ba sabuwa ba a jikin ta,  Lokacin da labarin ya je wa Manzo (s.a.w) sai ya tambaye ta dalilin yin hakan. Sai ta ce: "ya Baba na na koyi wannan darasin ne a cikin kur'ani, in da Allah yake cewa:"ba za ku zama masu kyautatawa ba har sai kun ciyar (ko bayar) da abin da ku ka fi so".  
Suratu ali Imaran aya ta 92.

     SADAUKAR WAR TA

Sayyida Zahra'a(a.s) ta kasance mai sadaukar da duk abin da ta mallaka matukar mabukaci ya zo ya nemi tai makon a wajen ta. 
Babbab misali shi ne lokacin da diyan ta Hasan da Husain (a.s) su ka yi rashin lafiya sun yi Azumi na kwana Uku yayin da duk lokacin da suka zo yin buda baki sai wani mabukaci ya zo ya nemi taikamkon abinci a wajan su yayin da abincin da suka tanada na wannan lokacin ne kawai amma sai su ba shi duka har ya zama sun yi kwana uku ba tare da yin buda baki da abinci ba, wannan ya kai gayar sadaukar wa.
Haka kuma lokacin da za a kai ta dakin mijin ta bayan Aure tasanya sabuwar riga sai wani mabukaci ya zo neman taimako wajn su haka ta dauki wannan sabuwar rigar wadda ba ta da sama da ita ta ba shi sadaka.
A nan zamu fahimci gayar sadaukar wa da muhimmantar da al'amuran mutane, wanda wannan babban abin koyi ne a wajan mu 

        IBADARTA
 Sayyida Fatima (a.s) ta kasance mai yawan ibada da komawa zuwa ga Allah a cikin duk lamuran ta, ta kasan ce mai yawan karatun kur'ani ta yadda har mai mata hidma ta haddace  Kur'ani a wajen ta; tana muhimmantar da Yawan zikri ambaton Allah a ko wanne lokaci, sannan kullum tana raya daren ta da ibada musamman Salloli ta yadda har sai da kafar ta ta nuna alamun yanwan tsayuwa,haka kuma mafi yawan lokuta tana tashi da Azumi a cikin rane ku,ta kasance mai yawan Adua da munajati da kuma yi wa muminai adu'a musamman makwabta, Tana yawan fadin cewa:"makwabci sannan gida"

Wato duk lokacin da zatai Adu'a 
Takan fara yiwa makwabtan ta 
Sannan ta yiwa kanta .

Isma'il Hashim Ayyub
hashama101@gmail.com
Masdaro ri 
1-majma'ul bayan
2-biharul anwar
3-Usul-alkafi
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: