bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      00:53:55
Duk wani dan’adam zai iya yin aiki na gari ya kuma bawa wasu lada wadannan ayuukan wanda daga ciki akwai mahaifansa wadanda su ma zai iya ba su ladan wannan aikin kuma kari kan ladan da za’a ba su shi ma za’a ba shi makamancin wannan ladan ko ma a ba shi sama da haka.
Lambar Labari: 108
Yi wa Iyaye Aikin Lada

Shin Ya Hatta A Yi Wa Mahaifi Da Mahaifiya Wadanda Suke A Raye Ayyukan Alkhairi?

Shinfida 
Duk wani dan’adam zai iya yin aiki na gari ya kuma bawa wasu lada wadannan ayuukan wanda daga ciki akwai mahaifansa wadanda su ma zai iya ba su ladan wannan aikin kuma kari kan ladan da za’a ba su shi ma za’a ba shi makamancin wannan ladan ko ma a ba shi sama da haka.   

A wajen amsa wadannan tambayoyi guda biyu, zamu fara yin duba kan banbancin matsayin iyaye a mahanga ta imani, sannan mu yi Magana kan rawar da ‘ya’ya ke takawa wajen kyautata musu, kuma daga karshe za mu tuke kan cewa a fagen kyautata musu babu banbanci tskanin suna raye ko ba sa raye.
Kyautatawa mahaifi da mahaifiya na daga cikin umarnin da addinin musulunci ya wajbta a wajaje da dama ta yadda ya gwama yin biyayya ga Allah da kyautatawa iyaye.  Kuma hakika alkur’ani ya yi wasici mai yawa kan yi musu biyayya da kyautata musu da yi musu addu’ar neman gafara, kuma wannan ma ya zo da dama daga bakin annabawa (as)  
Sai da ya kamata mu gane cewa akwai banbanci tsakani iyaye salihai na gari masu bin tafarkin gaskiya da gyara masu tsoron Allah da suke kyautata tarbiyar ‘ya‘yayensu wadanda suke yin riko da hannayensu zuwa tafarki samun kamala da kuma iyayen da suka kauce wa gaskiya da shiriya. 
Dangane da kaso na farko na wadannan iyaye zamu iya cewa: " hakika da na gari na daga cikin rabutar mutum”  domin irin wannan yaron sakamakon aikinsa kaitsaye na koma wa zuwa mahaifan sa har ma ya zo a ruwaya cewa annabi (saw) yana cewa: "idan mumini ya mutu gaba dayan ayyukansa sun yanke in banda uku, sadaka mai gudana ko ilimi da ake yin amfani da shi ko yaro na gari da yake yi masa addu’a”. 
Kamar yadda aka rawaito daga annabi mafi girma (saw) ya ce: "ku nemi ilimin alkur’ani hakika a ranar alkiyama zai zo wa ma’abocinsa a cikin siffar saurayi, kyakkyawa mai kyakkyawan launi sai ya ce da shi ni ne al’kuranin da ka kasance kana bin dare da shi (ka hana kanka barci saboda shi) ka busar da makogoronka saboda shi ka busar da yawunka domin sa kuma na kwace maka hawayenka har zuwa inda yake cewa: ka yi bushara, sai a zo da hular sarauta a dora a kan sa sannan a ba shi aminci a hannunsa na dama da kuma shedar dauwama aljanna a hannunsa na hagu. Sannan a sa masa tufafi guda biyu masu kyau sannan ace da shi ka karanta  ka yi sama, duk lokacin da ya karanta aya sai ya yi sama martaba daya (haka zai yi ta yin sama martaba bayan martaba), sannan a sanya wa mahaifansa tufafi masu kyau kala biyu suma idan sun kasance muminai, sannan ace da su an saka muku da wannan ne saboda kun koya masa karatun kur’ani” . 
Hakika ya bayyana a sarari cewa ko da mutum bai yi nufin daba ladansa ga iyayensa ba to sakamakon aikinsa na zuwa gare su saboda lokacin sa suka bayar wajen tarbiyyar dansu (har ya zama na gari). 
Kaso na biyu: ya zama iyaye ba su da rawar da suka taka kan tarbiyyar yaro tarbiyya ta addini, ta yiyu ma su zama sun yi fito na fito kan yin imamninsa sai dai shi yaron na gari yana so ya bada kyuatar aikinsa gare su don ya temaka musu ya saukake musu al’amarinsu a wannan yanayin za mu iya sauwara fuskoki biyu: 
Ta daya: idana iyayen suka zama cewa ba su yi imani ba kuma sun sa yaron agaba don ganin sun hana shi bin tafarki madaidaici a irin wannan matsaya ya zama lalle ga yaron ya rarrabe tafarkinsa daga tafarkin iyayensa kamar yanda kur’ani ya ba da labarin annabi Ibrahim da babansa da kuma aikin babansa  Kuma wannan sheda ce mai kyau kan abin da ake Magana a kai ta yadda ya kasance yana nema masa gafara lokuta masu tsaho,  {amma lokacin da ta bayyana gare shi cewa shi makiyin Allah ne sai ya barranta daga gare shi hakika Ibrahim ya kasance mai yawan anbaton Allah mai kuma mai tsananin hakuri} . 
Don haka idan har iyaye suka zama makiyan Allah ta’ala da Manzo (saw) kuma wadanda suka kangare wa Allah addu’ar da ba za ta yi tasiri kan tsirinsu daga wuta ba, sai dai akwai wasu ruwayoyi da suke nuna cewa tare da haka addu’ar da da nema musu gafara na da wani nau’i na amfani ga iyayaensa kuma hakan na sa a saukaka musu azaba, ya zo a cikin lattafin durus na ibni abi Mansur ya ce na ce da Baban Hasan shin addu’a na anfanar da mamaci? Sai ya ce eh, ya kan kasance ma cikin tsanani sai a yalwata masa kuma ya kan zama wanda aka yi fushi da shi sai a yafe masa a yarda da shi sai na ce kuma ya san wanda ya yi masa addu’ar? Sai ya ce eh. Sai na ce: idan ya kasance daga cikin makiya ahlulbait fa? Sai ya ce wallahi wannan zai yi musu amfani sai a saukaka msu azaba.  
Na biyu: yanayi na biyu shi ne iyaye su kasance ba muminai ba amma kuma alokaci guda sa zama ba masu jayayya da kangara da kiyayya da muminai ba, kuma suna rayuwa ta dabi’a a tare da su kuma wandannan su suka fi yawa daga wasun muminai ta yanda ba sa ja- in-ja da muninai kai tsaye su dai kawai ba sa so ‘ya‘yansu su zama muminai, a irin wannan yanayi kur’ani mai girma yana Magana kan haka a inda yake cewa: {idan suka yi jayayya da kai a kan ka yi shirka da Allah bisa abin da ba kada ilimi a kai kar ka yi musu biyayya amma ka zauna da su a duniya cikin girmamawa}. 
Kuma an rawaito kan wannan lamarin daga mu’ammar dan khilad hakika ya ce: na ce da baban Hasan imam Ridha (as) shin na yiwa iyaye na addu’a idan suka kasance ba su san gaskiya ba? Sai ya ce: ka yi musu addu’a ka yi musu sadaka ko da kuwa suna raye ba su san gaskiya  ba, hakika Manzon Allah  (saw) yana cewa hakika Allah  ya aiko ni da rahama ba da ukuba ba”.  
Daga nan zamu ga cewa za a iya bada ladan ayyuka na gari ga irin wadannan nan iyaye kuma za’a iya yi musu addu’a da nema musu gafara da nema musu rahama wajen Allah Ta'ala mai karamci mai yawan kyauta. Hakika an rawaito daga imam Bakir (as) yana cewa: "addu’o’i guda biyar ba su da shamaki tsakaninsu da Allah mai girma da daukaka, - addu’ar sarki mai adalci da addu’ar wanda aka zalunta Allah  madaukakin sarki yana cewa na rantse sai na daukar maka fansa ko da bayan wani lokaci ne da addu’ar da na gari ga iyayaensa da addu’ar uba na gari ga dansa da addu’ar mumini ga dan’uwansa a boye sai ace masa kai ma za’a baka irin nasa.  Daga nan buri zuwa ga Allah  madaukaki ke karfafa kan cewa zai gafarta wa iyaye raunana a tunani da ba su iya motsawa ba zuwa tafarkin imani wannan kuma don albarkacin addu’ar ‘ya’yansu da kuma kyautar da ladan ayuukansu na gari zuwa gare su. 
Sai dai zai iya yiyuwa a aikawa iyaye da ma wasunsu ladan ayyuka na gari alhali suna raye? 
Sai mu ce hakika kyuatar da ladan ayyuka gare su bai takaitu da in ba sa raye ba ballantana ma ya hada da ko su na raye. Na’am ba zai yiyu a yiwa mutum mafi yawa daga cikin ibadu ba saboda sun wajaba a kansa kuma shi ya zama wajibi ya zo da su, ba wani ya zo masa da su ba, bisa misali ba zai yiyu a yiwa iyaye salla ko azumi na farilla ba alhali suna yare, amma idan sun mutu za’a iya yi musu.
Amma dangane da abubuwanda suke na mustahabbi akwai ruwayoyi masu yawa da zai yiyu a jingina da su wajen inganta bawa wani ladan ayyuka musamman ma iyaye wadanda suke suna da matsayi na musamman.
Hakika an rawaito cewa lokacin da aka tambayi imam sadik (as) kan mutumin da zai yiwa wani aikin hajji shin yana da wani abu daga lada? Sai ya ce wanda ya yiwa wani aikin hajji yana da ninkin ladan aikin hajji sau goma kuma za’a gafarta masa shi da babansa da babarsa da dansa da ‘yarsa da dan’uwansa da ‘yar’uwarsa da baffansa da gwaggonsa na bangare uwa da na uba hakika Allah  mai yalwatawa ne mai karamci.  Saboda haka ne za mu ga mahajjata a duk lokacin da suka kusa tafiya suna zuwa su yi dawafia maimaiko iyayensa da makusanta da abokai rayayyu da matattu.
A wata ruwaya ya zo daga imam sadik (as) kan abin da muke Magana ya bayyana cewa zai iya yiyuwa ballantana ma ya kwadaitar a kai:- a inda yake cewa: "me zai hana daya daga cikin ku ya yiwa iyayayensa rayayyu ko matattu biyayya, ya rika yin salla a maimaikon su ya rika yin sadaka don su ya yi hajji a maiamakon su, ya yi musu azumi sai ya zama aikin nan da ya yi musu shi ma yana da ladan dukkanin aikin sai Allah mai girma da nuwaya ya kara masa alkairi mai yawa saboda niyayyarsa da sadarwarsa.  
Ta hanyar wadanna bayanai ya tabbata a sarari cewa: yin dukkanin wadannan abubu (da aka yi tambaya a kai) ya inganta kuma ladan wannan aikin kamar yadda yake zowa iyaye da makusanta da makamantansu shi ma wanda ya yi ayikin an rabuta shi gare shi kuma wannan ba abu ne mai ban mamaki mai wahala a wajen mai tausayi mai jin kai ba.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: