bayyinaat

Published time: 09 ,April ,2018      01:07:38
Sannan kuma Alusi ya ambata a cikin tafsirinsa bayani mai tsawo domin kore takiyya da yin raddinta, zamu ambato su akunshe mu kuma bada amsa a kai:
Lambar Labari: 110
Takiyya  a  Musulunci

NA
Sheikh     muhammad    jawad    al-fadilul
Lankarani
FASSARA
Shafiu Haruna Sigau

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.
   Mas'alar  takiyya  tana daya daga cikin bahasosin  Alkur'ani, wanda ake kirgata daga cikin ka'idoji na Fikhu, kuma tana da rassa masu yawa, da ita ce ake sanin mabiyin Imamai kuma ta kasance shi'arinsu  da kuma alamarsu ta wani bangaren, tare da cewa ta wani bangaren daban kuma ta kasance hanya ce ta batanci a kansu. ta yanda a cikin littafan 'yan uwanmu (mabiya halifofin Sunna) ba su da cikakken bincike a kanta, da wurin yin ta da nau'ointa sai dai abin da ya zo cikin kalmomin Ash- shaikul A'a zam, da wadanda suka zo bayan sa, shi ya sa ya za ma wajibi yin bincike a kan ta (Takiyya) , da kuma al'amuran da suke da alaka da ita.
Dalilin kawai da ya sanya Amawa ke batanci ga mabiyan Imamai, shi ne rashin saninsu dangane da hakikar ta da kuma rashin kaiwar su zuwa asalin ta, kamar yanda wannan shi ne dalili na asali ga sauran bahasosi na aklak wanda ake samun matsala tsakaninmu da su, abin da ya zama wajibi shi ne yin tunani matukar tunani.
Abin da da ke bada mamaki shi ne malaman Ammawa  ba su kai ga hakikar takiyya ba ba su kuma saurara daga wannan bahasin mai zurfi ba cewa menene ya shahara tsakanin sauran jama'a, Amma sai suka yi ma na hujumi,  hujumina  jahilci da kiyayya ba tare da sun koma zuwa ga litattafanmu na kafa dalilan fikihu ba, wasu sashi daga cikinsu su ce tana (takiyya) daidai da karya, wasu kuma daga cikin su su ce tana daidai da munafinci, Amma ya ya zai zama munafinci da karya alhalin Alkur'ani na kira zuwa halascinta a musulunci yana kuma kawo mana labarin yanda Annabawa suka aikata ta?
Sannan kuma Alusi ya ambata a cikin tafsirinsa bayani mai tsawo domin kore takiyya da yin raddinta, zamu ambato su akunshe mu kuma bada amsa a kai:
1- Cewa kalmomin mabiya Imamai ta sha banban a wannan maudu in ta mahanga na hukuncin shari'a, wasu daga cikin su sun ce wajiba ce, wasu kuma sun tafi zuwa ga mustahabbancin ta, na uku kuma sun tafi zuwa ga halascin ta, wannan rashin matsaya dayan da suka kasa samu dalili ne na cewa maudu'in ba tabbatacce ne a wurinsu ba, kuma dalili ne dake nuna rashin ingantaccen dalilin su.
Amsa: su ba su san cewa a kan samu maudu'i guda wanda yakan inganta ya zamto yana da alaka da hukunce-hukunce maban-banta ba da bangarori masu yawa, takiyya ta kasu ta bangaren hukunci na takalifi zuwa ga hukunce-hukunce biyar da sannu cikakken bayanin zai zo, in Allah madaukaki ya so.
2 - Cewa a cikin kalmomin Imamai kamar Imam Ali (A.S) da 'ya 'yansa, ya zo cewa akwai abubuwan dake sanya takiyya ta zamto haram bama maganar mustahabbancin ta ba da falalar ta saboda fadin sa (A.S): Alamar imani shine fifita  gaskiya ta yanda zai cutar da kai a kan karya cewa idan ka yi karya ba za ka cutuba.
Sannan yana kara cewa:  Ni wallahi da zan hadu da wani dake da sanin dukkanin kasa gaba dayan ta bazan damu ba kuma bazan ji tsoroba.
Wadannan kalmomin dalili ne akan wajibcin zabar gaskiya ko da ko mai cutarwa ce (zaka cutu),  kuma dalili ne a kan cewa Imam Ali bai tsoron alhalin yana shi daya wurin yakan makiya su kuma suna da yawa, sannan ya ce bayan wannan ibarorin:  yaya suke fassara fadin Allah:
 ۚ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ ٌۚ [سوره الحجرات : 13]
Da cewa ai wanda ya fi takiyya ne.
Amsa: 
a - Lallai ne ita takiyya ba karya ba ce kuma bai inganta a fassara ta da karya ba, domin yana daga cikin jiga-jigan gabobin  karya shi ne saba ma daidai amma ita takiyya ba haka take ba, domin idan sharuddan ta suka cika to an yi umarni da yin ta a halin matsuwa kuma shi halin matsuwa umarni ne  na hakika na biyu, (hukuncin na biyu) yin aiki bisa ga tsari na takiyya aiki ne da hukunci na biyu idan ba haka ba da ya kasance dukkanin ayyuka a halin matsuwa sun zama karya kenan.   
b - Lallai ne karya tana daga cikin maganganu na labari (da ke iya yiwuwa ya zama karya ko gaskiya) amma ita takiyya ba labari ba ce, sai dai takiyya da ake yi a cikin maganganu, sai ka yi tunani. 
c -  Mun yarda cewa tana daga cikin masadik na karya, sai dai abin nufi da maganar Imam Ali(A.S) shi ne cutuwan da bai kai ga kisa ba kuma ba zai kasance cin mutunci ba, da karya zata wajabta kashe rai to saboda kashe rai ya fi muni a kan karya to za a koma ga karya ne, domin mas'ala na mai muhimmanci da wanda ya fi muhimmanci da gabatar da wanda ya fi muhimmanci yana daga cikin ka'idoji na hankalin masu hankali wanda babu wani kokwanton da zai shigo ciki.
d – Abin da ake nufi da أتقى  cikin ayar mai alfarma ita ce takiyyar daga Allah madaukaki wanda ake mata ibara da Takawa wanda Kur'ani da Hadisai su ka kwadaitar , da sannu zai zo cewa ita bata daga cikin bahasin takiyyar da aka yi bahasin ta a fikhu.
3- kafa dalilai da wasu bangaren ruwayoyi wanda suke nuni a kan rashin halascin takiyya wajen shafar huffi.
Amsa: Lallai shi shafa a kan huffi da makamancinsa na daga cikin masu wuraren da aka togace su, muma muna cewa a nan takiyya ba ta halasta ba.
4- Yin kafa hujja da ruwayar Kulaini da ya rawaito daga Mu'azu dan Kasir daga Abi Abdullah (A.S) ya ce: "Allah mai girma da buwaya ya saukar da Annabinsa (S.A.W) Littafi, Jibrilu ya ce: ya Muhammadu wannan ita ce wasiyyarka ga zababbu.
Sai ya ce su wane ne zababbu?
Sai ya ce: Ali Dan abi Dalib da Dansa ya kasance a kan littafi akwai Zobba, zuwa wajen da ya ce : a zobe na biyar : Ka fadi gaskiya cikin aminci da lokacin tsoro kada ka ji tsoron wani sai Allah.
Wannan ruwayar a fili ta nuna cewa wadancan masu girman addinin su ba takiyya ba ce kamar yanda Shi'a suke rayawa.
Amsa: Ita takiyya -kamar yanda zai zo- shari'a ta yarda da ita idan har yinta ba zai  kai ga fasadi a cikin addini ba, kamar  wasu daga cikin wurare da ake da zaton cewa shirun Imam (a.s) zai haifar da fasadi a cikin addini, to ya zama wajibi gare shi ya bayyanar da gaskiya, da wannan bayanin ne karyar abin da yake fada na cewa da  takiyya wajiba ce da Shugaban A'imma bai ki bai'a ga kalifan musulmai ba, ka yi tunanin wajen karyar wannan maganar.

Abin al'ajabi ya kai daga wannan kafa dalilin wanda ba komai ba kuma wanda ya yi nisa daga mai neman ilmi ballantana wanda ake ambaton sa da malami, a bayyane yake cewa nisa amawa ga fikhu na asali shi ne dalili na wadannan hujjojin.
Yaya Shaikul A'azam ya yi dikka na nazari yayi kuma cikakken tunani  cikin bahasin takiyya .
Mafi yawan abubuwan da suke cikin litattafan wanda suka zo a bayansa na daga bincike-bincike cikin takiyya an samo tushen su ne daga maganganun sa, musamman ma binciken isuwa, lallai ne ya kafa dalili ne da ruwayoyi masu inganci ba mu ga wani kafa dalili da aka yi kamar sa ba kafin Sheikh a cikin kalmomin wanda suka yi bincike a bangaren kamar Muhakki na biyu a cikin risalarsa da kuma Shahid na biyu a cikin littafin ka'idodin sa.
A cikin wannan risalar da ke a hannun ka na rubuta ta ne saboda sauke wadansu bangare na hakkokin sa da yawa ga dukkanin Masu kokari (Mujtahidai) da kuma amsa kiran wasu daga cikin masoya masu girma daga cikin ma'aikata a wurin taron karawa juna sani na duniya na tuna wa da haihuwarsa da ta cika shekara dari biyu, kuma na bayar da kyautar ta ga ruhinsa mai tsarki wanda ya kasan ce dukkanin kokarin da na yi sakamakon sa ne da dukkanin ilmin da nake samu da bincike- binciken da na yi, Ina fatan Allah Madaukaki ya karba da kyakkyawar karba sannan suma masu karatu masu daraja su yi duba da tunani a ciki da  ido na zurfafa wa da kai kawo. " zuwa gares hi dukkanin kalmomi masu kyau suke hawo wa".
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: